DAGA Mairakumi

DAGA Mairakumi LABARAI DA DUMI-DUMINSU AKO YAUSHE

27/06/2025
Tabbas El Rufai ya taimaka min wajen zama shugaban kasa - Bola Ahmed TinubuShugaban Najeriya Bola Tinubu ya jinjinawa ts...
16/02/2025

Tabbas El Rufai ya taimaka min wajen zama shugaban kasa - Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jinjinawa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai, wanda ya bayyana shi a matsayin mutumin da ya bada gagarumar gudummawa wajen samun nasararsa a zaben da ya gabata. A sakon da ya aike masa na taya shi murnar cika shekaru 65 a duniya, Tinubu ya bayyana El Rufai a matsayin jigo wajen kafa jam'iyyar APC, wanda ake yaba masa saboda fasaharsa da kuma jajircewa. A saƙon da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya rabawa manema labarai, Tinubu ya yabawa tsohon gwamnan akan kokarinsa na gina dimokiradiya da yiwa kasa aiki da kuma goya matasa wajen koya musu dabarun mulki. Shugaban ƙasar ya ce El Rufai baya ga taimakawa wajen kafa APC, ya kuma taimaka wajen samun nasararta a zaben shugaban ƙasa na shekarar 2015 da 2019 da kuma 2023.

📷 Daily Trust

DA DUMI-DUMI: Kamfanin mai na NNPC ya fara daukar sabbin ma'aikata DAGA MairakumiKamfanin mai na NNPCL ya shirya daukar ...
26/07/2024

DA DUMI-DUMI: Kamfanin mai na NNPC ya fara daukar sabbin ma'aikata

DAGA Mairakumi
Kamfanin mai na NNPCL ya shirya daukar karin sabbin ma’aikata k**ar yadda A Yau ta ruwaito kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma'a.

Soneye ya ce za a dauki ma’aikata ne a matakai da muk**ai daban-daban a sassa daban-daban na kamfanin,

Shafin A Yau ya ruwaito Mista Soneye ya umurci masu bukatar aiki da kamfanin su ziyarci shafin ma’aikata na NNPC don cike fom na aikace-aikacen da suke nema

Ga shafin nasu k**ar haka https://careers.nnpcgroup.com

Kamfanin ya ce za a rufe shiga daga ranar 20 ga watan Augusta, 2024

To sai dai bayanai sun nuna zuwa yanzu shafin ya soma fuskantar tangarɗa sak**akon cinkoson masu ziyara da neman aiki amma kamfanin ya ce yana faman gyara website din

Fasarar Jawabim Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Na Murnar Cikar Nijeriya Shekaru 25 A Mulkin DimokradiyyaRANAR DEMOKARAD...
12/06/2024

Fasarar Jawabim Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Na Murnar Cikar Nijeriya Shekaru 25 A Mulkin Dimokradiyya

RANAR DEMOKARADIYA.12/JUNE/2024.

Ya ku `yan uwana `yan Najeriya bari mu fara da taya juna murnar sake ganin zagayowar ranar Demokaradiya a yau, ranar sha biyu ga watan Yunin shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu. Wannan ranar ta zo dai dai da cikar kasar mu shekaru Ashirin da biyar a cikin mulkin Demokaradiya ba tare da katsewa ba.

A rana irin ta yau, shekaru talatin da daya baya, muka kaddamar da kudirin mu na zamowa al`ummar da ta yi cikakkiyar amincewa da Demokaradiya.

Ba abu ne mai sauki ba, kusan ma cike yake da had`arin gaske ta inda cikin shekaru shida da s**a biyo baya sai da duk muka rikide muka zamo `yan gwagwarmayar kwatan `yancin kanmu a matsayin mu na `yan kasa kuma halittun Allah a ban kasa.

A cikin wannan gwagwarmayar, mun rasa rayukan gwaraza maza da mata. Ciki kuwa har da wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa na ranar goma sha biyu ga watan Yunin shekara ta dubu daya da dari tara da casa`in da uku kuma ya zamo tambarin dimukradiyya, wato Cif MKO Abiola, da mai d`akinsa Hajiya Kudirat, da sauran wasu gwarazan irinsu janaral Shehu Musa `Yar Adua da Pa Afred Rewane, duka sun sadaukar da rayuwar su wajen samar wa Najeriya makoma mafi dacewa.

