30/08/2026
70 YEARS ANNIVERSARY 1956 - 2026..
MAULUDIN ~ NABIYY [S.A.W] IBADAN 1448/2026..
TAQAITACCEN TARIHIN MAULUDI A IBADAN..
MAULANMU SHEHU MALAM ABDUWA KOKI KANO [Radiyallahu Anhu] ALLAH YA SAKA MASA DA ALKHAYR..
Shine Wanda Ya Assasa Mana Wannan Alkhayri [MAULUD] Wanda Babu K**arsa, Yau Bana 2026/1448 Mauludi Yake Cika Shekaru SABA’IN [70] Da Kafuwarsa A Wannan TSARI Na Zaman HAIHUWA Da SUNA..
Amma Kafin Zuwan Shehu Malam Abduwa Koki [Radiyallahu Anhu] Ana Zaman Mauludi [NA RABIN DARE] Wanda Su SHEIKH MALAM MUHAMMAD INUWA ALIYYU ZARIA [R.A] Da SHEIKH MALAM UKASHATU KURNA [R.A] Da Sauran Sadatu Suke Jagoranta Wanda Sun ‘Dauki Shekaru TAKWAS [08] Suna Yi..
Amma Da Shehu Malam Abduwa Koki [Radiyallahu Anhu] Yazo, Sai S**a Sallama Masa Gabaki ‘Daya Musamman Daya Fad’a Musu Cewa Ya Fitone Da IZININ SHEHU MALAM TIJJANI BIN USMAN ZANGON BARE BARI KANO [R.A]..
Shehu Malam Muhammad Inuwa Aliyyu Zaria [R.A] Saboda SALLAMAWARSA Ga Shehu Malam Abduwa Koki [R.A] Hatta Bada ‘Dariqa Saida Ya Daina, Tareda Yanada Cikakken Izini MU’DLAQI, Idan Akazo Karbar ‘Dariqa Yana ZAWIYYARSA Tsallake Gidan ALHAJI IYAJI Kakan Chairman ’Dinmu Na KHUDDAMUL FAYDHA [ILAN] Sai Ya K**a Hannunka Ya Tsallako T**i Har Zawiyyar Shehu Malam Abduwa [Radiyallahu Anhu] Unguwar ‘Yan Ata Gidan ALHAJI SABO, Mahaifin ALHAJI AMINU WAZIRI Sai Shehu Malam Abduwa [R.A] Ya Baiwa Wanda Yazo Kar’bar ‘Dariqa Izini..
Hatta Bada ILIMI Saida S**a Daina S**a Koma Qarqashin Shehu Malam Abduwa Koki [R.A]..
SAHIBUL FAYDHA SHEIKH IBRAHEEM NIASSE [Radiyallahu Anhu] Shine Wanda Yake MAULUDI, Ayi ZAMAN HAIHUWA A DAREN 12 Ga Rabi’ul Auwal, Bayan Kwana 7 Asake Zaman SUNA..
SHEHU MALAM TIJJANI BIN USMAN KANO [Radiyallahu Anhu] Shine Kaff NIGERIA Ya Fara ASSASA Kwaikwayon Wannan Tsari Na MAULUDI Ayi Zaman HAIHUWA Da SUNA..
Shi kuma Maulanmu Sheikh Malam Abduwa Koki Kano [R.A] Wanda Shine Babban ALMAJIRIN Shehu Malam Tijjani Bin Usman [R.A] Ya Kwaikwaya Daga Shehinsa, Shehu Malam Tijjani Bin Usman [R.A] Shi Ya ASSASA Wannan Tsari A Gabaki ‘Daya KUDU [SOUTH WEST]..
Wanda Gabaki ‘Daya Daga LAGOS, OGUN, OSUN Da Sauran Jihohi Ana Had’uwa A IBADAN A Gabatar Da Mauludi..
Da HIMMAR MAULANA KHALEEFA IBADAN Sheikh Ibraheem Inuwa Aliyyu Zaria [R.A] Magajin Asiransu Gabaki ‘Daya Har Kawo Yau Al’amarin Sai Qara Cigaba Yake Da Bunqasa [LAMARIN SAI WANDA YAZO YA GANI DA IDONSA]
Muna Roqon Allah Da Albarkan Manzan Allah [Sallallahu Alaihi Wasallam] Ya Jaddada Musu Rahama Ya Kula Da Bayansu..
MAULANMU KHALEEFA Allah Ya Qara Masa Kyakkyawan Jagoranci Albarkan Manzan Allah [Sallallahu Alaihi Wasallam]..
LAHADI 30TH-AUGUST-2026..
ABDULLAHI MUHAMMAD INUWA [A.K.A ]
ABBA KHADIMU ✍️
[DIRECTOR GENERAL] KHALEEFA IBADAN MEDIA 🎤📸
08064953787