04/07/2025
Falalar Azumin Tasu'a Da Ashura
Gobe, Juma’a, 4 ga watan Yuli 2025, ita ce tara ga watan Muharram, rana da ake kira Tasu’a a cikin harshen Larabci. Wannan rana na ɗaya daga cikin kwanaki masu albarka da Manzon Allah ﷺ ya nuna darajarsu cikin hadisai sahihai, musamman idan aka yi azumi a cikinta tare da ranar Ashura, wato ranar goma.
An karɓo daga Ibn Abbas (RA) cewa: “Lokacin da Manzon Allah ﷺ ya zo Madina, ya tarar da Yahudawa suna azumin ranar Ashura. Sai ya ce: Me yasa kuke yin hakan? S**a ce: Wannan rana ce da Allah ya ceci Musa da mutanensa, sai Musa ya yi azumi domin godiya. Sai Annabi ﷺ ya ce: Mu muna da cancanta fiye da su wajen bin Musa.” Sai ya azumta kuma ya umurci musulmi da su azumta. (Sahih Muslim: 1130; Bukhari: 2004)
Daga nan ne Manzon Allah ﷺ ya bayyana cewa yana da niyya idan ya rayu zuwa shekara mai zuwa, zai yi azumin Tasu’a da Ashura tare. Ya ce: “Idan na rayu zuwa shekara mai zuwa, lallai zan yi azumin ranar tara (Tasu’a).” (Sahih Muslim: 1134) Wannan yana nuni da hikimar bambanta musulmi da Yahudawa a ibada, da kuma ƙara daraja ga azumin.
Azumin Ashura da Tasu’a yana da girma matuƙa. A wani hadisi daga Abu Qatada, Manzon Allah ﷺ ya ce: “Ina fatan Allah zai gafarta zunuban shekara guda da ta gabata saboda azumin Ashura.” (Sahih Muslim: 1162). Malamai sun ƙara bayani cewa wannan falala na shafe zunuban saghā’ir – wato ƙananan zunubai – ne kawai, amma duk da haka yana nuni da girman wannan rana.
A mahangar fikihu, malamai kamar Imam Nawawi, Ibn Rajab, da Ibn Qudamah sun yi ittifaki cewa azumtar Tasu’a da Ashura tare ya fi daraja fiye da yin Ashura kawai, kamar yadda Manzon Allah ﷺ ya ƙudurta. Kuma wannan ya zamo hanya mai kyau ta sabunta ibada da tsarkake zuciya ga sabon shekara ta Hijira.
Musulmi da ya azumci gobe, ya tanadi tsarkakakkiyar niyya, kuma ya guji yin karya, zargi, ko munanan halaye. Ana kuma karfafa yin azumin Ashura (rana ta goma) a ranar Asabar, domin cikar sunnah da samun falala gaba ɗaya.
A ƙarshe, wannan wata ne da Allah Ya karrama, rana ce da Manzon Allah ﷺ ya fifita, azumi ne da ke gogewa da yafe zunubai. Ya kamata musulmi ya yawaita ibada, istighfar da kyautatawa. Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya tsarkake zukatanmu, Ya tabbatar mana da falalar wannan muhimmiyar rana. Ameen.