Mu yi jinjinar ban-girma ga mutanen da ba za a manta da su ba, irin su Cif Anthony Enahoro da Chif Abrahama Adesanya da Comando Dan Suleiman da chif Arthur Nwankwo da chif Chukwuemeka Ezeife da Admiral Ndubuisi Kanu da Chif Frank Kokori da Chif Bola Ige da chif Adekunle Ajasin da chif Ganiwu Dawodu da chif Ayo Fasanni da Chif Gani Fawehinmi da chif Olabiyi Durojaiye da Dakta Beko Ransome-Kuti da Chima Ubani da dai sauransu da s**a riga mu gidan gaskiya.

Zai zama an yi tuya an mance da albasa idan aka manta da sadaukawar gwaraza irinsu Alani Akinrinade da farfesa Bolaji Akinyemi da farfesa Wole Soyinka da chif Ralph Obioha da chif Cornelius Adebayo ba, da dai sauran su, mutane ne da s**a jure wa radadi da wahalhalun rayuwar `yan gudun hijira.

A yayinda gwarazan `yan gudun hijirar ke aiki daga nesa don tabbatar da diga-digin dimukradiyya, takwaroroinsu da ke gida Najeriya sun ci gaba da nuna juriya ga matsin mulkin sojoji. Cikin su akwai Olisa Agbakoba da Femi Falana da Abdul Oroh da Sanata Shehu Sani da Gwmna Uba sani da chif Olu Falae da saura jagororin tabbatar da ganin cewa an samar da demokaradiya irin su Chif Ayo Adebanjo da Chif Ayo Opadokun.

Sadaukarwa da gudunmuwar da wadannan hazikai s**a bayar a wannan muhimmin fage, abu ne da ba za a ta6a iya biya ko a manta da shi ba.

Da babu gudumuwar jajirtattun `yan jaridar Najeriya da s**a sadaukar da kafafen yada labaransu wajen isar da amon `yan rajin samar da dimukaradiyya ga duniya, da ba mu yi nasara a akan `yan mulkin k**a-karya ba. Wannan ya sanya a yau za mu mika jinjinar mu ga kafafen yada labarai irin Jaridan Punch da Guardian da National Concord da Tribun da News Tempo da kuma Tell wadanda s**a fusaknci katsalandan din gwamnatocin mulkin-danniya a aiyukansu har ta kai ga daure wasu `yan jaridunsu, ba don komai ba sai don sun nuna dagiya kan `yancin fadin-albarkacin baki ga `yan kasa da kuma tabbatar da nasarar za6en sha biyu ga watan yuni.

Sarkin yawa ya fi sarkin karfi! Duk da tarin karfin mulkin k**a-karya, sannu a hankali sai da aka ci karfinsu har s**a zama tarihi. A nan ne karfin ra`ayi da zabin al`umma s**a nuna cewa suna sama da karfin bindigogi da tankokin yaki da ma duk wata barazanar masu karfi.

A shekarar 1999 Kasar nan ta samu kwato kanta daga hannun `yan k**a-karya hakan ya sa ta zamo kasar Africa mafi yawan al`umma, daya daga cikin kasashe mafi yawan al`umma a duniya, kuma hasken kasashen bakar fata da ke kan turbar Demokaradiya.

Wannan sauyi ya zama wani juyin-juya-hali mai muhimmanci ga tarihin Dan Adam da ba za a taba mantawa da shi ba b***e a ce ya zama kashin-yadawa.

A yau, bayan shekara ashirin da biyar, ga shi muna murnar dawowa wannan gwadabe na mulkinn
demokaradiya.

Bayan dogon nazari da hange, mun tabbatar da cewa Demokaradiya ba kayan aro ko bakon abu ba ce gare mu, don haka ba za mu yi sakaci da ita ko mu tsuke ta zuwa wani abu da ake yi daga lokaci zuwa lokaci ba, ko mu bar ta ta zamo zallar zabe da nsarar wata jam`iya a kan wata ba.

