
02/06/2025
*DAN UWANA BARI NA BAKA WANI SIRRI...*
Ya dan uwaNa mai Albarka ka rike wanan sirri in sha Allahu zai taimake ka da izinin Allah. Wanan sirri kuwa shine:
1. Ka zama mai fita masallaci domin Sallar Asubahi acikin jam'i lallai akwai wani sirri tattare da duk wanda yake sallatar asubah acikin jam'i.
2. Ya zama idan zaka fita ka dan fita da kudi, idan nace kudi ba ina nufi kudi irin nasu Alhaji wane ba, ah ah ina nufin kudi ko ya yake, naira 500 ce naira 1000 ce, naira 2000 ce kudi dai mai k**a da haka.
3. Bayan kayi Sallah kayi tasbihi ka duba kaga daga cikin mutanan dake masallacin waye yake da alamar yana da bukata, kayi masa kyauta da abinda Allah ya h**e maka cikin sirri.
4. Kaga idan ka bude yininka da Sallar asubah acikin jam'i da tasbihi da sadaka zuwa ga mabukaci sanan kace "Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faqir" Akalla sau dari, sanan kace "La ilaha illallahul malikul haqqul mubin" Shima sau dari hmnnn brother zaka sha mamaki.
Nasan zaka tambayen to maye sirrin bayan kayi haka, brother karka tambayen kawai ka gwada da kanKa zaka gane sirrin dake cikin hakan, kuma in sha Allahu zakai min addua, kuma kaima zaka sanar da wasu kuma zasuyi maka addua, kaidai kawai ka jarraba tare da tsarkake niya ka jira kaga ikon Allah, Musanman acikin kwanaki goman nan da muke ciki. ya k**ata fah ku fara bada abin Sadaka fahπ.
*DR JAMEEL MUHAMMAD SADIS ZARIA* π€