Jaharmu A Yau

Jaharmu A Yau ONLY POST YOU CAN TRUST

INEC ta rufe cibiyar sa ido da tattara sak**ako bayan kammala zaɓen OsunHukumar INEC ta rufe cibiyar sa ido kan zaɓen gw...
16/08/2026

INEC ta rufe cibiyar sa ido da tattara sak**ako bayan kammala zaɓen Osun

Hukumar INEC ta rufe cibiyar sa ido kan zaɓen gwamnan Osun, bayan kammala zaɓen da kuma bayyana Gwamna Ademola Adeleke a matsayin wanda ya yi nasara.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya yaba wa jami’an hukumar kan sadaukarwarsu da ƙwarewar da s**a nuna, yana mai cewa zaɓen Osun zai zama darasi wajen shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Jam’iyyar adawa ta Accord Party ta sha gaban APC a yayin da aka kammala tattara sak**akon zaben gwamnan jihar Osun A yan...
16/08/2026

Jam’iyyar adawa ta Accord Party ta sha gaban APC a yayin da aka kammala tattara sak**akon zaben gwamnan jihar Osun

A yanzu ana jiran hukumar zabe ta ayyana wanda ya yi nasara

DA DUMI-DUMI: ’Yan b!ndiga sun mamaye cibiyar tattara sak**akon zabe a Osogbo.Wasu ’yan b!ndiga da s**a rufe fuskokinsu ...
15/08/2026

DA DUMI-DUMI: ’Yan b!ndiga sun mamaye cibiyar tattara sak**akon zabe a Osogbo.

Wasu ’yan b!ndiga da s**a rufe fuskokinsu sun mamaye wata cibiyar tattara sak**akon zaben a Osogbo, babban birnin Jihar Osun, lamarin da ya kawo cikas ga aikin tattara sak**akon zaben gwamna da ake gudanarwa.

Cibiyar tattara sak**akon da ke Ataoja D, cikin Union Baptist Primary School, tana kula da sak**akon rumfunan zabe da dama na Ward 4.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun mamaye cibiyar ne da misalin karfe 9:45 na dare, yayin da ake ci gaba da tattara sak**akon zaben.

15/08/2026

Governor Oyebanji of Ekiti State is going to congratulate Governor Oyebamiji of Osun State inshallah 🙏

DA DUMI-DUMI: Komitin yakin neman zaben Adeleke ta zargi INEC da shirin ayyana zaben Osun a matsayin INCONCLUSIVE Komiti...
15/08/2026

DA DUMI-DUMI: Komitin yakin neman zaben Adeleke ta zargi INEC da shirin ayyana zaben Osun a matsayin INCONCLUSIVE

Komitin yakin neman zaben Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ta yi zargin cewa akwai wani shiri na ayyana zaben gwamnan jihar da aka gudanar a yau a matsayin zaben da bai kammala ba (Inconclusive).

A cikin wata sanarwa da Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Imole Campaign Council, Rep. Bamidele Salam, ya fitar, kungiyar ta bukaci masu sa ido kan zaben da su sanya ido sosai kan yadda ake tattara sak**akon zaben.

Komitin ta zargi wasu gwamnoni da shugabannin jam’iyyar APC da kokarin yin katsalandan wajen tabbatar da sak**akon zaben, tare da yin kira ga INEC da jami’an tsaro da su tabbatar da cewa an kare cibiyoyin tattara sak**ako.

Labari Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ya tabba ADC ta sauya ɗan takararta na gwamnan AdamawaDaga karshe dai magana ta ƙare jam’iyyar A...
15/08/2026

Labari Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ya tabba ADC ta sauya ɗan takararta na gwamnan Adamawa

Daga karshe dai magana ta ƙare jam’iyyar ADC ta tabbatar da sauya ɗan takararta na kujerar gwamnan jihar Adamawa Hon. Suleiman Umar Omarana da tsohon jigonta a Adamawa Babachir David Lawal ya tsayar, da Hamman Tukur Ribadu.

