03/03/2024
NASARORIN DA MUKA CIMMAWA TUN BAYAN K**A RANTSUWAR AIKI A OFFICE
A Cikin kasa da kwanaki dari da goma da rantsar da Dan Majalissar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kankia Kusada da Ingawa Rt.Hon Abubakar Yahaya Kusada ,wadannan sune wasu daga cikin abubuwan da muka aiwatar a yankunan:
1.Ya raba Mashina 36 ga dukkanin wards 31 dake yankin Kankia Kusada da Ingawa.
2..Bada kekunan Dinki ga Mata dansu dogara da kawunansu a fadin Kankia Kusada da Ingawa
3.bada injinan markade ga wasu Alummar kankia kusada Ingawa dansuyi amfani Dashi su dogara da kansu
4.Saka Fitulu masu amfani da hasken Rana (Security Light):
a. A garin Kafarda dake Karamar hukumar kusada
b. A garin Magam dake Karamar hukumar kankia
c. A garin Ganjuwa dake Karamar hukumar Ingawa
D.A garin Dara dake Karamar hukumar Ingawa
5.Bayarda Gudummuwar 200k a makarantar CAIS kusada
6.Bada Horo ga matasa 31 Kan Sana'ar gyaran waya da Basu tallafin kudi Naira *N930,000* Wanda kowannensu ya amfana da 30K
7.Bada jari na N930,000 ga wasu mutane maza su 31 daga kowacce ward inda kowa ya amfana da 30K
8.Bada tallafin kudi N620,000 ga mata su 31 da s**a fito daga kowacce ward inda kowace ta amfana da 20k
9.Bada kyautar freezers guda ukku ga wasu mata su ukku daya daga kowace Karamar hukuma domin dogaro da kansu.
10.Bada kyautar freezer ga Bishir Rabi'u yashe Da Allah ya jarabta da konewar shago Danrage radadin abinda aka rasa.
11.Ana kan kokarin Samar da Admission guda 100 tare da Biyama Matasa 100 Yan kankia kusada Ingawa kudin Registration Wanda zasuyi karatun N.C.E Dana Diploma harsu Gama kyauta
12.Samar da Jamb Forms da biyan kudin PIN Registration guda 120 ga dalibai Wanda aka dauko a dukkanin makarantun Sakandire dake Yankin kankia kusada Ingawa anyi zaben ne ga yara masu kokari da wadanda basu da karfi
13.Samar da injinan Ban ruwa ga wasu daga cikin manoma ranin kankia kusada da Ingawa
14.Bada Tallafin kudade ga wasu daga cikin matasanmu maza da mata,matasa da dattawan kankia kusada Ingawa Dan inganta sana'o'insu
15.Kaddamar da cigaba da aikin hanya mai tsawon 5km a Garin kankia wacce ta taso daga kusa da hanyar kafindangi ta shigo ta Kofar fada zata bulle har 1 Million Road
16.Gyaran Famfuna a 'Yar Bare da Daunaka makaranta dake a karamar hukumar Ingawa
17.Bayar da gudummuwar Sabon generator a Masallacin Jibwis na juma'a dake garin 'Yandoma
18.Bayar da kekunan dinki ga wasu bayin Allah su ukku da s**a fito daga kananan hukumomin Kankia Kusada da Ingawa
19.Shirya wasan sada zumunci ga matasa na kwallon kafa ga matasan Kankia Kusada da Ingawa tare da bada kyautar Kofi,kudade,kwallo,jersey ga dukkanin kungiyoyin da s**a shiga gasar
20.Gudummmuwar 100k ga Wani bawan Allah Amadu Mai takalma
21.Biyan kudin bude Centre ta BECE da SSCE duk a Makarantar Sakandire ta Dugul dake Karamar hukumar Ingawa
22.Gudummuwar Sabon Generator a masallacin Jummaβa dake garin Yashe
23.Tallafin kudi na Million daya da dubu dari ukku da goma N1,310,000.00K ga wasu matasa su goma sha hudu da s**a fito daga yankunan Kankia Kusada da Ingawa
Insha Allah zamu cigaba da kawo abubuwan da Dan Majalissar tarayyar ya aiwatar lokaci bayan lokaci tare da karbar shawarwarin al'umma
Ibrahim Abubakar Ingawa
S.A On Digital Media to The MhOR Kankia Kusada and Ingawa Federal Constituency
03/03/2024