16/01/2023
Hotuna 📷 Major Enzegwu Kaduna Da Kabarinsa A Kaduna.
Patrick Chukwuma “Kaduna” Nzeogwu hafsan sojan Najeriya ne wanda ya taka rawa a juyin mulkin farko na soja na 15 ga Janairun 1966, wanda a ka hambarar da jamhuriyar Najeriya ta farko. Wanda shi ne da kansa ya Kashe Sir Amadu Bello Sardauna.
An haifi Patrick Chukwuma Nzeogwu a Kaduna babban birnin yankin Arewa iyayensa al’ummar Anioma a Garin Okpanam na Yankin Tsakiyar Yamma (kusa da Asaba a Jihar Delta a yau ).
Nzeogwu Kaduna ya halarci makarantar firamare ta Katolika ta Saint Joseph da ke Kaduna in ya yi karatun firamare sannan kuma ya yi karatun sakandire a makarantar Saint John's College duka Dai A Kaduna.
A watan Maris na shekarar 1957, Nzeogwu ya shiga aikin sojan Najeriya rejiment na rundunar sojojin Afirka ta Yamma kuma ya ci gaba da samun horon sharar fage na watanni 6 a Ghana, sannan a kirata da (Gold Coast) Ya k**alla horonsa a Ghana a watan Oktoban 1957 sannan ya wuce Royal Military Academy, Sandhurst inda daga nan Ya zama sojan kasa a shekarar 1959.
Daga baya ya yi kwas na jami'an rundunar a Hythe da kwas na kwamandan runduna a Warminster. Max Siollun, wani masanin tarihi na soja ya bayyana Nzeogwu a matsayin Kirista dan Darikar "katolika mai kishin katolika, Wanda ko taba sigari baya sha.
Aikin soja
A lokacin da ya dawo Najeriya a watan Mayun 1960, Nzeogwu an tura shi zuwa Bataliya ta daya da ke Enugu inda Manjo Aguiyi-Ironsi ya kasance babban kwamanda na biyu a karkashin wani jami’in Birtaniya.
Daga baya aka tura shi bataliya ta 5 da ke Kaduna inda s**a yi abota da Olusegun Obasanjo. Abokan aikinsa Hausawa a cikin sojojin Najeriya ne sanya masa suna " Kaduna " saboda alakarsa da garin.
Bayan ya yi aiki kiyaye zaman Lafiya a Kongo a 1961, Nzeogwu ya zama jami'in horaswa na sojoji a Depot da ke Zariya na tsawon watanni 6 kafin a tura shi Legas. ya jagoranci sashin leken asirin soja a hedkwatar sojojin in da ya kasance jami'i dan Najeriya na farko, Wanda ya jagoranci rundunar leken asiri ta Sojojin Najeriya (NAIC) shi ne Sashen Tsaro (FSS) na Rundunar Sojojin Najeriya, wanda aka kafa a ranar 1 ga Nuwamba 1962 tare da Kyaftin PG Harrington (BR) a matsayin Babban Hafsan Soja na Grade Two (GSO2 Int). FSS da gaske kungiyar tsaro ce wacce ayyukanta s**a hada da tantance jami'an Sojojin Najeriya (NA), da daftarin tsaro da bayanan sirri.
Manjo Nzeogwu shi ne jami’in Najeriya na farko da ya rike wannan mukami daga watan Nuwamba 1962 zuwa 1964. A matsayinsa na jami’in leken asiri na soja, ya shiga cikin binciken manyan laifuka na cin amanar kasa da aka yi wa Obafemi Awolowo da jam'iyyarsa ta AG (Action Group) A cewar Olusegun Obasanjo , "Chukwuma yayi wasu zafafan kalamai game da tsaron kasa [Najeriya], da kuma wadanda ake bincike.
An ruwaito cewa Nzeogwu ya caccaki wasu abokan aikin soja a matsayinsa na jami'in leken asiri na soja har ma s**ayi musayar kalamai masu zafi da karamin ministan soji, Ibrahim Tako.
Saboda haka sai aka tura shi Kwalejin Horar da Sojoji ta Najeriya da ke Kaduna inda ya zama Babban hafsa.
Juyin mulkin 15 Ga Watan Junairu 1966
Shirye-shiryen juyin mulkin ya fara ne da wasu gungun matasa masu ilimin jami'a wadanda s**a yi niyyar juyin juya hali na soja na kasa ta hanyar kwace iko a manyan biranen yankin Kaduna (yankin Arewa) da Ibadan (yankin Yamma), daga bisani kuma s**a kwace iko da Legas (Tarayya) An ba Nzeogwu alhakin jagorancin juyin juya hali a yankin Arewa wanda ya fara da Operation Damisa a ranar 15 ga Janairu 1966, sannan daga baya, Operation Kura, Operation Zaki da Operation Giwa wanda zai kai ga kisan gillar da aka yi wa manyan 'yan arewa.
