12/09/2025
SANARWA TA MUSAMMAN DAGA OFISHIN KWAMISHINAN HARKOKIN JIN ƘAI DA AYYUKA NA MUSAMMAN
ƘARIN BAYANI DANGANE DA ƊAUKAR MA'AIKATA NA NIGERIA CUSTOMS SERVICE DA SUKE GUDANARWA
Mai Girma Kwamishinan Harkokin Jin Ƙai da Ayyuka Na Musamman na sanar da jama'a, musamman al'umar Jihar Jigawa, game da aikin da Hukumar Kwastam ta Najeriya ke ɗauka a halin yanzu.
Kashi na biyu na aikin, wato Jarabawar Kwamfuta (CBT), zai gudana ne daga ranar 14 zuwa 21 ga Satumba, 2025. Ana buƙatar waɗanda s**a samu nasarar wuce mataki na farko, su yi amfani da kwamfuta Laptop ko kwamfutar tebur (desktop) mai kyamarar gizo-gizo da kuma ingantaccen intanet don yin jarabawar. Haka kuma, za a gudanar da jarabawar gwaji wanda dole ne na kwana biyu kafin ainihin CBT don taimakawa masu neman su san da yadda tsarin yake.
Ga duk wata tambaya da ta shafi wannan aikin, ana shawartar waɗanda s**a samu nasara daga Jihar Jigawa su tuntubi Hukumar Bada Shawara da Kula da Bada Jagoranci ta Jihar Jigawa wato Jigawa State Guidance and Counseling Board don neman ƙarin bayani da tambayoyi.
Muna yi wa dukkan masu nema fatan alheri a wannan Jarabawar.
Sa hannu,
Hon. Auwal D. Sankara (F**a),
Mai Girma Kwamishina
Ma'aikatar Harkokin Jin Kai da Ayyuka Na Musamman,
Jihar Jigawa