Duk da a wani sa`in, harkokin zabe kan yi k**a da wasan kwaikwayo, sai dai ya k**ata mu sani cewa zabe wani bangare ne na demokaradiya, amma ba dukkanta ba, Demokaradiya wani tsari ne rayuwa da ke nuna yadda ake da zaben ra`ayi ko makoma, don haka, kasa tana iya gudanar da zabe ba tare da tana demokaradiya ba, amma babu yadda za a yi kasa ta yi demokaradiya ba tare yin zabe ba.

Ta hanyar dimukradiyar ne muka raya al`adar gudanar da sahihin zabe a kasar nan, kuma wannan al`adar ta gudanar da zabe a bayyane ita ce ta tabbatar da cewa mun aminta da demokaradiya, kasancewar muna ganin yadda aka mika mulki daga gwamnati zuwa wata zababbiyar ta hanyar demokaradiya ya nuna cewa demokaradiya ta zame mana jini da tsoka.

Ya ku `yan uwana `yan Najeriya, sahihiyar demokaradiya wata fitila ce da take haskaka rayuwar al`ummar da ke karkashinta ta hanyar ba su damar yin `yantaccen tunani, da rayuwar da suke so,ta hanyar da s**a zaɓa muddin bata saɓawa doka ba.

Wasu daga ababen da Demokaradiya ke kyama da inkari sun hada da yaudara ko tilasta wani ra`ayi ga masu mabambanta ra`ayoyi da hange, hasali ma ita demokaradiya a kullum tana maraba da banbance-banbancen ra`ayi da samun saɓanin fahimta, kasancewar Allah Ya halicci mutane daban daban, dole ne kowa akwai yadda yake fahimtar abu.

Demokaradiya ta fi amincewa da yi amfani da tattaunawa da musayar ra`ayoyi a matsayin hanyoyin warware saɓani, maimakon amfani da salon tursasawa.

A yayin da wasu gwamnatocin da ba na dimukradiyya ba ke tilasta wa al’ummar da suke jagoranta ra’ayoyi da manufofin da s**a saɓa da buƙatunsu, ita demokaradiya tana dasa ruhin bauta wa talakawa ne a zukatan shuwagabanni na-gari, ba wai ta mai she su wasu gumaka ababen bautar talakawa ba.

Ya ku ƴan uwana masu kishin kasa. A shekaru ashirin da biyar da s**a shuɗe, Najeriya ta tsinci kanta a tsakanin zaɓin ɗayan-biyu na ko dai ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ƴan mulkin k**a-karya ko kuma ta zaɓi tafarkin da ya fi dacewa da ita. A wancan lokacin mun zaɓi matakin da ya fi dacewa, kuma ya wajaba mu ci gaba da bin wannan mataki a yanzu.

A matsayin mu na ƴan kasa, dole ne mu cigaba da tunatar da kawunan mu cewa, duk rintsi da tsananin da ke cunkushe a demokaradiya, ita din ce dai tsarin mulki ɗaya tilo da ya fi dacewa, dole ne mu san cewa a cikin mu akwai wasu ɓata-gari da ke hanƙoron ganin sun yi amfani da ƙalubalen da ƙasarmu ke fuskanta don su samar da koma-baya ga tafarkin demokaradiyar da muka sadaukar da rayukan mu a dominta, idan ma fa ba su rusa shi baki ɗaya ba.

Wannan shine babban yaƙin da ke gabanmu a yanzu, kuma shine dalilin da ya sa muke bikin Ranar demokaradiya.

Babban makasudin bikin wanan rana bai takaita ga tuna-baya ko kyawawan abubuwan da s**a kawo mu war-haka ba. Eh! Tabbas muna girmama rayuka da dukiyoyin da da aka sadaukar domin dora kasar nan a turbar da ta dace. Ni kaina zakaran-gwajin dafi ne a wannan shafin, tunda da ni aka dauki duk wata kasada ta ganin cewa Dimukradiya ta haifar da da-mai-ido a kasar nan, kuma a yau ni ne kan gaba cikin wadanda s**a girbi abinda s**a shuka a tsagin dimukradiyya.

