17/01/2026
Kungiyar Tsofaffin Ɗaliban Na'ibi Academy Littahafizil Qur’ani Sun Karrama Shugaban JIBWIS na Ƙasa, Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau
Kungiyar Tsofaffin Ɗaliban Makarantar Na'ibi Academy Littahafizil Qur’an sun shirya wani taro na musamman domin karrama Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta Tarayyar Najeriya, Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau, bisa irin gagarumin gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ilimi da kula da rayuwar ɗalibai.
Wannan karramawa ta biyo bayan ƙoƙari na musamman da Sheikh Bala Lau ke yi wajen tallafa wa ɗalibai, inda ya ɗauki nauyin karatunsu kyauta, tare da basu damar samun ilimin Alƙur’ani mai girma da na zamani cikin tsari da kulawa. Tsofaffin ɗaliban sun bayyana cewa wannan taimako ya taka muhimmiyar rawa wajen gina rayuwarsu, tare da zamar musu ginshiƙin nasara a fannoni daban-daban na rayuwa.
A cewar Kungiyar, abin da ya fi jan hankali shi ne yadda Sheikh Bala Lau ke gudanar da wannan aiki cikin ikhlasi da kishin addini, ba tare da neman yabo ko wata fa’ida ta duniya ba, sai dai burinsa na ilimantar da al’umma da gina ingantattun matasa masu tsoron Allah.
Shugabannin Kungiyar Tsofaffin Ɗaliban sun jaddada cewa irin wannan tallafi ya sa makarantar ta zama tushen haske da tarbiyya, inda ake haɗa ilimin addini da na zamani domin amfanin al’umma baki ɗaya. Sun kuma yi addu’a ga Sheikh Bala Lau da Allah Ya saka masa da alheri, Ya ƙara masa lafiya, tsawon rai da albarka a dukkan ayyukansa.
Hakika, wannan karramawa ta nuna cewa wanda ya zuba jari a ilimi, musamman ilimin Alƙur’ani, ya gina al’umma ne gaba ɗaya, kuma irin wannan aiki na Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau abin koyi ne ga shugabanni da masu hannu da shuni a faɗin ƙasa.
Jibwis Nigeria