07/02/2026
Darasi Daga Rayuwar Tsohon Daraktan Finafinan Hausa, Ashiru Nagoma
Duk wani dan kannywood indai ka ga bai dauki darasi akan wannan bawan Allah ba to wallahi bai san me yake yi ba, domin kuwa idan ana maganar daukaka, izza, gadara da isa, to an gama daga kansa, amma yanzu ya zama tarihi.
Ashiru Nagoma shine mai kamfanin 'Nagoma Film Production' shekaru da dama da s**a wuce, wanda idan ya fara aikin fim to duk wani Furodusa ko Darakta sai ya jira shi ya gama aikinshi sannan ya fara nasa, saboda yana kwashe jarumai da ma'aikatan masana'antar gaba daya.
A lokacin sa babu wani jarumi da ya isa ya yi masa gadara ko jiji da kai, domin kuwa idan ya ce ba zai yi fim da kai ba gani ake ka mutu murus a masana'antar.
Shine daraktan da idan ba ka zo akan lokaci ba to a gabanka zai ce ya cire ka a fim din saboda gadararsa da takama da daukakar da Allah Ya ba shi a waccan lokacin.
Amma abun mamaki yanzu wasu da dama a masana'antar ba su san shi ba ma saidai suke jin labarinsa.
Ya shirya manyan finafinai da s**a hada da;
1.ASABARI
2.DUBAYYA
3.FANNIN SA'A
4.NAGARI NA KOWA
5.MURNA
6.MAGAGI
7.TUTAR SO
8.NAGOMA
9.YAR ADUWA
10 HAUSA BAKWAI
11 KAMBUN SO
12.GOBEMA RANA CE
14.GOBE DA NISA
15.DARDUMA
17.ZAKKA
18. DAUKAKA
19.TAKURA
Allah Sarki rayuwa! Ko yana ina yanzu haka?
Za ku iya tuna fim dinsa da kuka kalla a zaminsa kuwa?
Daga Magatakarda