30/12/2024
Matar da ke ษauke da ciki ta ce wa mijinta, "Me kake fata na haifo, namiji ko mace?"
Mijin ya yi murmushi ya ce, "Idan muka samu namiji, zan koya masa lissafi, za mu tafi mu yi wasa, kuma zan koya masa kamun kifi."
Matarsa ta sake tambaya, "Idan mace ce fa...?"
Mijin ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Idan muka samu mace, ba zan mata koya mata komai ba."
Matarsa ta tambaya cike da Mamaki , "Me yasa?"
Mijin ya amsa, " bazan koya mata duk waษannan hidimomi ba a haka ฦดaฦดa Mata ake haifarsu. idan na fara tsufa zata Koyamin yadda zan saka kaya, yadda zan ci abinci, abin da zan ce da abin da ba zan ce ba. Ta wani ษangaren za ta zama mahaifiyata ta biyu. Za ta ษauke ni a matsayin jaruminta, ko da ban yi mata wani abu na musamman ba."
"Ko da yaushe idan na hana ta wani abu, za ta fahimce ni. ko da yaushe zata dinga kwatanta mijinta da ni. Ko abinci ta dafa ta kawo min sai ta tabbatar ta ga na ci sannan zata tafi, Ko tufafi ta siyamin sai ta ga na gwada yayi min kyau sannan ta tafi gida. za ta so ni ta Kula dani da yimin hidima kamar yadda Yara Mata ke so da yiwa ฦณar "tsana" loฦacin da suna yara."
"Za ta yi yaฦi da duniya saboda ni, idan wani ya cutar da ni, ba za ta taษa yafe musu ba."
Matar ta yi murmushi ta ce, "To, kana nufin duk abin da ษiyarka za ta yi, ษanka ba zai iya yi ba?"
Mijin ya ce, "A'a, a'a, wa ya sani, ษana zai iya yin haka, amma na tabbatar ba zai iya yimin hidima irin ta ฦดa mace ba. ษiya mace ana haifarta da waษannan halaye ne. Babban Matakin Nasara ne ga kowane mutum ya zama mahaifin 'ya mace."
Matar ta ce tare da ษan hawaye a idanunta, "Amma ba za ta kasance tare da mu kullum ba...?"
Mijin ya rungume ta ya ce, "Eh, amma za mu kasance a zuciyarta kullum. Ba ya da muhimmanci inda ta je, 'ya'ya mata mala'iku ne da Allah ke aiko su ga iyaye Maza don hidimta musu haife su don samun kauna da kulawa mara iyaka."
"'Ya'ya mata ba sa cikin kaddarar kowa Ya Haife su, 'ya'ya mata ana haifar su a gidan da Allah ke so."
Allah ya bamu ฦณaฦดa Nagari.