05/09/2025
ZIYARAR GANI DA IDO: YADDA RUWA YA YI AMBALIYA A KWARIN YAÆŠIYA TARE DA TAFIYA DA GONAKIN AL'UMMA
Sakamakon ruwan saman da aka yi jiya kamar da baƙin ƙwarya ya sabbaba asara a Kwarin Yaɗiya, musamman yadda ruwa ya tafi da gonakin al'umma.
Hakan ya sa ƙasar da aka yi cikon katafariyar gadar nan ta Kwarin Yaɗiya ruwa ya tafi da ita, amma cikin yardar Allah gadar ko gezau ba ta yi ba, domin an yi ingantaccen aiki, aikin da za a ɗauki tsawon zamani al'umma su na amfana da shi, domin aiki ne Mahadi ka ture.
Al'ummar yankin Kwarin Yaɗiya da su ka ba da shaidar gani da ido, sun tabbatar da ba a taɓa yin ruwa mai ƙarfin na jiya ba, wanda hakan ya sabbaba asarar gonakin al'umma, kuma cikin yardar Allah gadar ba ta yi ko gezau ba, saboda aiki ne mai cike da inganci.
Al'ummar yankin Kwari sun sake jaddada godiya ta musamman ga Shugaban Karamar Hukumar Ikara, Hon. Bashir Muhammed (RAJA) na yadda ya yi musu wannan ingantacciyar gada, wacce duk wannan ruwan da aka yi gadar ba ta yi komai ba, lallai wannan ruwan ya sake tabbatar musu da ingancin wannan gada..