Arewa Daily News

Arewa Daily News Shafi ne dake kawo maku abubuwan karuwa na yau da kullun. Domin kawo maku ingantattun labarun Arewacin Najeriya da Najeriya baki ɗaya.

YANZU-YANZU: Cikin Gaggawa An Garzaya da Wata Mata Asibiti Saboda Amfani da Rogo da Tayi Domin Biyan Buƙata Saboda Maza ...
12/10/2025

YANZU-YANZU: Cikin Gaggawa An Garzaya da Wata Mata Asibiti Saboda Amfani da Rogo da Tayi Domin Biyan Buƙata Saboda Maza Sun Gaza

Wani lamari mai ban tsoro da mamaki ya faru a yankin Mararaba, karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa, inda wata mata ta tsinci kanta a asibiti bayan wani abin kunya da ya faru da ita sak**akon amfani da rogo a matsayin abun wasa na jima’i.

Shaidun gani da ido sun ce matar, wacce asali ta fito daga Ogoja, ta gyara wani lafiyayyen rogo Inda ta yi masa siffar azzarin mutum. An ruwaito cewa ta lullube rogon da kwaroron roba (condom) kafin fara amfani da shi, amma daga baya ta cire roban saboda ta samu Daɗi sosai.

A cewar rahoto, bayan kai ruwa rana da tayi har ta samu biyan bukata, yayin cire rogon Sai aka yi sa'a ya karye, inda wani bangare ya makale a cikin jikinta, lamarin da ya jefa ta cikin tsananin tashin hankali.

Ihun neman taimako da tayi ne yasa maƙwabta s**a yi gaggawar kai ta asibiti domin samun kulawar likita.

Rahotanni na cewa likitoci suna kokarin cire sassan rogon daga jikinta a halin yanzu, yayin da ‘yan sanda s**a fara bincike kan lamarin.

DA ƊUMI-ƊUMI: ASUU Ta Zata Shiga Yajin Aiki Cikin Kwana 14 Idan Gwamnati Bata Cika Alkawura BaKungiyar Malaman Jami’o’i ...
06/10/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: ASUU Ta Zata Shiga Yajin Aiki Cikin Kwana 14 Idan Gwamnati Bata Cika Alkawura Ba

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta sake jan kunnen Gwamnatin Tarayya da cewa za ta tsunduma yajin aiki muddin ba a aiwatar da alkawuran da aka cimma tsakaninsu ba cikin kwanaki 14.

Shugabannin ASUU sun bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai, inda s**a zargi gwamnati da kin aiwatar da yarjejeniyoyin da s**a hada da biyan bashin albashi, sauya tsarin albashi da inganta kayan aiki a jami'o'i.

Kungiyar ta ce bata da wata mafita illa daukar mataki mai tsauri domin kare mutuncin malaman jami'a da ingancin ilimi a kasar.

Sun bukaci gwamnatin da ta gaggauta daukar mataki kafin lokaci ya kure, domin kauce wa durkushewar tsarin ilimi a jami’o’in gwamnati.

TAMBAYA: Wai meyasa maza suke son auren Farar mace?Mu haɗu a comment section. Like and share
05/10/2025

TAMBAYA: Wai meyasa maza suke son auren Farar mace?

Mu haɗu a comment section. Like and share

DA DUMI-DUMI: Sarkin Nafada Ya Kaddamar Da Sabbin Dokokin Rage Tsadar Aure A GarinDaga Muhammad Kwairi WaziriWakilin Mai...
05/10/2025

DA DUMI-DUMI: Sarkin Nafada Ya Kaddamar Da Sabbin Dokokin Rage Tsadar Aure A Garin

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Wakilin Mai Martaba Sarkin Nafada, Alhaji Umaru Muhammad Baraya (Madakin Nafada), dake jihar Gombe, ya gabatar da sabon tsarin rage tsadar aure da kuma magance matsalolin da ke hana sauƙin aure a cikin al’umma. Taron ya gudana ne a Unguwar Madaki, Gundumar Nafada Central Ward, tare da goyon bayan manyan hukumomi, kotun majistare, da jami’an tsaro.

