
05/05/2025
TAKAITACCEN TARIHIN ALHAJI ALIYU MAI BORNO
An haifi Mallam Aliyu Mai Bornu ne a shekarar 1919 sannan ya fara makaranta firamari a shekarar ta 1932. Daga baya aka koma da shi makarantar sakandare ta Yola daga nan ya tafi kwalejin Kaduna a shekarar ta 1938 sannan ya kamala karatun sa a shekara ta 1942 bayan ya cancanci ya zama Malami Mai koyar da Ingilishi.
Mallam Mai Bornu ya koyar da Ingilishi a makarantar, Yola Middle School daga shekara ta 1942 zuwa 1946 sannan ya koma zuwa Kwalejin Kaduna inda yaci gaba da koyarwa a shekara ta 1954, sannan kuma ya yi aiki a matsayin Mai Kula da Gidan Makaranta a Veterinary School kafin nan ya tafi zuwa Jami’ar Bristol duk dai a shekara ta 1954, don nazarin tattalin arziki (Economics).
Bayan kammala karatunsa a shekarar 1957, ya dawo Najeriya ya kuma yi aiki tare da ma’aikatar kula da jama’a ta Arewacin Najeriya a matsayin Babban Jami’in Gudanarwa inda ya rike mukamai daban-daban kafin nan yasamu zuwa Babban Bankin Najeriya a 1959 a matsayin Mataimakin Sakatare a CBN.