09/10/2025
DA DUMI-DUMI: Gargaɗi ga ƙasashen Afirka musamman Najeriya da Arewa: A yi hattara da magungunan tari daga Indiya
Gwamnatin Indiya ta gano wasu manyan matsaloli wajen gwajin magungunan tari da wasu kamfanonin ƙasar s**a ƙera, bayan da aka danganta mutuwar yara 17 da shan magungunan da s**a ƙunshi sinadarin diethylene glycol, wani guba mai haddasa lalacewar koda, jijiya da ma mutuwa.
Rahoton majiyar Muryoyi ta jaridar Reuters ya bayyana cewa magungunan da ake bincike sun haɗa da Coldrif, Respifresh, da RELIFE, waɗanda aka samu da sinadarin da ya fi na daidaitaccen ƙima sau 500.
Muryoyi ta ruwaito wannan matsala ta janyo hankalin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wadda ta yi gargadin cewa Indiya ba ta kula sosai wajen gwajin magungunan kafin su shiga kasuwa, abin da ke iya sa su yadu zuwa ƙasashen waje, ciki har da ƙasashen Afirka.
Masana sun ba da shawarar cewa jama’a su daina siyan magunguna ba tare da shawarar likita ba, kuma su tabbatar cewa kowanne magani da suke saya yana da rajista daga hukumar NAFDAC domin guje wa haɗarin guba da mutuwa.
KUN SAN MAGUNGUNAN?