Hakan ya tabbata ne bayan sabon ɗan takarar tare da tawagar ‘yan takarar ADC na shekarar 2027 daga jihar Adamawa s**a ziyarci ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, a gidansa da ke Abuja.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya gana da ‘yan takarar ADC na jihar Adamawa a dukkan matakan zaɓe, ciki har da sabon ɗan takarar gwamnan jihar, Hamman Tukur Ribadu.

Atiku ya kuma buƙaci shugabannin jam’iyyar, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa mai kula da Arewa maso Gabas, Daniel Bwala, da Shugaban ADC na jihar Adamawa, Rt. Hon. Sadiq Ibrahim Dasin, da su sasanta tare da haɗa kan dukkan ‘yan jam’iyyar.

Ya ce ya kuma ƙarfafa shugabannin da su fara tuntuɓar al’umma ta hanyar gangamin wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a da kuma shirye-shiryen ƙara yawan magoya bayan jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

Atiku ya bayyana farin cikinsa kan abin da ya ce alama ce ta haɗewar jam’iyyar domin kafa tafiya guda, yana mai ƙarfafa su da su ci gaba da wannan yunƙuri.

WATA SABUWA: Dan Takarar Gwamnan jihar Osun na APC ya bukaci INEC ta yi Adalci..Dan Takarar Gwamnan jihar Osun Bola Oyeb...
15/08/2026

WATA SABUWA: Dan Takarar Gwamnan jihar Osun na APC ya bukaci INEC ta yi Adalci..

Dan Takarar Gwamnan jihar Osun Bola Oyebamiji na Jam'iyyar APC,ya Bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa akan ta tabbata ta yi Adalci a cigaba da Bayyana Sak**akon Zaben Jihar.

Kana kuma yayi Kira ga Al'ummar Jihar akan su fito su kare Kuri'unsu don Tabbatar da Cewa abunda s**a zaba aka basu.

Me za ku ce?.

Da ɗumi-ɗumi: Ko kun san Shugaba Bola tinubu ɗan Asalin jihar Osun? Ga Abin da Tarihi da Wasu Bayanai S**a Nuna, Haihuwa...
15/08/2026

Da ɗumi-ɗumi: Ko kun san Shugaba Bola tinubu ɗan Asalin jihar Osun? Ga Abin da Tarihi da Wasu Bayanai S**a Nuna, Haihuwarsa da Haihuwar Iyayensa sun kasance a jihar Osun

A binciken da Mikiya Hausa Tayi Ya nuna cewa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, wanda aka fi sani da Jagaban, yana daga cikin fitattun ‘yan siyasar Najeriya, amma batun asalin danginsa da garinsu na asali ya kasance wani batu da ke ci gaba da jawo muhawara.

A yayin da bayanan da gwamnatin Najeriya da jam’iyyar APC s**a wallafa s**a bayyana cewa an haifi Tinubu a Lagos kuma iyalinsa na Tinubu ne na Lagos, wani kundin tarihin Najeriya mai suna Nigerian Dictionary of National Biography ya bayyana Jihar Osun, musamman Boripe Local Government Area, a matsayin jihar asalin Shugaba Tinubu.

Haka kuma, wasu masu bincike kan tarihin iyalan Yarbawa sun yi ikirarin cewa tushen dangin Tinubu yana Iragbiji, wani gari da ke cikin Boripe Local Government Area na Jihar Osun.

Wasu daga cikin waɗannan bayanan sun danganta asalin Tinubu da wasu iyalai daga Iragbiji, tare da cewa akwai alaƙar jini tsakanin danginsa da wasu fitattun ‘yan siyasar Osun.

Sai dai wannan batu ba shi da cikakkiyar yarjejeniya, domin akwai wasu bayanai da s**a musanta cewa an haifi Tinubu a Iragbiji ko kuma cewa yana da wani suna na daban kafin saninsa da Bola Ahmed Tinubu.

Saboda haka, abin da ya fi dacewa shi ne a bambanta tsakanin wurin da aka haifi mutum da kuma asalin danginsa. Wasu bayanai sun ce Tinubu an haife shi ne a Lagos, yayin da wasu bayanan tarihi s**a danganta tushen danginsa da Jihar Osun.

Tambaya ga masu karatu: Shin kun taba jin cewa asalin Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da alaƙa da Iragbiji a Jihar Osun?

