JOKES in HAUSA Extreme

JOKES in HAUSA Extreme Fatanmu sanar da ku cikakken 'yanciku. 08166494442

18/04/2020

Sallar jana'izar Marigayi Abba kyari.

01/05/2019

RAMUWA

Alhaji ne kullum yana azabtar da direban sa, ba ya biyansa albashi sai wata ta kai tsakiya. Kuma ga zagin sa da ya keyi ko yaushe.

Wata rana direban yace zai rama, suna cikin tafiya a mota sun kai tsakiyar daji sai Alhajin yace a tsaya zaiyi fitsari. Suna tsayuwa Alhaji na fitsari sai yaga direba aguje k**ar ana binsa a baya.

Shi ma ya runtuma da gudu, su kayi ta gudu tunda rana har yamma tayi. Alhajin ya gaji k**ar ransa zai fita sai ya tsaya sannan yace "Na hakura zan tsaya su kashe ni amma Menene ya sakamu gudun?".

Direban yace " Na jimane ban motsa jiki ba shi ne yau nakeyi".

30/04/2019

Ku bani Shawara* last week ina gyaran kayan miya sai na nika ban cire yayan tattassi ba to na yi miya na Kuma shanye abita to Shi ne sai na fara jin ba Dadi a ciki na yanzu naje asibiti anyi aune aune anyi scanning an tabbatar cewa shukar tattasai ce ta fito min a ciki a kalla ze yi kwando daya shi ne na ke neman mafita shin in sami manoma su nome Ko yaya zan yi ?

30/04/2019

MUSHA DARIYA..

wata me tallan zogale da kuli kuli ce tadauko kayan tallar tashgo birni saitazo wucewa ta wajen majalisar samari,sai s**a kirata s**a sayi hartayi gaba sai wani yace nifa saina tsokani mai zogalennan,saiyace mezogalee tana juyowa sai yace I LOVE YOU,wai abinki da yarkauye ta zaci irin mugun zaginnan yaimata,harda dawowa da sauri ta sauke kayan tallar tacire dankwali tai damara tace tonima I LOVE YOU din sai me??

29/04/2019

Ga nishadi kadan

29/04/2019

IDAN KAINE YA ZAKA FIDDA KANKA?

Watarana Wani Saurayi Yana gida a kwance a Cikin Gidansu Sai Yafito kofar gida domin Yasha iska Yana Zaune Kamin Bacci Yazo Masa Saiga Wani Dansanda Yabiyo ta kofar gidansu ya tambayeshi mai Yakeyi a wannan dare be shige gida ba?

Sai Yace Zafi ne ya Fiddashi a cikin Gida Shine Yasa Yafito Waje Domin Yaji Dan Sauki Sai Dansanda Yace karya ne sai Sunje Police station Wajen D.P.O sai saurayin yace Yayi Hakuri Yaki suje Sai Yace To Suje

Da Zasu Wuce Sai Yaron Ya Dauki katifarsa da yake zaune akanta da Nufin idan Sukaje Office ya Nunawa D.P.O cewa yana hutawa ne aka k**ashi.

Da Zuwansu office sai D.P.O yace wannan mai katifa kuma ina aka kamoshi sai dansanda yace ai barawon katifa ne yakamo idan kaine saurayin ya zakayi ka fidda kanka.

29/04/2019

???MAWAKAN ZAMANI???
Acikin jerin mawakan nan da muke dasu
wannene
yafi kwarewa afagen raira wakar soyayya
mai
ma,ana da kalaman sanyaya zuciya kuma
wace
wakarsa ce tafi burge ka/ki ????
1=sadi sidi sharifai
2=nazifi asnanic
3=nura m inuwa
4=saeed nagudu
5=adamu hassan nagudu
6=mahmud nagudu
7=tasiu unguwa uku
8=naziru mai waka
9=ibrahim danko
10=ali isa mai jita
11=abubakar sani
12=audu boda
13=sulaiman double
14=ahmad shanawa
15=yusuf karka sara
16=tijjani gandu
17=yakubu muhammad
18=musbahu ahmad
19=mudansir kasim
20=adam a zango
21 Ibrahim Ibrahim
22 Auwal lamari
23 Kamal nabil
25 Bilio
26 Danladi kima
27 umar m shareef
28= wani daban wanda bamu sanya shiba
Sannan wani mawaki ne yadace yai wake?

29/04/2019

FULANI DA D.P.O

Wani Bafulatani da Kanuri suna fada sai
Kanurin ya kwada masa mari, Bafulatani zai
rama ke nan sai aka hana shi, ’Yan sanda s**a
k**a su aka tafi dasu ofis. Da s**a je ofis Difi’o
ya tambaye su yadda aka yi, kowa ya yi bayani.
Sai Difi’o ya yanke hukunci, ya ce Kanurin ya
biya Bafulatani Naira dubu biyu diyyar marin da
ya yi masa. Kanurin ya nemi a ba shi lokaci ya je
gida ya dauko. Da ya tafi, ana tajira bai dawo ba,
Bafulatani ya dade yana jira kuma har ya gaji sai
ya daga hannu ya falla wa Difi’o mari, ya ce:
“Idan ya kawo dubu biyun sai ka rike!” ni sauri
ni ke yi.

29/04/2019

Idan kai ne ya zaka yi

Wani dan saurayi ne ya shiga motan haya ya hadu da wata yar budurwa mai kyau, ya rasa yanda zaiyi ya yi mata magana ko kuma ya burge ta sai ya ciro wayansa ya sa a kunne yana mai fadin hlo momy wllh bazan samu daman zuwa ba kiba kanina ya kai man 25million yanzu ni ina hanya ne zan tafi gidan gwamna za muje wani meeting.Bayan ya gama wayan sai yaga yarinyar tana ta kallon shi sai yace mata ya akayi sai tace mai dama tun dazu nake so in fadama tun da kaciro wayan ka battery ya fado kasa

idan kune ya zakuyi?

29/04/2019

Wani Yaro ne Mahaifiyarsa ta kira shi tana mar tambayoyi akan karatunsa na Boko sai ta ce wanene sunan Shugaban da ya mikawa Buhari mulkinsa Nigeria? Sai yaron yace Mama nasani Obasanjo ne, sai ta ce ka ji wawa, Jonathan ne, don haka ka kula da karatunka. Shi kuma yaron ya ce to Mama kekuma ga tambaya wacece Anty Jamila? Sai Mahaifiyar ta ce ban sani ba, sai yaron yace wawiya ki kula da Aurenki Budurwar Baba ce.🙊🙊🙊🙈🙈🙈🙈

Ni dai Admn na yi nan🏃🏽🏃🏽🏃🏽

Address

Tudun Wada
Gusau

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when JOKES in HAUSA Extreme posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to JOKES in HAUSA Extreme:

Share