02/12/2025
Babban matakin karfin hali da namiji zai kai a rayuwa shine lokacin da duniya ta juya masa baya, amma ya ki karaya.
Ka zama irin namijin da zai iya fuskantar:
Rabuwa da masoyiya.
Rasa aikin yi ba zato ba tsammani.
Ko shiga bashi mai tarin yawa.
Amma duk da haka, ya kalli kansa a madubi, ya share gumi, ya ce: "Zan samu mafita"
Kuka da ba da uzuri ba dabi'un maza bane.
Namiji na gaske baya zama yana lissafin "Me yasa abin ya faru," yana tashi ne yana lissafin "Yadda zai gyara abin da ya faru."
Kada ka bari tsoro ya cinye ka. Kai ne mai gidanka, kai ne direban rayuwarka. Matukar kana numfashi, akwai mafita.