BA News HAUSA

BA News HAUSA Labari masu inganci

An samu hatsaniya a sansanin NYSC da ke Abuja bayan soja ya lakadawa dan NYSC duka.Lamarin ya faru a yau yayin da sojan ...
13/12/2023

An samu hatsaniya a sansanin NYSC da ke Abuja bayan soja ya lakadawa dan NYSC duka.

Lamarin ya faru a yau yayin da sojan ya fasa wa matashin wayar salula da kuma agogon hannu mai tsada.

Daraktar sansanin ta dauki mataki kan kwamandan nan take da alkawarin biyan matashin asarar da ya yi.

Hotuna :Yadda wata babbar motar daukar kaya (Tirela) ta fadi yanzu haka a ƙasan gadar Muhammadu Buhari dake Hotoro a bir...
13/12/2023

Hotuna :Yadda wata babbar motar daukar kaya (Tirela) ta fadi yanzu haka a ƙasan gadar Muhammadu Buhari dake Hotoro a birnin Kano.

Zuwa yanzu babu alamun asarar rai, amma ana fargabar ko motar ta danne wani, haka ne yasa al’ummar wajen s**a kai agajin gaggawa.

An kai hari a Gidan Shaho washegari aka koma kauyen Nasarawar Zurmi inda aka yi asarar mutane, rayuka, dukiya da abinci ...
11/12/2023

An kai hari a Gidan Shaho washegari aka koma kauyen Nasarawar Zurmi inda aka yi asarar mutane, rayuka, dukiya da abinci – Karanta cikakken rahoto a sashen sharhi

Hoto: Dauda Lawal (Facebook)

Yan bindiga sun kai sabon hari a jihar Plateau, sun kashe mutum hudu nan take.Daga bisani s**a cinna wa gidan basaraken ...
11/12/2023

Yan bindiga sun kai sabon hari a jihar Plateau, sun kashe mutum hudu nan take.

Daga bisani s**a cinna wa gidan basaraken garin wuta da iyalansa a ciki.

Rundunar soji ta kai dauki garin amma babu rahoto ko an k**a wani dan bindiga a harin.

Rayuwa kan iya juyawa kowa ba tare da zato ko tsammani ba, k**ar dai yadda sufetan 'yan sanda ya koma barar abin da zai ...
08/12/2023

Rayuwa kan iya juyawa kowa ba tare da zato ko tsammani ba, k**ar dai yadda sufetan 'yan sanda ya koma barar abin da zai ciyar da iyalinsa shekara biyar da yin ritaya. Duba labarinsa a sashin sharhi.

Hoto: (Twitter)

YANZU YANZU : Wata kotu a garin Potiskum ta yanke hukuncin kisa ga sojan da ya Kashe Sheikh Aisami Gashuwa, Shikuma wand...
05/12/2023

YANZU YANZU : Wata kotu a garin Potiskum ta yanke hukuncin kisa ga sojan da ya Kashe Sheikh Aisami Gashuwa, Shikuma wanda ya tayashi Daurin 10yrs.

Rundunar sojin kasa ta bada hakuri game da jirginta da ya yi ruwan bamabamai kan yan mauludi bisa kuskure a KadunaShugab...
05/12/2023

Rundunar sojin kasa ta bada hakuri game da jirginta da ya yi ruwan bamabamai kan yan mauludi bisa kuskure a Kaduna

Shugaban rundunar sojin kasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja da tawagarsa sun ziyarci garin Tudun Biri karamar hukumar Igabi jihar Kaduna, inda mutanen garin s**a gamu da iftila'in bam da ya fada bisa yan mauludi suna tsaka da gudanar da bikin a kauyen na Tudun Biri.

A ziyarar da shugaban rundunar sojin kasar ya kai, ya ce sun zo ne don su jajanta tare da bada hakuri game da wannan iftila'in da ya faru a cikin kuskure.

Ya ce yankin nasu na zagaye da yan bindiga, hakan ne ya sa bayan samun wasu bayanai game da yan bindigar rundunar ta yi niyar kai masu hari don darkake su, cikin tsautsai jirgin ya sauka kan wadannan mutanen da ba su ji ba su gani ba, inda ya tabbatar wa al'ummar garin da cewa za su gudanar da kwakkwaran bincike a kan jami'ansu da kuma na'urorin da s**a yi amfani da su dan kauce ma sake afkuwar irin haka

Ya kuma yi ta'aziya ga shugaban Jama'atu Nasarul Islam reshen jihar Kaduna da sauran malaman addinin Musulunci baki daya

Lagbaja ya kuma ziyarar makabartar da aka rufe waɗanda iftila'in ya rutsa da su don yi masu addu'a, sannan kuma ya ziyarci asibitocin da aka kai wadanda s**a jikkata don duba su

Za a iya tuna cewa Katsina Daily News ta rawaito cewa dama tun da farko rundunar sojin sama NAF ta nisanta kanta da kai wannan harin inda ta ce tun kafin iftila'in ya afku, ta share sama da awanni 24 ba tare da ta tada jirgi ya kai hari kan yan bindiga ba.

Students of Abubakar Tafawa Balewa University Bauchi evacuating the school premises from both campuses  .The students of...
05/12/2023

Students of Abubakar Tafawa Balewa University Bauchi evacuating the school premises from both campuses .

The students of Abubakar Tafawa Balewa University Bauchi

Wannan sanarwa ta fito ne bayan da rundunar sojan saman Najeriyar ta ce ba ita ta kai hari kan masu Maulidin ba, ta kuma...
04/12/2023

Wannan sanarwa ta fito ne bayan da rundunar sojan saman Najeriyar ta ce ba ita ta kai hari kan masu Maulidin ba, ta kuma jaddada cewa ba ita kadai ke amfani da jirage a yaki da ake yi da 'yan bindiga a arewa maso yammacin kasar ba.

Ta tabbata tsaro na kara tabarbarewar a Arewacin Nijeriya, bayan Rundunar Soji tace basu s**a Kai hari Bam a taron masu ...
04/12/2023

Ta tabbata tsaro na kara tabarbarewar a Arewacin Nijeriya, bayan Rundunar Soji tace basu s**a Kai hari Bam a taron masu gudanar da Maulud ba, wanda yai sanadiyar mutuwar a akalla mutane 70 izuwa hanzu

Lamarin tsaro kullum na ƙara taɓarɓarewa.Ƴan bindiga sun kai farmaki a unguwar sai wane da wane a birnin tarayya Abuja.A...
04/12/2023

Lamarin tsaro kullum na ƙara taɓarɓarewa.

Ƴan bindiga sun kai farmaki a unguwar sai wane da wane a birnin tarayya Abuja.

A da harin ƴan bindiga bai wuce ƙauyukan da ke wajen birnin tarayya Abuja.

ZANGA-ZANGAR MATA A KANO: Ya Kamata Matar Gwamna Ta Fito Ta Jagoranci Zanga-Zanga Tunda Kujerar Mijinta Ne, Cewar Sheik ...
04/12/2023

ZANGA-ZANGAR MATA A KANO: Ya Kamata Matar Gwamna Ta Fito Ta Jagoranci Zanga-Zanga Tunda Kujerar Mijinta Ne, Cewar Sheik Lawal Triumph

Shehin Malamin ya ci gaba da cewa Gwamna ba shi da 'ya'ya mata ne? Su fito su yi zanga-zangar mana, ai kujerar Uban su ne? Kune ba ku san ciwon kanku ba? Kune ba ku san ciwon kanku ba, ba ku da maza?

Me zakù ce?

Address

ABBA NA SHEHU
Jos

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when BA News HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share