
16/09/2024
Cikin Hotuna: Ɗan takarar Kansila ya gudanar da feshin maganin sauro a yankinsa a Zamfara
Wani mai neman a tsayar da shi takarar kujerar Kansila a mazaɓar Galadima da ke ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara, Hon. Imrana Abdullahi Shagamu, ya ƙaddamar da aikin feshin maganin sauro a yankunan gundumar da yake neman wakilta.
Sahel24 Tv ya ruwaito cewar al'umma da dama a gundumar sun yi farin ciki da wannan aikin jinƙai da matashin ya gudanar, domin a cewar wasu daga cikinsu kusan babu gidan da ba a fama da cutar zazzaɓin cizon sauron sakamakon yawaitar sa a yankin.
A jawabinsa yayin ƙaddamar da wannan aikin, Hon. Imrana Abdullahi, ya jaddada aniyar da yake da ita ta ci gaba da inganta wannan gunduma, idan Allah ya ba shi nasarar zamewa Kansila mai wakiltarta.
Ba dai a kasafai ake samun ƴan siyasa masu tunani irin wannan ba, domin mafi yawancin lokuta al'umma kan nemi gwamnati mai ci da irin wannan jinƙai, to sai dai kuma haƙar ta su ta kan gaza cimma ruwa.