16/10/2025
Miyetti Allah Ta Dakatar da Shugabanninta na Taraba, Bauchi da Adamawa Saboda Zarge-Zargen Rashin Kyakkyawan Jagoranci
Kungiyar Miyetti Allah Kautal H**e Fulani Sociocultural Association ta dakatar da shugabanninta na jihohin Taraba, Bauchi da Adamawa bisa zarge-zargen rashin ingantaccen jagoranci da kuma sakaci wajen kare muradun mambobinta.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar na ƙasa, Ambasada Mohammed Tasiu Suleiman, ya fitar, an bayyana cewa Shugaban Kungiyar na ƙasa Alhaji Dr. Abdullahi Bello Bodejo (Lamido Fulbe), ne ya amince da dakatarwar nan take.
Shugabannin da aka dakatar sun haɗa da Bammi Bello Jane na Taraba, Muhammed Hussaini Buzaye na Bauchi, da Usman Abubakar Yirlabe na Adamawa.
Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan samun koke-koke da yawa daga makiyaya a jihohin da abin ya shafa, waɗanda s**a nuna rashin gamsuwa da yadda shugabanninsu ke tafiyar da harkokin ƙungiyar.
Kungiyar ta ce matakin ya zama dole don dawo da amincewa da kwarin gwiwar mambobi tare da tabbatar da gaskiya da adalci a cikin ƙungiyar.
Haka kuma, ƙungiyar ta umarci hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da kada su ci gaba da hulɗa da waɗanda aka dakatar, domin ba su da hurumin wakiltar ƙungiyar daga yanzu.
Sanarwar ta gargadi shugabannin da aka dakatar da su guji ci gaba da bayyana kansu a matsayin wakilan ƙungiyar, inda ta ce duk wanda aka k**a da hakan zai fuskanci shari’a.
A ƙarshe, Shugaban ƙungiyar na kasa, Dr. Abdullahi Bello Bodejo, ya tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da himma wajen kare muradun makiyaya da tabbatar da haɗin kai a tsakanin mambobinta a fadin ƙasar.