03/01/2026
An gano wasu muhimman bayanai dangane da dalilin da ya sa aka dage shirin ficewar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC mai mulki, duk da an riga an kammala shirye-shirye tun da farko.
A ranar Juma’a, jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa gwamnan ya kammala dukkan shirye-shirye na sanar da ficewarsa zuwa APC a ranar Litinin.
Kafin dagewar shirin sauya shekar jam’iyyar, hedkwatar APC ta kasa ta shirya cewa gwamnan zai kasance mutum na farko da za a yi wa rajista a Kano a sabon tsarin rajistar jam’iyyar ta yanar gizo.
A cewar tsarin da aka tsara tun farko, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ne zai raka gwamnan zuwa Mazabarsa ta Diso, domin yin rajista a shafin jam’iyyar tare da karɓar katin zama mamba.
Bayan kammala rajistar gwamnan, an tsara cewa shi kuma zai raka Ganduje kai tsaye zuwa garinsu na Dawakin Tofa, domin Ganduje ya sabunta rajistarsa a sabon tsarin rajistar APC.
Sai dai majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun ce an dakatar da wannan tsari ne bayan an ja hankalin gwamnan cewa ya dace ya fara ganawa da manyan shugabannin APC a Kano, musamman Abdullahi Ganduje da Sanata Barau Jibrin, domin neman albarkarsu kafin sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.
Wata majiya da ta san abin da ke faruwa ta ce:
“Idan gwamna ya fice ba tare da ya gana da Ganduje, Sanata Barau da sauran shugabannin APC ba, hakan zai nuna kamar ya raina su, kuma hakan ba zai yi masa kyau ba.”
Ko da yake jaridar Platinum Post ta ruwaito cewa gwamnan zai sanar da ficewarsa a ranar 12 ga Janairu, wasu majiyoyi sun ce ranar ba ta tabbata ba tukuna, kuma lamarin na iya faruwa “a kowace rana bayan ya gana da shugabannin APC na Kano.”
Wasu majiyoyi kuma sun bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya bayar da umarnin a dakatar da shirin ficewar, har sai an yi kokarin karshe na shawo kan uban gidan siyasar gwamnan, Rabiu Musa Kwankwaso.
A cewar majiyoyin, shirin Kwankwaso na komawa jam’iyyar ADC ya sauya lissafin APC gaba daya.
“Fadar Shugaban Kasa na da bayanan sirri cewa Kwankwaso ya gana da Olusegun Obasanjo da Peter Obi, kuma akwai yiwuwar su hada kai domin kalubalantar Tinubu a zaben 2027.
Hadakar Obi/Kwankwaso hadaka ce mai karfi wadda za ta iya sauya tsarin siyasar APC.
“Kuma ba tare da Kwankwaso ba, karfin siyasar gwamnan yana raguwa sosai. Saboda haka Tinubu na sake tunani kan batun karɓar ficewar Gwamna Yusuf.
“A gaskiya, gwamnan ne ke neman shiga APC, ba APC ce ke nemansa ba. Shi ya sa har yanzu babu wani tsayayyen sharadi kan rabon matsayi ko iko bayan ficewarsa,” in ji wata majiya.
Sai dai wasu majiyoyi sun shaida wa wannan jarida cewa gwamnan da kansa ne ya nemi a kara masa lokaci, domin samun damar shawo kan karin ‘yan Majalisar Jiha da na Tarayya su bi sahunsa wajen sauya sheka.
Wasu majiyoyi da ba a tabbatar da sahihancinsu ba sun kuma ce tsananin martanin da gwamnan ke fuskanta daga bangarori daban-daban ya sanya shi cikin rudani, har ya fara tunanin janye shirin ficewar gaba daya, ya koma ya sasanta da uban gidansa na siyasa, Rabiu Musa Kwankwaso.