An Tarwatsa Masu Zabe a Rumfar Aregbesola Yayin da Ake Zaben OsunOsun — An samu tashin hankali a rumfar zaɓe da ke yanki...
15/08/2026

An Tarwatsa Masu Zabe a Rumfar Aregbesola Yayin da Ake Zaben Osun

Osun — An samu tashin hankali a rumfar zaɓe da ke yankin da tsohon Gwamnan Jihar Osun kuma tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ke kada ƙuri’a, yayin da ake gudanar da zaɓen gwamnan jihar a ranar Asabar.

Rahotanni sun ce wasu mutane da ake zargin ’yan daba ne sun kutsa cikin rumfar, lamarin da ya sa wasu daga cikin masu kaɗa ƙuri’a s**a bar wurin saboda fargabar rashin tsaro.

A wannan zaɓe, Gwamna Ademola Adeleke na neman komawa kan kujerarsa, inda yake fuskantar ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, da sauran ’yan takarar gwamna.

Wasu jami’an jam’iyyun da ke rumfar sun yi zargin cewa mutanen da s**a kawo cikas suna da alaƙa da jam’iyyar APC. Sai dai wakiliyar APC a rumfar, Abogunloko Olufunke, ta musanta zargin, tana mai cewa mutanen ba ’yan jam’iyyar ba ne kuma ba ta san su ba.

“Waɗannan mutanen ba ’yan jam’iyyarmu ba ne. Ban san su ba,” in ji ta.

Wani Zargin a Boluwaduro

A wani lamari mak**ancin haka, an kuma samu zargin cewa wani jami’in ‘yan sanda mai kula da wani sashen ‘yan sanda (DPO) a ƙaramar hukumar Boluwaduro ya jagoranci wasu mutane da ake zargin ’yan daba ne zuwa Otan-Ayegbaju, inda ake zargin sun yi yunkurin kwashe kayan zaɓe.

Rahotanni daga wurin sun ce wasu mazauna yankin sun bijirewa yunƙurin, inda s**a hana a fitar da kayan zaɓen daga yankin.

Wani faifan bidiyo da kafar Sahara Reporters ta ce ta gani ya nuna wasu mazauna yankin suna zargin cewa DPO ɗin ne ya jagoranci mutanen zuwa wurin tare da ƙoƙarin tarwatsa jama’ar da ke wajen.

Sai dai waɗannan zarge-zarge ba su zama tabbataccen hukunci kan duk wanda aka ambata ba, kuma ana buƙatar hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike domin tabbatar da hakikanin abin da ya faru.

K**ar yadda Daily True Hausa ta tattaro daga rahotannin kafafen yaɗa labarai.

ALLAH KA TSARE MANA IMANINMU KA RABA MU DA MUMMUNAR KADDARARundunar ’Yan Sandan Adamawa Ta K**a Wani Mutum Bisa Zargin F...
14/08/2026

ALLAH KA TSARE MANA IMANINMU KA RABA MU DA MUMMUNAR KADDARA

Rundunar ’Yan Sandan Adamawa Ta K**a Wani Mutum Bisa Zargin Fille Kan Wata Mata A Otal.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta shirya farautar wani mutum da ake zargi da fille kan wata mata mai matsakaicin shekaru a cikin ɗakin wani otal da ke ƙaramar hukumar Girei ta jihar.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da rana a Otal ɗin Novex, inda ake zargin wanda ake tuhuma ya shiga otal ɗin tare da matar.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa sun ji hayaniyar faɗa daga ɗakin da wanda ake zargin ya sauka, lamarin da ya sa s**a gaggauta shiga ɗakin. A nan ne s**a ga matar kwance cikin jini, tare da wani mummunan rauni a wuyanta.

An kwashe gawar matar daga otal ɗin zuwa wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba, yayin da aka ce ’yan sanda sun k**a wanda ake zargin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya ce rundunar ta k**a wani mutum guda da ake zargi da hannu a cikin laifin.

Address

001
Jigawa

Telephone

+2349027074793

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaharmu A Yau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaharmu A Yau:

Shortcuts

Share