Sabon dokar za ta fara aiki daga shekara ta 2025, inda matasa s**a samu gargadi mai tsanani da kada su tsokani ko raina ’yan mata da kalaman "aure yayi arha". Duk wanda aka k**a yana aikata hakan zai fuskanci hukunci.

Wannan mataki na daga cikin kokarin da ake yi don karfafa tarbiyya da inganta zaman lafiya a Nafada da Jihar Gombe baki ɗaya.

Ranakun Da Ba Zan Taba Mantawa Da Su Ba A RayuwataNa yi aure 07/Oct/2021Mijina ya rasu 12/Feb/2022Na haifi 'yata na 02/J...
05/10/2025

Ranakun Da Ba Zan Taba Mantawa Da Su Ba A Rayuwata

Na yi aure 07/Oct/2021
Mijina ya rasu 12/Feb/2022
Na haifi 'yata na 02/June/2023
Mamana ta rasu 02/June/2025 daidai da ranar zagayowar haihuwar 'yata

Allah Ya gafarta masu.

Daga Jawahir Bashir

Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un: Mata Mai Juna Biyu Ta Rasu Sak**akon Lalacewar Babban Hanya a Keffi – AbajiRahotann...
05/10/2025

Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un: Mata Mai Juna Biyu Ta Rasu Sak**akon Lalacewar Babban Hanya a Keffi – Abaji

Rahotanni daga jihar Nasarawa sun tabbatar da rasuwar wata mata mai juna biyu da ta kai wata bakwai daga garin Marmara, bayan hatsarin da s**a gamu da shi sak**akon lalacewar hanyar hanyar Keffi–Nasarawa Toto zuwa Abaji.

Matar, wacce ake kaiwa asibiti domin duba lafiyar cikinta (antenatal), ta rasa ranta sak**akon mummunan yanayin hanyar da ta rutsa da su cikin wahala a hanya kafin su kai asibiti.

Mazauna yankin sun bayyana cewa matsalar lalacewar titin na ci gaba da jefa rayukan mutane da dama cikin haɗari, inda s**a roƙi gwamnati ta gaggauta gyaran hanyar don ceton rayuka.

Allah Ya jikanta da rahma, Ya kuma bai wa iyalanta hakurin jure wannan babban rashi. Ameen.

An Samu Wani Bata Gari Yayiwa Wannan Yarinyar Mai Shakaru Goma  13 Ciki Kasancewar Rashin Kular Waca ta Rike ta yasa sai...
05/10/2025

An Samu Wani Bata Gari Yayiwa Wannan Yarinyar Mai Shakaru Goma 13 Ciki Kasancewar Rashin Kular Waca ta Rike ta yasa sai da cikin ta ya girma sosai a jikin wannan yarinyar

Aka kai Ga Gano Halin da wannan yarinyar take ciki Bayan wannan Yarinyar Ta Haihu Aka Fara Binciken wanda yayi mata wannan Danyen Aikin Amma wannan Bawan Allah da yayi mata wannan cikin yace Sam

Shi ba zai karbi wannan cikin ba A cewar sa ai Biyan ta kudi yake kuma shi Duk lokacin da zaiyi Amfani da ita sai yasa Roba kawo i yanzu dai wllh Abinda wannan yarinyar zata ci ma wahala yake yi mata Ga Maraici Ga Rashin Gata

Mahaifin wannan yarinyar girma ya cimma sa sosai mutane da dama sun bashi Shawara akan ya Shigar da kara akan a karba wa yar sa yancin ta Amma yace shi yanzu ta Kansa yake Abinda Zai ci ma wahala yake yi masa