A matsayina na shugaban wannan ƙasa mai albarka, a dabi`a da dokar kasa duka sun wajabta min tsare mutuncin wannan tafarki na gwamnatin dimukradiyya, kuma na lashi takobin kare `yancinku da walwalar ku a matsayin ku na `yan Najeriya. Kai! A shirye nake na taka duk wata rawar da ta dace wajen yin duk mai yiwuwa domin ganin demokaradiya ta cigaba da zama hanyar rayuwar mu.

Duk da cewa ƙalubalen suna da yawa da tsanani, hakan ba zai hana ni nuna farin cikina na zamowa jagoran kasar nan a wannan lokaci mai muhimmanci ga tarihin demukaradiyar ta ba.

Na gurfana a gabanku ne don na jaddada muku mahimmancin aikin da ke gaban mu a yanzu, hakika aikinmu bai takaita ga jure radadi ko iya tunkaran kalubale da makircin `yan mulkin-k**a-karya ba. Ainihin aikin mu shine tunkarar jarabawar da ke gabanmu ta ganin ko za mu yi kasa a gwiwa mu kasa kare demokaradiya kawai don muna zaton inuwar mulkin- k**a karya ta shude.

A nan, kuma a yanzu da muke tsaka da bikin demokaradiyan mu, ina kira a gare mu da mu sake zage dantse wajen ganin mun cika wani sabon buri wanda shi ma yake da matukar mahimmanci. Wannan buri shi ne cinma nasara a yakin bunkasa tattalin Arizikin Najeriya.

Na san muna fuskantar kalubalen tattalin arzikin mai tsanani.

Tattalin arzikin mu ya yi shekaru da dama yana bukatar garanbawul saboda shiga tsaka mai wuya da ya yi sak**akon an gina shi ne akan tubalin toka har ta kai ya kasa samun daidaito saboda dagaro da ya yi a kan kudaden shiga na man fetur kadai.

Mun bullo da sabbin tsare-tsare da za su gina tattalin arzikinmu a kan kwakkwaran tubali da zai kawo ci gaba mai dorewa, ba shakka, sabon tsarin ya haifar da radadi da matsi, sai dai ba mu da wani zabi da ya rage na gyara ga tattalin arzkin kasa wanda amfaninsa zai karade kowa da kowa nan gaba kadan sai ta wannan hanyar.

A yayin da muka dukufa kan gyaran tattalin arzikin kasa,ina mai jaddada muku cewa na dauki alwashin ci gaba da sauraron ra`ayoyin al`ummar Najeriya kuma ba zan taba juya musu baya ba.

Domin samun mafita mun tattauna da kungiyar kwadago da zuciya daya kuma a shirye muke da mu biya mafi karancin albashi. Kuma nan ba da dadewa ba za mu aike da sabon tsarin zuwa ga majalisar dokoki kasar nan domin su sanya hannu kan matsayar da aka cimma ta zama doka na tsawon shekaru biyar masu zuwa.

A yayin da kungiyar kwadago ta yi kiran yajin aikin gama-gari, idan kun lura ba mu dauki matakan muzganawa ko kawo sabani a tsakanin kungiyoyin kwadagon k**ar yadda aka saba gani a gwamnatocin `yan mulkin-mulaka`u ba, maimakon hakan sai muka zabi hanyar samin fahimtar juna. Babu wadda aka k**a ko aka yi wa barazana, maimakon haka an gayyaci shuwagabannin kungiyar kwadago inda aka tattauna da su domin samun maslaha ta bai-daya.

Yin amfani da tattaunawa da hawa teburin sulhu sune tambarin demokaradiya, kuma su ne za su ciga ba da zama tsari na wajen mu`amalantar `yan kasa a a siyasar mu ta inganta tattalin arziki.

Na rungumi wannan tafarki ba tare da jin shayi ko son zuciya ba,kuma zan ci gaba da sadaukar da kai na a wannan bangaren har sai mun gina Najeriya mai iya yin adalci ga kowa.

