23/05/2025
MANYAN DALILAI 11 DA SUKE DURKUSAR DA MATASAN AREWA DA ZARAR MUN SOMA TASHE A KASUWA
Nazari: Auwalu El-Yobawi | 09-05-2025
🔴 1. RASHIN NAZARI DA TSARI:
Akasarinmu, bamu tsayawa mu nazarci me ya dace damu amatsayin hanyar nema.
Kawai da mun wuce ta gaban shago ko rumfar wani cike da kaya sai muji aranmu nantake inama da wannan wajen namu ne, ba tareda tambayar kanmu ko zamu iya zama k**ar yadda me wannan shago ko rumfar ya zama ba.
Bamu nazarin wane irin hatsari ke tattare da irin wannan kasuwar.
Bamu nazarin wai shin daga ina irin wannan kaya ke isowa inda muka gan su har s**a burge mu?
Kawai da mun gani, muna komawa gida zamu soma neman shago da Jari wai mu ma a dole sai mun zama;
🔴 2. RASHIN TUNTUBA DA GIRMAN-KAI:
Da wuya kaga Dan Arewa ya kaskantar da kansa yaje wajen wani da yaga sana'ar sa har ta burge shi ya nemi alfarmar ya saurare shi ya bashi shawara amatsayinsa na wanda zai fara.
A'a, shi kawai a tunaninsa, tunda mutum ne Dan Uwansa yake yi, to shima kai-tsaye zai iya.
Wani abin mamaki ma, nantake wani zai soma gaaba da wanda yakeson ya koyi irin sana'ar sa;
🔴 3. GAGGAWA:
Mun fi son da zarar mun soma kasuwa mu Kudance afujajan-afujajan ba tareda bata lokaci ba.
Zaka ga sabon Dan Kasuwa yana hada kansa da wanda yayi Shekaru da dama yana yi; wai so yake nantake ya zama k**arsa.
So yake ba tareda bata lokaci ba ya gina gida irin nashi, ya hau mota irin tashi, ya sanya sutura irin tashi, ya auri mata irin tashi. Da sauransu.
🔴 4. SAURIN SAUYA SALON RAYUWA:
Idan mutum ya soma kasuwa kuma ta soma karbuwa yana samun bunkasa, nan da nan zakaga ya sauya salon rayuwa.
Ba tareda bata lokaci ba, zaka ga ya soma almubazzaranci da kashe kudi maras Ma'ana: abincin sa saida nama, rigarsa saida guga, morarsa sai da Esi, gidansa kusan duk wata sai an sauya fenti, karin Aure da sabbin Abokai;
🔴 5. MANTAWA DA ASARA:
Gani muke riba kadai ake samu a kasuwa, ba tareda tuna cewa 'Hannun da ya kirga riba ayau zai iya kirga asara agobe ba.
Hakan yakesa 'yan kasuwar mu basu cizawa kafin su hura. Ba mu lissafa me zaije yazo. Kafin ka kashe 10 ka samu 20?
Tunda gani muke kawai indai mun kashe to zamu samu;
🔴 6. RASHIN BAMBANCE RIBA DA UWAR-KUDI:
Idan bukatu s**a motsa, a ka'idar kasuwanci fa ba'a taba Uwar-Kudi. Duk abinda za'ayi, tsayawa ake a riba saidai idan wata Annoba ko Ibtila'i ne ya gitta.
Amma Inaaaaaaa, mu kawai idan bukata ta motsa ba tareda nazari ba, kawai duk kudin da hannunmu ya taba da shi za'ayi. Wannan kuma babban kuskure ne da muke yi;
🔴 7. RASHIN ADANA BAYANAI KO 'RECORD' A TURANCE:
Sau da yawa, riba da zumudi kansa mu manta wani muhimmin abu da bai k**ata mu manta ba. Alal misali kananan bashi, lalatattun kaya da suke bukatar sauyawa, alkawurra da Abokan hulda da warware matsalolin hada hada da sauransu.
Muna da wannan Sakacin sosai. Wani abin idan k**anta shi, ka manta shi har abada kuma zai iya haddasa wa sabuwar kasuwar ka Babbar Barazana;
🔴 8. RAINA KARAMAR RIBA:
Wai mutum ba zai sayar ba sai riba ta ninka ko ta kusa Uwar kudi. Alhalin kuwa, me bin karamar riba sai ya sayar yaje ya saro wasu kayan, me jiran babbar riba bai sayar ba.
Sannan me bin karamar riba yafi yawan Abokan hulda. Akan rashin Naira 5, sai wani yayi doguwar tafiya don yazo ya saya awajen ka;
🔴 9. KIN NEMAN KARIN ILIMI DANGANE DA SANA'AR DA MUKEYI
Akasarinmu, da zarar muna sana'a kuma tana kawo mana riba, to shikenan ba zamuke kokarin sanin wane cigaba sauran sassan Duniya s**a samu dangane da ita ba. Ko kuma wani sauyi aka samu domin tafiya daidai da yanayi ko zamani.
A'a, kawai sai mu cigaba da yinta kara-zube !
🔴 10. KARANCIN ADDU'A
idan mutun yana kasuwa ko wata harka, shikenan gani yake dabara ko wayonsa da iya sarrafa kasuwancinsa ne yake bashi.
Ka lura sosai da sosai, lokacin da akasarinmu muke halin rashin dawwamammiyar sana'a a hannu munfi komawa ga Allah amma da zarar abubuwa sun hau hanya, zakaga hakan ya cibaya munfi mayarda hankula kan sana'ar;
🔴 11. Saurin butulcewa iyayen gida, ogogi ko wa'yanda s**a koya mana kasuwa ko aikin-hannu, musamman idan muka karbu fiyeda su bayan an soma sanin mu. Daga sannan muke soma ganin ai muma karan mu yakai tsaiko. Ai wai abinda s**a sani muma munriga mun sani.
Duk Matashin Dan-Kasuwar da zai gaza kiyaye wadannan abubuwan guda 8 (duk da ba iyakarsu kenan ba) ba zaikai labari ba; karya ne.
Mu lura da kyau mana !! Abokan zamanmu da suke kwararowa daga Kudancin kasarnan haka suke yi?
Ya k**ata mu gaggauta yiwa kawunanmu fada don mu gudu tare kuma mu tsira tare.
Allah SWT ya sanya mana albarka cikin neman halalin mu ba don mun iya ba.
Allah kar yabarmu da iyawar mu.
Mu isarda wannan sako ga sabbin matasan 'yan kasuwar mu don a kiyaye !!