05/05/2022
Fom-Fom din takara a jam'iyyar APC zasu yi kwantai saboda 'yan takara dayawa sun kasa saya saboda kudin da aka rafka misu
Jam'iyyar APC na shirin fadawa wani sabon al'amari wanda zai kai jam'iyyar ga faduwa zaben 2023 matukar uwar jam'iyyar bata rage kudin saye Fom ba nan da kwana 5 masu zuwa ba.
Bisaga al'adar siyasa, a duk sanda jam'iyya mai mulki ta fitar ranar sayen Fom din takara daga lokacin da ta sanya ranar rufe sayarwa kafin wannan rana ta zagayo kowa zai sayi na shi Fom.
To sai dai a wannan karo jam'iyyar APC ta yi rashin sa'a, domin Fom-Fom din takara suna nan birjit babu mai saya saboda kudin da aka rafka misu. Wanda haka ya sa doli uwar jam'iyyar ta kara wa'adin ranar rufe sayar da Fom zuwa 10-5-2022.
Yanzu haka akwai Foms-Foms din takara 'yan majalisun tarayya da na jihohi birjit anki saya an bar su da kayan su. Wanda yake wannan ba karamar illa zai yi wa jam'iyyar ba, kasancewar dayawa daga cikin 'yan takarar da ba su da kudin sayen Fom za su bar ta.
Don haka ya ragewa uwar jam'yya APC, ko ta rage kudin Fom ko kuma a bar ku da kayan ku.
S-bin Abdallah Sokoto