01/08/2023
AN ƊAUKI MATAKI KAN SHUGABANNIN ASIBITIN GUMEL
Biyo bayan ziyarar bazata da Gwamna Mallam Umar Namadi ya kai babban asibitin Gumel a ranar Juma’ar da ta gabata, dangane da yadda gwamnan ya sami asibitin cikin wani mummunan yanayi, yanzu haka an ɗauki matakan ladabtarwa ga manyan jami’an gudanarwa na wannan asibiti.
Matakan sun haɗa da rushe hukumar gudanarwar asibitin nan take da kuma mayar da ɗaukacin manyan jami’an wannan asibitin zuwa hedikwatar ma’aikatar da ke Dutse inda za su jira hukuncin da zai hau kansu bayan an kammala bincike.
Jami’an da abin ya shafa sun haɗa da: Medical Director, Director Clinical Services, DAF, H.O.D Pharmacy, H.O.D Laboratory da kuma Accountant.
Idan ba a manta ba, a lokacin ziyarar Gwamnan, inda ya kewaya sassa daban-daban a cikin asibitin ya gane wa idonsa yadda ake tursasa wa marasa lafiya biyan kuɗin kayayyakin da ya kamata a samar da su a asibitin. Alal misali, Gwamnan ya tattauna da marasa lafiya da dama waɗanda s**a tabbatar masa da cewa ana tilasta musu biyan kuɗi har naira 7,000 kafin a ɗauki jinin da ‘yan uwansu s**a ba su gudunmuwar sa. Haka kuma ya gano cewa hatta auduga da ake amfani da ita asibitin marasa lafiyar ne suke saye da kuɗinsu, wanda kuma hakan ya saɓawa manufar gwamnatin jiha na samar da waɗannan abubuwa kyauta musamman ga yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar da kuma mata masu shayarwa.
Baya ga wannan kuma Gwamnan ya gane wa idonsa yadda asibitin yake fama da matsalar isasshen ruwan famfo a duk kuwa da kuɗaɗen da gwamnati take samarwa asibitin a kowane wata. Bugu da ƙari kuma, Gwamnan bai sami shugabannin asibitin a bakin aikinsu ba a lokacin wannan ziyarar.
To a sakamakon haka ne Gwamna Mallam Umar Namadi ya yi taron gaggawa da manyan jami’an ma’aikatar lafiya da na hukumomin da ke ƙarƙashinta a safiyar litinin, inda nan take ya umarci kwamishinan ma’aikatar da ya ɗauki matakan ladabtarwa akan wannan halayya ta ma’aikatan kiwon lafiyar.
Government House Media Office