07/03/2026
RABON KAYAN ABINCIN AZUMI DA TALLAFIN KUƊI GA AL’UMMAR ƘARAMAR HUKUMAR DUTSE NA SAMA DA KIMANIN NAIRA MILIYAN (28,000,000).
A wani mataki na ƙara ƙarfafa jin daɗin al’umma da kuma tallafa musu a wannan wata mai alfarma na Ramadan, Mai Girma Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Kimiyya da Fasaha ta Jihar Jigawa, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ya gudanar da rabon kayan abincin Azumi ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Dutse.
A cikin wannan shiri na alheri, an raba buhunan shinkafa guda 420 masu nauyin kilo 15 ga mazabu 11 na Ƙaramar Hukumar Dutse domin taimaka wa iyalai da dama su samu sauƙin gudanar da ibadunsu na Azumi cikin walwala da kwanciyar hankali.
Baya ga rabon kayan abincin, Mai Girma Kwamishinan ya kuma bayar da tallafin kuɗi ga manyan shugabannin al’umma, ciki har da Limamai, Ladanai, Dagatai, Masu Unguwanni, da sauran al’umma a lungu da saƙo na Ƙaramar Hukumar Dutse. Wannan tallafi na nufin ƙarfafa musu gwiwa da nuna godiya bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen jagorantar al’umma, tabbatar da zaman lafiya da kuma ƙarfafa haɗin kai.
Haka kuma, shirin tallafin ya haɗa da shugabannin jam’iyya na Ƙaramar Hukumar Dutse tare da kwamitocinsu (Excos), shugabannin jam’iyya na mazabu 11 da kwamitocinsu, shugabannin akwatuna, da kuma Masu Bai Wa Gwamna Shawara (Special Assistants) daga faɗin Ƙaramar Hukumar Dutse.
Sauran waɗanda s**a amfana sun haɗa da Kansiloli, Supervisor Councillors, masu taimakawa Shugaban Ƙaramar Hukumar Dutse (S.A to the Chairman), ‘Yan Media da sauran ‘Yan Gwagwarmaya. Gaba ɗaya, an raba zunzurutun kuɗi da ya kai kimanin naira miliyan ashirin da takwas (₦28,000,000) domin tallafa wa waɗannan rukunin jama’a.
Tallafin kuɗin da aka raba ya haɗa da naira dubu goma-goma (₦10,000), dubu ashirin-ashirin (₦20,000), da kuma dubu hamsin-hamsin (₦50,000) ga bangarori daban-daban na matakan jam’iyya a Ƙaramar Hukumar Dutse, gwargwadon matsayinsu a tsarin jagoranci da hidimar al’umma.
Wanda sama da mutum 11,550 za su amfana da wannan shiri mai albarka, wanda ke nuni da yadda Mai Girma Kwamishinan ke da himma wajen kusantar al’umma da tallafa musu a lokuta daban-daban.
Wannan rabon tallafi ya zo ne domin sauƙaƙa wa al’umma halin da ake ciki tare da ƙarfafa musu gwiwa a wannan wata na ibada. Hakan kuma ya ƙara tabbatar da jajircewar Farfesa Isa Yusuf Chamo wajen kyautata rayuwar al’umma da inganta jin daɗinsu.
Allah Ya saka da alkhairi, Ya ƙara ɗaukaka da nasara.
Usman Muhammad Ismail
Media Assistant to the Honourable Commissioner
7th March, 2026.
Isa Yusuf Chamo