18/08/2026
Netanyahu Ya Ce Kashe-kashen Mutane A Gaza Za Su Ci Gaba, Yayin Da Kushner Ke Adawa Da Su
Rahotanni sun ce Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya shaida wa Jared Kushner, wakilin Shugaban Amurka Donald Trump kuma surukinsa, cewa hare-haren kashe-kashen da ake kaiwa Gaza za su ci gaba.
Rahoton ya ce Kushner ya nuna adawa da ci gaba da kashe-kashen, yana mai ganin cewa hakan na iya kawo cikas ga kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Tashar talabijin ta Isra’ila ce ta ruwaito wannan batu.
PMHN Hausa News
゚