
28/08/2025
MUHIMMANCIN KARƁAR KATIN ZABE
A ƙarƙashin jagorancin Arc. Shehu Ahmad Tukur Sarkin Fadar Keffi, ana kira ga al’ummar mu da su tabbatar sun karɓi katin zabe domin kada kuri’unsu ya ƙara ƙima da tasiri a zabubbuka masu zuwa.
Katin zabe shi ne makamin da zai ba mu damar zabar shugabanni nagari da za su jagorance mu zuwa ci gaba. Idan ba mu da katin zabe, ba mu da murya a zabubbuka.
Arc. Shehu Ahmad Tukur ya jaddada cewa:
"Zabe hanya ce ta sauya al’amura cikin lumana, kuma karɓar katin zabe shi ne mataki na farko wajen tabbatar da cewa muryar mu ta yi tasiri."
Ku tashi tsaye, ku karɓi katin zabenku, ku zama ɓangare na canji mai kyau!
- Ka karɓi katin zabe
- Ka yi rijista idan baka yi ba
- Ka shirya don kada kuri’a
Sako daga Arc. Shehu Ahmad Tukur – Sarkin Fadar Keffi