17/11/2025
Sunan sa ; Muhammadur Rasulullah (ﷺ)
Sunan mahaifin sa ; Abdullahi Ibn Abdulmuɗallib
Sunan mahaifiyar sa ; Aminah Bint Wahab
Sunan Qabilar sa ; Quraishu.
Sunan dangin sa ; Banu Hashim.
Sunan unguwar zomar da tazo tarar haihuwar sa; Sayyada Shaffa'u.
Sunan wacce ta shayar dashi; Halimatu sadiya.
Sunan garin da aka shayar dashi; Banu Sa'ad.
Sunan garin da yaje kafin nubuwa; sham.
Sunan malamin da ya fara gane shi Annabi ne tun yana ɗan shekara sha biyu ; Bahira.
Sunan Jakin sa ; Ya'afuru.
Sunan dokin sa ; Duldulu
Sunan alfadarin sa ; Ufairu.
Sunan taguwar sa; Qaswa'u
Sunan takubban sa ; Qal'aya, Hatafu & Battaru.
Sunan kogon da aka farai masa wahayi ; Hira.
Sunan kogon da ya shiga lokacin hijira; Sauru.
Sunan wanda ya nuna musu hanya lokacin hijira; Abdullahi Bin Uraiƙiɗil laisi.
Sunan abokin sirrin sa ; Huzaifatul yaman.
Sunan dutsen da yabawa aljannah; Uhudu.
Sunan mawaƙan sa; Ka'abu, Hassanu da Abdullahi Bin rawaha etc.
Sunan kwamandojin yaƙin sa; Khalid Bin Walid, Ja'afar Bin Abu Dalib etc.
Sunan zaagin sa; Abdullahi Bin Mas'ud.
Ya rayu a garin makka shekara hamsin da uku (53) ya rayu a madinah shekara goma.
Ya isar da saƙon sa a shekara a shirin da uku.
Yayi yaƙuna guda ashirin da bakwai (27).
Allah (SWT) ya ƙara masa tsira da aminci.
- Khalifa Imam Abdulqadir