13/12/2025
LABARIN MALAMIN ISLAMIYYA MALAM NURA DA AKE ZARGIN YAYIWA YARA 9 LUWAƊI
Wannan yana daya daga cikin labaran da s**a tadamin hankali acikin wannan shekarar baki daya, Subhanallah Allah ka tsare mu daga mummunar ƙaddarar rayuwa. Nafara samun labarin ne kwanaki hudu da s**a wuce ta hanyar gidan Rediyon Berekete Family yayin da Iyaye yaran s**a kai korafin lamarin sannan kuma Ordinary President na Berekete Family ya tabbatar da tabbacin faruwar wannan lamari ta hanyar tuntubar wani Babban mutum dake zaune a can garin da lamarin ya faru.
A garin Abuja Katampe extension nan ne inda iyayen yaran suke da zama sannan kuma ananne inda shi Malam Nura yake da Islamiyyar tasa dayake koyar da yaran unguwa karatun Alqur'ani mai girma, amma sam bicika a kirashi da malami ba duba da cin amanar daya aikatawa iyayen yaran das**a yarda da shi s**a danka masa amanar yaransu.
Bisa bayanai da s**a fito daga bakin iyayen yaran da kuma su wadanda aka aikata mawa laifi shi wanda ake zargin yana amfani da kalmomin tsoratarwa ga yaran kan cewa duk sanda wani ya kuskura ya faɗi abinda yake aikata masu to babu makawa a wannan ranar zai mutu (Amma shi Allah ba azzalumin sarki bane kasani duk wani laifi da kake aikatawa yana kallo sannan kuma yana sane).
Bayan jita-jitan unguwa kan cewa ansamu Malamin Islamiyyar Malam Nura yana lalata da wani yaro shine aka samu wata jajirtacciyar Mahaifiya ta tsare yaranta ta tambaye shin dakwai wani abu daya taɓa shiga tsakanika da Malam Nura wanda kakeson ka sanar dani?, a nan ne yaron nata yake sanar da ita shi fa babu kawai dai wani lokacin yana shashshafa masa jiki ne har yake tambayarsa wai shin kanajin daɗi idan inah shafa ka?, yaro yace a'a kuma Ni banason abinda kakemin gaskiya. Sannan yace mata dakwai ranar da muna tare da abokina wane......!!!, shine Malam Nura yakirani naki zuwa shine shi abokin nawa yacemin mai yasa baki zuwa? Nace masa ga abinda yakemin shine yace Ni eai nawa mai sauki ne shi har hawansa yake ta baya🥹 Subhanallah.
Dakwa wannan mata taji haka sai tayi maza maza ta nufi gidansu wannan Abokinna Danta tasanar da mamarsa halinda ake ciki tace mata ta tuntube shi taji gaskiyar afkuwar lamarin, kamar yadda waccan matar ta farko tayi haka ita ma wannan tayi sannan yaro ya shaidawa Mamansa Eah kam haka ne amma kuma yace idan na fada muku mutuwa zanyi🥹💔 nan yaro ya faɗi yanata kuka.
Abu kamar wasa sai gashi ansamu yara ɗaiɗai har guda 5 wanda ya lalata sannan kuma babban abun takaici dukkansu yarane kanana wanda shekarunsu basu wuce 12, 13, 14, dakuma 15 ba. (They minor in terms of age). Lamari da ya gawurta nan iyayen yaran s**a kai kara gidan su Malam Nura domin suji ba'asi amma kuma sai kash, babansa yace da su wai suyi hakuri shida kansa zai saka Nura yabar gari kaji wani rashin hankali da son zuciya agun babban mutum kuma a matsayin uba namiji.......!!!😏
Iyayen yara s**a kai maganar zuwa gurin yan sanda sannan bayan sunje can anan aka samu karin wasu iyayen yaran wanda yara har s**a kai su 9 wanda ya lalata, daga nan kuma aka ɗauki sample dinsu a clinic din headquarter na police dake Abuja za'ayi gwaji sannan kuma aka kamu mai laifi aka kuma fada masa abinda ake zarginsa da aikatawa sannan aka tambayeshi shin ka aikata? Ya amsa laifinsa da cewa EAH NA AIKATA.🤗
Dakwai Part II yana nan zuwa bada jimawa ba ku saurareni. Nagode.