27/08/2023
An gudanar da Bikin Ranar Hausa a Garin Jibiya...
Rubutawa: Yusuf Aminu Jby
K**ar yadda majalisar dinkin duniya ta ware ranar 26 ga watan Ogusta a matsayin ranar Hausa ta duniya, dalibai da malamai masu nazarin harshen Hausa na karamar hukumar Jibiya Sun shiga sahun wadanda s**a gudanar da bikin zagayowar ranar.
Bikin wanda ya gudana a filin wasa na Firamaren Tudun Wada (Pilot) ya samu tagomashin samun mahalartan daban-daban. Daga cikin mahalartan akwai baturen 'yan sandar karamar hukumar, shugaban sashen nazarin harshen Hausa na kwalejin kimiyya ta Katsina, (Dr. Isah Dahiru) wanda yana cikin masu gabatar da makala, Akwai sanannen malamin malamin nan da ya yi fice wajen koyar da harshen Hausa a karamar hukumar, (Malam Mansur Mamuda). Daraktan Ta'asisul Qur'an kuma shugaban makarantar Makarantar gwamnati ta Daddara, Mai girma sarkin Arewa hakimin Jibiya ya shi ma ya amsa kiran taron ta hanyar wakilcin Yariman Jibiya, (Mubarak Rabe Rabi'u). Sarkin noma, da sarkin makera, da sarkin bakin Jibiya da sauran manyan mutane sun amsa katin gayyatar taron.
Malaman makaranta, da daliban makarantun gwamnati da masu zaman kansu, sun cika taro. Inda mafi yawancin abubuwan da s**a gudanar daliban makarantun ne s**a gudanar. Taron ba zai cika ba idan ba a ambaci masu kide-kiden gargajiya, da masu bushe-bushe.
Abubuwan da s**a gudana a wurin baya ga makaloli guda biyu masu taken, "Muhimmancin Rikon Al'adu Ga Hausa.", da "Yaduwar harshen Hausa a Duniya." Sannan akwai raye-rayen gargajiya, da wasan dambe, wasan 'Yar tsana, wasan tafa-tafa, wasan wargin fadawa, Al'adar bakar magana, Gasar Karin Magana, da sauran abubuwa masu kayatarwa.
Bayan kammala taron, al'ummar gari dai na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan taron, da kuma yin tsokaci. Yayin da wasu suke korafin yadda aka ci aka tsire ba tare da sun ji duriyar taron ba, an yi babu su.