A karshe ya k**a mu sani cewa ba za mu iya isa ga nasara ta hanya mai sauki ba sai ta hanyar da ta fi dacewa.

Tsohon shugaban kasar Amurka Franklin Roosevelt ya yi gaskiya a shahararriyar maganarsa mai cewa: “Tabbas akwai hanyoyi da dama na samin cigaba, amma daya ce a cikinsu mai dorewa”.

Mu tashi tsaye mu hana idanuwanmu bacci, mu cigaba da tafiya kada mu tsaya a tsakiyar hanya har sai mun shaida cikar burin mu na cigaban Najeriya.

Mun san tudun-mun-tsirar mu tsaf, kuma can za mu dosa. Mu hada ƙarfi da ƙarfe wajen ganin mun ɗora Najeriya da ƴaƴanta a jirgin tsira.

Ya Allah Ka ci gaba da yi wa najeriya albarka, Ka kare mana ita da demokaradiyar mu

Ina yi muku murnar zagoyowar ranar demokaradiya!

Bobrisky ya ɗaukaka ƙara don ƙalubalantar hukuncin ɗaurin wata shida
23/04/2024

Bobrisky ya ɗaukaka ƙara don ƙalubalantar hukuncin ɗaurin wata shida

An sallami wasu sojoji daga aiki bisa yin wata gagarumar sata a matatar manfetur ta DangoteRundunar sojin Najeriya, a ra...
23/04/2024

An sallami wasu sojoji daga aiki bisa yin wata gagarumar sata a matatar manfetur ta Dangote

Rundunar sojin Najeriya, a ranar Litinin, ta ce ta kori sojoji biyu, wadda ya hada da Kofur Innocent Joseph da Lance Kofur Jacob Gani, da ake zargi da satar wasu igiyoyin waya masu muhimmanci a matatar man fetur ta Dangote a ranar 14 ga Afrilu, 2024.

Gidan jaridar PUNCH ya ruwaito yadda sojojin s**a shiga cikin matatar a cikin wata mota kirar Acura jeep amma an cafke su a babbar kofar kamfanin da wayoyin keburan har guda 897.

Yanzu-yanzu: Jirgin kamfanin Dana ya yi hatsari a filin jirgin sama na LagosWani jirgin saman kamfanin Dana Air ya yi ha...
23/04/2024

Yanzu-yanzu:

Jirgin kamfanin Dana ya yi hatsari a filin jirgin sama na Lagos

Wani jirgin saman kamfanin Dana Air ya yi hatsari a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke birnin Lagos da safiyar Talatar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa ba a samu asarar rai ba k**ar yadda Jaridar Leadership ta rawaito.

Har zuwa wannan lokacin ba a samu cikakkun bayanai da game da afkuwar lamarin ba.

Inna Lillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un Allah ya yiwa Jaruma Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso rasuwa.Yan uwan Daso su...
09/04/2024

Inna Lillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un

Allah ya yiwa Jaruma Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso rasuwa.

Yan uwan Daso sun shaida wa Freedom Radio cewa mutuwar fuju’a ta riske ta daga kwanciya barci bayan ta yi sahur.

Za a yi jana’izarta nan gaba a Kano.

Allah ya gafarta mata.

DA DUMI-DUMI: Majalisar dokokin Najeriya ta yi wata doka da zata tilasta a riƙa bawa ma'aikata hutun wata Biyar idan mij...
20/03/2024

DA DUMI-DUMI: Majalisar dokokin Najeriya ta yi wata doka da zata tilasta a riƙa bawa ma'aikata hutun wata Biyar idan mijinsu ko matarsu ta mutu,

A cewar majalisar kwanaki 14 da ake bayarwa a yanzu yayi ƙaranci don haka s**a ƙara. DAGA Mairakumi ta ruwaito yanzu haka dai dokar ta tsallake karatu na Biyu a zauren majalisar.

