11/04/2025
Addu’ar Yaye Zalunci da Kau da Shi
Wacce Jagora Sayyid Zakzaky (H) ya umarci ’yan’uwa da su rika karantawa tun yana tsare
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِ
اللّهُمَّ صَلِّ عَلى مُحَمَّدٍ وَآلِ مُحَمَّدٍ وَعَجِّلْ فَرَجَهُمْ يَا كَرِيمُ
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammad da iyalan Muhammad, kuma ka gaggauta farfadowarsu, Ya Mai karamci.
اَللَّهُمَّ اِنَّ ظُلْمَ عِبادِكَ قَدْ تَمَكَّنَ فِي بِلادِكَ،
حَتَّى اَماتَ الْعَدْلَ وَ قَطَعَ السُّبُلَ،
Ya Allah, lalle zaluncin bayinka ya mamaye ƙasarka, har ya kashe adalci, ya katse hanyoyi.
وَ مَحَقَ الْحَقَّ وَ اَبْطَلَ الصِّدْقَ،
وَاَخْفَي الْبِرَّ وَ وَاَظْهَرَ الشَّرَّ،
Ya shafe gaskiya, ya kawar da amana; ya ɓoye kyautatawa, ya bayyanar da sharri.
وَاَخْمَدَ التَّقْوَي وَ اَزالَ الْهُدَي،
وَ اَزاحَ الْخَيْرَ وَ اَثْبَتَ الضَّيْرَ،
Ya kashe tsoron Allah, ya kawar da shiriya; ya kore alheri, ya tabbatar da cutarwa.
وَ اَنْمَي الْفَسادَ وَ قَوَّي الْعِنادَ،
وَ بَسَطَ الْجَوْرَ وَ عَدَي الطَّوْرَ.
Ya watsa fasadi, ya ƙarfafa girman kai; ya shimfiɗa zalunci, ya ƙetare iyaka.
اَللَّهُمَّ يَا رَبِّ، لا يَكْشِفُ ذلِكَ اِلاَّ سُلْطانُكَ،
وَ لا يُجِيرُ مِنْهُ اِلاَّ امْتِنانُكَ،
Ya Allah, Ya Ubangiji, babu wanda zai iya kawar da hakan sai da mulkinka, kuma babu mai karewa daga gare shi sai falalarka.
اَللَّهُمَّ رَبِّ فَابْتُرِ الظُّلْمَ وَ بُثَّ جِبالَ الْغَشْمِ،
وَ اَخْمِدْ سُوقَ الْمُنْكَرِ وَ اَعِزَّ مَنْ عَنْهُ يَنْزَجِرُ،
Ka sare zalunci, ka bazar da azzaluman da s**a yi girman kai; ka kashe kasuwar mummuna, ka ɗaukaka masu nisantar shi.
وَاَحْصُدْ شَاْفَةَ اَهْلِ الْجَوْرِ،
وَاَلْبِسْهُمُ الْحَوْرَ بَعْدَ الْكَوْرِ،
Ka sare tushen masu zalunci, ka sanyasu cikin rikicewa bayan sun taɓa shiriya.
وَعَجِّلِ اللَّهُمَّ اِلَيْهِمُ الْبَيَاتَ،
وَ اَنْزِلْ عَلَيْهِمُ الْمَثُلاتِ،
Ka gaggauta musu azaba ba zato ba tsammani, ka saukar da hukunci a kansu.
وَاَمِتْ حَيوةَ الْمُنْكَرِ لِيُؤْمَنَ الْمَخُوفُ،
وَيَسْكُنَ الْمَلْهُوفُ وَيَشْبَعَ الْجائِعُ،
Ka kawo ƙarshen rayuwar mummuna domin masu tsoro su sami aminci, masu damuwa su huta, masu yunwa su ƙoshi.
وَيُحْفَظَ الضَّائِعُ وَيَاْوَي الطَّريدُ،
وَيَعُودَ الشَّريدُ وَيُغْنَي الْفَقيرُ،
A kare wanda ya ɓace, a ba mafaka ga wanda aka kore, a dawo da ɓatacce, a wadatar da matalauci.
وَيُجارَ الْمُسْتَجيرُ وَيُوَقَّرَ الْكَبيرُ،
وَيُرْحَمَ الصَّغِيرُ وَيُعَزَّ الْمَظْلُومُ،
A tsare mai neman kariya, a girmama babba, a jiƙan ƙarami, a ɗaukaka wanda aka zalunta.
وَيُذَلَّ الظَّالِمُ وَيُفَرَّجَ الْمَغْمُومُ،
وَتَنْفَرِجَ الْغَمَّآءُ وَتَسْكُنُ الدَّهْمآءُ،
A ƙasƙantar da azzalumi, a sauƙaƙa wa mai damuwa, a warware ƙunci, a lafa bala’i.
وَيَمُوتَ الاِخْتِلافُ وَيَعْلُوَالْعِلْمُ،
وَيَشْمُلَ السِّلْمُ وَيُجْمَعَ الشَّتاتُ،
A kawar da sabani, a ɗaukaka ilimi, a yada zaman lafiya, a haɗa kawuna.
وَيَقْوِيَ الإيمَانُ وَيُتْلَي الْقُرْآنُ،
اِنَّكَ اَنْتَ الدَّيَّانُ الْمُنْعِمُ الْمَنَّانُ.
A ƙarfafa imani, a karanta Alƙur’ani. Lalle Kai ne Mai shari’a, Mai ni’ima, Mai yawan baiwa.
وَصَلِّ اللّهُمَّ عَلى مُحَمَّدٍ وَآلِهِ الطَّيِّبِينَ الطَّاهِرِينَ.
Ka yi salati, ya Allah, ga Muhammad da iyalansa masu tsarki, masu tsabta.