Nzeogwu ya fara shirye-shiryensa ne ta hanyar shirya atisayen dare na kwana biyu "Damisa" (Operation Tiger) domin horar da sojoji sabbin dabarun yaki. Hukumomin hedikwatar Brigade ta daya ce ta amince da atisayen bisa dukkan alamu ba su san ainihin manufar Nzeogwu ba, da Brigade Manjo Alphonso Keshi ya aike da kasidu ga dukkan sassan da ke aiki a karkashin Brigade domin bayar da gudunmawar sojoji domin samun nasarar atisayen. A lokacin da Manjo Keshi ya fahimci cewa "Operation Damisa" wani makarkashiyar soji ne, Amma ina!! an Riga an makara wajen dakile aikin.
A safiyar ranar 15 ga watan Janairun 1966, Nzeogwu ya jagoranci wasu gungun sojoji a wani atisayen soji, inda s**a kai su farmaki kan gidan firayim ministan arewa, Sir Ahmadu Bello a wani juyin mulkin da ya yi sanadiyar mutuwar sa da mutane da dama.
Ciki harda Firimiyan Yammacin Najeriya Samuel Akintola, An kuma kashe firaminista ( Abubakar Tafawa Balewa ) da ministan tarayya ( Festus Okotie-Eboh ) da kuma manyan hafsoshin soja daga yankunan Arewa da yammacin kasar nan.
Firayim ministan yankin Gabas ( Michael Okpara ), shugaban tarayyar Najeriya ( Nnamdi Azikiwe ) da kuma shugaban sojoji ( Johnson Aguiyi-Ironsi).) Dukkanin Yan Kabilar ibo sun kasance sanannun waɗanda s**a tsira, Ba'a Kashesu ba.
A cewar wani rahoto na musamman na rundunar ‘yan sandan Najeriya, Nzeogwu ya kashe akalla sojoji 4 da jami’an tsaro na ‘yan sanda ciki har da daya daga cikin mutanen da ke cikin tawagarsa (Sajan Daramola Oyegoke). Nzeogwu ya kashe Kanar Raph Shodeinde, babban jami’insa a Kwalejin Horar da Sojoji ta Najeriya, kuma rahotanni sun ce ya harbe mata da kananan yara da s**ai Yunkurin gudu ba gaira ba dalili.
Bayan jiran sanarwar da aka yi da sanyin safiyar ta rediyo daga Manjo Adewale Ademoyega a Legas wanda hakan bai faru ba saboda gazawar juyin mulkin da aka yi a Legas, Manjo Nzeogwu ya yi sanarwar da tsakar rana, inda ya ayyana dokar ta-baci a Arewacin Najeriya.
An k**a Enzegwu Kaduna
Bayan sanarwar da aka samu daga Kaduna, da kuma bayanin cewa Nzeogwu na tattara sojoji domin kai hari Legas wanda hakan abu ne mai matukar yiwuwa a lokacin, Kwamandan rundunar, Sojojin Najeriya Manjo Janar Aguiyi Ironsi ya aika da jakadu karkashin jagorancin wani soja mai suna Col Conrad Nwawo, zuwa Kaduna domin tattaunawa da Maj. Nzeogwu da yiwuwar ya mika wuya.
Maj. Nzeogwu ya gindaya sharudda da Gen. Ironsi ya amince da su. Aguyi Ironsi ya karbi mulki, daga baya kuma an k**a Nzeogwu a Legas a ranar 18 ga Janairun 1966 sabanin yarjejeniyar da aka cimma a baya tsakanin Nzeogwu da Ironsi.
An tsare shi a gidan yarin Kirikiri mafi girman tsaro a Legas kafin a kai shi gidan yarin Aba da ke yankin Gabas. Inda Gwamnan yankin Gabas kuma shugaban kasar Rushashshiyar Chukwuemeka Ojukwu ya sake shi a watan Maris 1967.
Yakin basasa da mutuwa
A ranar 30 ga Mayun 1967, Biyafara ta ayyana ‘yancin kai daga Najeriya; hakan ya samo asali ne sak**akon kashe-kashen da ake yi wa ‘yan kabilar Igbo a Arewacin Najeriya ba tare da kakkautawa ba, da kuma yadda shugaban mulkin soja na wancan lokacin Janar Yakubu Gowon ya ki sanya jami’an tsaro su dakile kashe-kashen.
A ranar 29 ga watan Yulin 1967 Nzeogwu - wanda aka kara masa mukami a Sojan Biafra zuwa Laftanar Kanar - ya makale a wani harin kwantan bauna a kusa da Nsukka a lokacin da yake gudanar da aikin leken asiri da daddare kan sojojin gwamnatin tarayya na bataliya ta 21 karkashin Captain Mohammed Inuwa Wushishi.
A lokacin ne a ka kashe shi, bayan an gano gawarsa; Duk da haka 'yar uwarsa ta dage cewa ya kashe kansa ne don gudun kada sojojin tarayya su wulakanta
Bayan an gano Gawar ta sa shugaban mulkin sojan Najeriya Janar Yakubu Gowon ya ba da umarnin a binne shi a makabartar sojoji da ke
Kaduna tare da cikakkiyar girmamawa ta soja.
Daga Saliadeen Sicey