SHUGABA TINUBU YA UMARCI MINISTOCI SU TABBATAR ANA AMFANI DA SAKAMAKON BINCIKEN DA AKE YI A KOWANE FANNIShugaban ya bayy...
08/03/2024

SHUGABA TINUBU YA UMARCI MINISTOCI SU TABBATAR ANA AMFANI DA SAKAMAKON BINCIKEN DA AKE YI A KOWANE FANNI

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabar ƙungiyar makarantun kimiyya, ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa, Abuja.

Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito Tinubu ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta kai wani mataki na cigaba wajen rungumar fasahohi da ƙirƙire-ƙirƙire na ƴan Najeriya waɗanda za su samar da masalaha a kowane fanni na rayuwa waɗanda s**a haɗa da Noma, ƙirƙira, fasahar zamani da harkokin sadarwa da fannin ilimi.

"Ministan ilimi, ministan lafiya da walwalar al'umma, da ministan kasafi da tsare-tsare duk suna wannan waje. Duk wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnati ya zama wajibi su zauna su tabbatar da cewa sak**akon binciken kimiyya ya zama hanyar da za ta jagoranci inganta fannoni daban-daban masu fa'ida. Lallai ka da mu yi ƙasa a gwiwa wajen amfani da sak**akon bincike". -Shugaban ƙasa.

A nata tsokacin shugabar ƙungiyar makarantun kimiyyar, Farfesa Ekanem Braide, ta gode wa shugaban ƙasar bisa goyon bayan da yake ba wa asusun gudanar da bincike na ƙasa, inda ta ƙara da cewa ba shakka hakan zai taimaka wajen magance matsalolin da ake fuskanta tare da taimaka ƴan ƙasar ta kowane fanni.

ELRUFA'I NA BIYU: Gwamna Bago Na Jihar Neja Ne  A Duke Yana Gaida Shugaba Tinubu
08/03/2024

ELRUFA'I NA BIYU: Gwamna Bago Na Jihar Neja Ne A Duke Yana Gaida Shugaba Tinubu

Tinubu ya kori shugabannin kula da wutar lantarki da ake zarginsu da almundahana ya naɗa ɗan Ganduje ya maye gurbinsuShu...
08/03/2024

Tinubu ya kori shugabannin kula da wutar lantarki da ake zarginsu da almundahana ya naɗa ɗan Ganduje ya maye gurbinsu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugabannin gudanarwa na hukumar samar da wutar lantarki a karkara bisa zargin almundaha tare da maye gurbinsu da wasu ciki har da Umar Abdullahi Umar, ɗa ga mai girma tsohon gwamnan Jihar Kano, kana kuma shugaban riƙo na jam'iyyar APC ta ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito, waɗanda shugaban ƙasar ya dakatar ɗin sun haɗa da:

1. Alaniyi Alaba Netufo, a matsayin babban daraktan hulɗa.

2. Barka Sajou, a matsayin babbar darakta kan harkokin gudanar da ayyuka

3. Sa'adatu Balgore, a matsayin babbar darakta kan harkokin kuɗaɗen gudanarwar hukumar.

Baya da haka, shugaban ƙasar ya buƙaci a zurfafa bincike a kansu dangane da tuhumar da ake musu ta kashe sama da Naira Biliyan 1.2 ba bisa ƙa'ida ba shekaru biyu baya. Wanda kuma tuni hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta samu nasarar gano wasu daga cikin kuɗaɗen.

Nan take kuma, shugaban Tinubu ya umarci a maye gurbin waɗanda aka dakatar ɗin da wasu ƴan ƙasa waɗanda s**a cancanta a matsayin riƙon ƙwarya. Waɗanda aka naɗa ɗin sun haɗa da:

1. Abba Abubakar Aliyu, a matsayin shugaba.

2 Ayoade Gboyega, a matsayin babban daraktan hulɗa.

3. Umar Abba Umar, a matsayin daraktan ayyuka.

4. Doris Uboh, daraktan kuɗaɗe na hukumar.

5. Alufemi Akinyelure, shugaban kulawa da gudanuwar ayyuka.

Shugaba Tinubu ya h**e su da su gudanar da ayyukansu daidai da ƙudiri da tanadin doka.

Address

Hadejia

Telephone

+2349030510709

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DAGA Mairakumi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to DAGA Mairakumi:

Share