04/07/2020
Assalamu alaikum
Muna kara baiwa yan uwa masu bibiyar wannan shafi hakuri, na rashin ji shiraruwan mu, wannan ya farune sakamakon wata tangarda da muka samu a baya.
Saidai dayake yanzu komi ya daidaita, In Allah Yasa a kowane sati ranar LITANIN da misanin karfe 9:00na dare zaku jimu kai tsaye dauke da shirin INA MAFITA inda zamu rinqa zaqulo wasu matsaloli da suke faruwa acikin al-umma tare da tattaunawa akansu domin ganin an samo MAFITA. Daga gidan rediyon HASKE COMMUNITY FM 89.1
Buguda kari idan Allah yaso zamu sako muku wasu daga cikin shiraruwan da s**a gabata. Da fatar Allah yasa mu dace.