Bare har ya samu Damar yin Shari,a da wani Hakan yasa muke nema wa wannan yarinyar Taimakon Abinda zata ci Domin ta samu i sha Shan nonon da zata Shayar da wannan yaron nata Abu na biyu kuma muke kara neman Taimakon

Yan uwa Akan muga an sama wa wannan yarinyar Hakkin ta akan wannan Da yayi Bata mata Rayuwa Allhmdllh yar uwa Abokiyar Aiki wato Safiyya da sauran yan uwa muna

Godiya sosai da Gudun Mawar da s**a bayar muna kara mika Godiyar mu Ga wani Bawan Allah da ya bata Tallafin kudi na naira dubu biyar da wannan Dubu Biyar din muka sayawa wannan yarinyar kayan Abinci Allah yasa muyi kyakkyawan Karshe

Bazawara Mai neman mijin Aure tsakaninta da Allah. ya Allah kafito Mata da miji Nagari Mai tsoron Allah
05/10/2025

Bazawara Mai neman mijin Aure tsakaninta da Allah. ya Allah kafito Mata da miji Nagari Mai tsoron Allah

Ni bazawara ce ban taɓa haihuwa ba, idan ka shirya aure ka aje mun numbarka zan kiraka...
04/10/2025

Ni bazawara ce ban taɓa haihuwa ba, idan ka shirya aure ka aje mun numbarka zan kiraka...

Kungiyar 'Gassol Facebook Connect' Sun Kai Ziyara Gidan YariDaga Hamisu Hassan Ahmed Kamar Dai Yadda Mafiya Rinjayen Mal...
19/08/2025

Kungiyar 'Gassol Facebook Connect' Sun Kai Ziyara Gidan Yari

Daga Hamisu Hassan Ahmed

Kamar Dai Yadda Mafiya Rinjayen Malamai Su Kayi Bayani Akan Bayyana Kyau Ta Ko Sadaka Ko Wani Aiki Alheri Yana Da Kyau Domin Wani Ya Kan Iya Yin Koyi Da Abinda Kayi Sai Ku Shiga Ladar Tare

To Alhamdulillah Cikin Yardar Allah Tare Da Amincewar Sa A Jiya 18\8/2025 Hadaddiyar Kungiyar Nan Mai Suna Gassol Facebook Connect (GLFC) Sun Gabatar Da Ziyara Gidan Gyaran HALI Dake Garin Mutum Biyu A Karamar Hukumar Gassol Dake Jihar Taraba Domin Kaiwa Mazauna Gidan Yari Kayan Abinci Da Sauran Abubuwa Na Rayuwa.

Allah Ya Saka Da Alkairi Allah Yasa A Minzani.

Neman Taimako 😭 Neman Taimako 😭 Neman Taimako 😭Assalamu alaikum:Ina amfani da wannan kafa domin nemawa Dan'uwa Gudunmawa...
04/07/2025

Neman Taimako 😭 Neman Taimako 😭 Neman Taimako 😭

Assalamu alaikum:
Ina amfani da wannan kafa domin nemawa Dan'uwa Gudunmawarku ta addu'a da tallafin Kudi, Ibrahim Sahabi Wanda Aka fi Sani da Alhajijo daga Tella wanda Allah ya jarabceshi da Rashin lafia tsawon lokaci yana jinya.

Yanzu haka Alhajijo yana Kwance a Gida yana fama da Ciwon DAJI wanda ya Tsananta har wannan matakin Don Haka Ana Neman taimako dan kai shi Asibiti.

Sanadiyar doguwar jinya al'amurra sun tsananta yanzu haka ana neman Kudin da za'a yimasa aiki da Siyen Magungunna da Sauran hidimar Rayuwa.

Ga wanda Allah ya horema, Dan Allah a taimaka masa da kudi ko kadan ko da yawa.

Acct. No.: 3141961957
Acct. Name: Isa Muhammad
Bank Name: First Bank

07062603454, 07087819224, 07060724357,

Allah bada Ikon taimakawa

Address

Gwarinpa
420241

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Daily News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share