Albahrain Hausa

Albahrain Hausa Albahrain Hausa ta shahara wajen kawo labarai sahihai da rahotanni gami da hirarraki masu ma'ana.

15/05/2026

Ku shaƙata da wannan.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bar China bayan kammala wata muhimmiyar tattaunawa da shugaban ƙasar, Xi Jinping, a bi...
15/05/2026

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bar China bayan kammala wata muhimmiyar tattaunawa da shugaban ƙasar, Xi Jinping, a birnin Beijing.

Ganawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a inganta dangantakar tattalin arziki da siyasa tsakanin manyan ƙasashen biyu masu ƙarfin tattalin arziki a duniya.

Bayan tattaunawar, Trump ya bayyana cewa sun cimma wasu yarjejeniyoyin kasuwanci masu muhimmanci, duk da cewa bai bayyana cikakken bayani kan yarjejeniyoyin ba.

Rahotanni sun nuna cewa shugabannin biyu sun tattauna kan batutuwa masu yawa da s**a haɗa da kasuwanci, tsaro, yankin Taiwan da kuma rikicin Gabas ta Tsakiya.

A yayin wata ganawa a babban ɗakin taron jama’a na Beijing, Xi Jinping ya gargadi Trump cewa batun Taiwan na iya zama babban ƙalubale ga dangantakar ƙasashen biyu idan ba a tafiyar da shi cikin hikima ba.

14/05/2026

Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, kuma Shugaban Kwamitin Tsare-tsaren Shirya Babban Taron Bunƙasa Tattalin Arzikin Jihar Jigawa, Injiniya Aminu Usman Gumel, FNSE, ya jagoranci ganawa da mambobin kwamitin shirya taron da za a gudanar a cikin watan Yuli a babban birnin jihar, Dutse.

Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, kuma Shugaban Kwamitin Tsare-tsaren Shirya Babban Taron Bunƙasa Tattalin Arzikin Jihar ...
14/05/2026

Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, kuma Shugaban Kwamitin Tsare-tsaren Shirya Babban Taron Bunƙasa Tattalin Arzikin Jihar Jigawa, Injiniya Aminu Usman Gumel, FNSE, ya jagoranci ganawa da mambobin kwamitin shirya taron da za a gudanar a cikin watan Yuli a babban birnin jihar, Dutse.

14/05/2026

Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da kafa kwamitin da zai sanya ido kan tsarin kuɗin akwati da gwamnatin da dawo dashi.

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa kamfaninsa ya yi watsi da buƙatar da NNPC Limited ya...
14/05/2026

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa kamfaninsa ya yi watsi da buƙatar da NNPC Limited ya gabatar na ƙara yawan hannun jarinsa a matatar mai ta Dangote da kaso 7.25 cikin 100.

Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da shugaban asusun zuba jari na Norway, Nicolai Tangen.

Rahotanni sun nuna cewa matatar man Dangote da ke Lekki na ci gaba da ƙara yawan man da take tacewa, inda aka ce an tace sama da lita biliyan 3.18 a watanni ukun farko na shekarar 2026.

A lokaci guda kuma, an samu raguwa sosai a yawan man fetur da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje, abin da masana ke ganin na iya rage matsin tattalin arziki da kashe kuɗaɗen musayar kuɗi ga Najeriya.

Bincike ya nuna cewa tashin hankali tsakanin Amurka da Iran da ya haifar da hauhawar farashin mai a kasuwannin duniya ya taimaka wajen ƙara kuɗin shiga ga matatar Dangote, musamman ta fuskar fitar da tataccen mai zuwa wasu ƙasashe.

Dangote ya ce dalilin da ya sa aka ƙi amincewa da ƙarin hannun jarin da NNPC ke nema shi ne saboda kamfanin na da shirin bai wa sauran ‘yan Najeriya damar zuba hannun jari a matatar nan gaba.

Masana tattalin arziki na ganin cewa wannan mataki na iya buɗe ƙofofi ga masu zuba jari na cikin gida tare da ƙarfafa kasuwar hannayen jari a Najeriya.

Matatar Dangote dai na daga cikin manyan ayyukan masana’antu a Afirka, kuma ana kallonta a matsayin wani muhimmin mataki wajen rage dogaro da shigo da tataccen mai daga ƙasashen waje.

13/05/2026

Manyan shugabannin duniya na tattauna batutuwan tsaro da tattalin arziki.

13/05/2026

Tinubu Ya Isa Rwanda Domin Babban Taron Kasuwancin Afirka!

13/05/2026

Iran ta ce jami’anta sun shiga ruwan Kuwait ne saboda tangarɗar na’ura.

12/05/2026
12/05/2026

An rantsar da shugaban Uganda karo na 7.

Address

Kano State
Hadejia

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Albahrain Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share