
26/02/2025
Hakika akwai darasi mai yawa a tattare da rayuwar wannan bawan Allah shugaban Human rights Television Brekete Family Brekete Family Hausa Ahmad Isa Ordinary President.
A yanzu haka da nake wannan magana ba zai rasa Cases sama da 300 ba na al'umma da yake kokarin kwatowa hakkinsu daga azzalumai daga chikin wadanda s**a taiyemusu hakki.
Dare da rana bayada wata himma kamar tabbatarda adalchi da gaskiya tareda kare martabar marasa karfi da basuda gata.
Ba zai rasa sama da marayu 30 ba, Inda yayi musu gata daga karatunsu har abinda yakai kulawa da tarbiyansu dedai gwargwado ga abinda yake iyawa inda yake ji dasu tamkar shine ya haifesu.
Al'ummar Najeriya shin kuna sane da miyagun kasarnan ba zasu taba barinsa ya zauna lafiya ba ko,โ๏ธ hakki ne ga duk musulmi ya tayashi da addu'o'en samun nasara da kariya daga sharri da makirchin wadannan miyagu da s**a mamaye mana kasarmu Najeriya.๐๐ฟ
Muna rokon Allah subhanahu wa'atala ya kara dafamasa ya kuma karesa daga sharrin dukkan wani mugu na boye da bayyane Ameen.๐คฒ๐ผ