11/09/2024
Saƙon Jaje wa Al'ummar Maiduguri!!!
Tabbas akwai tashin hankali da tausayi a irin yanayin da al'ummar Garin Maiduguri s**a samu kan su a ciki.
Mutum ya wayi gari gidansa da inda yake neman abinci duk ruwa ya cinye, ga asarar dukiya da rashin sanin ina ya zai kai iyalansa su kwana!
Allah muna roƙonka da dukkan sunayenka kyawawa, da siffofinka maɗaukaka Ka kawo wa al'ummar Maiduguri mafita akan wannan jarabawa da s**a samu kansu aciki!
Ya Allah Ka maida musu mafi alkhairin abinda s**a rasa, Kasa wannan asarar ya zamo musu kaffara, ka kawo musu zaman lafiya da cigaba a jihar baki ɗaya.
Ya Allah Ka amintar da mu a garuruwanmu Ka shiryar da jagororinmu da majiɓinta lamuranmu ba dan halin muba ya Allah.