Zinariya Hausa News

Zinariya Hausa News For research and reporting news, we'll make you updated!

YANZU-YANZU; A Wannan Rana Ta Juma'a 16/June/2023 An Ɗaura Auren Sayyada Sadiya Haruna Da Abubakar Ibrahim Wanda Aka Fi ...
16/06/2023

YANZU-YANZU; A Wannan Rana Ta Juma'a 16/June/2023 An Ɗaura Auren Sayyada Sadiya Haruna Da Abubakar Ibrahim Wanda Aka Fi Sani Da G'Fresh.

Wanne Fata Zakuyi Musu?

Buhari Ya Bayar Da Umarnin Cigaba Da Amfani Da Tsohuwar Naira 200 Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa Babban Ba...
16/02/2023

Buhari Ya Bayar Da Umarnin Cigaba Da Amfani Da Tsohuwar Naira 200

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa Babban Bankin Ƙasar umurnin sake fito da tsofaffin Takardun Naira 200 domin a ci gaba da mu'amala da su a Ƙasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin Jawabin da ya yi wa Al'ummar Ƙasar da Safiyar yau Alhamis.

Buhari, wanda ya ce yana sane da irin halin Wahala da Al'ummar Ƙasar ke ciki, ya ce za a ci gaba da Amfani da Takardar Ƙuɗin na Naira 200 har zuwa 10 ga watan Afrilu.

Ya Kuma Buƙaci Al'umma Dasu Ƙara Haƙuri Kan Halinda Ake Ciki

Laila Ta Cikin Shirin Labarina Tare Da Mijinta Tsohon Dan Kwallon Nijeriya, Tijjani Babangida Sun Samu Ƙaruwa.Daga; Rari...
07/02/2023

Laila Ta Cikin Shirin Labarina Tare Da Mijinta Tsohon Dan Kwallon Nijeriya, Tijjani Babangida Sun Samu Ƙaruwa.

Daga; Rariya

YANZU-YANZU; Wani Soja Ya Bindige Direban Motar Kamfanin BUA Har Lahira Akan Babban Titin Kaduna Zuwa KanoTuni Masu Many...
11/01/2023

YANZU-YANZU; Wani Soja Ya Bindige Direban Motar Kamfanin BUA Har Lahira Akan Babban Titin Kaduna Zuwa Kano

Tuni Masu Manyan Motoci S**a Yi Dandazo Na Rufe Hanyar Ba Shiga Ba Fita Sak**akon Harbin Da Aka Yi Wa Takwaransu.

Daga Real Buroshi Mawaka Sokoto

YANZU-YANZU; Mabiya Shi'a Suna Gudanar Da Zanga-zangar A Saki Shaikh Abduljabbar A Babban Masallacin Abuja.
30/12/2022

YANZU-YANZU; Mabiya Shi'a Suna Gudanar Da Zanga-zangar A Saki Shaikh Abduljabbar A Babban Masallacin Abuja.

HOTUNA; Jaruma Maryam Booth Ta Zama Ambasadan Kamfanin Biskit Na (hhh! Biscuit).”
21/10/2022

HOTUNA; Jaruma Maryam Booth Ta Zama Ambasadan Kamfanin Biskit Na (hhh! Biscuit).”

Babban Labari! Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa Zai Angwance Da Matashiyar Budurwa, Hafizar Al-Qur'ani, Hafiza Haulatu Aminu...
19/10/2022

Babban Labari!

Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa Zai Angwance Da Matashiyar Budurwa, Hafizar Al-Qur'ani, Hafiza Haulatu Aminu Ishaq, Ranar Juma'a Mai Zuwa A Garin Gusau Dake Jihar Zamfara.

Allah Ya Sanya Albarka, Amin.

Bn Taheer Zinaria Textile; Mun Ƙara Bunƙasa Sana'armu"Duniyar sabbin Ɗunkuna na Zamani" shahararren Kamfanin na naku mai...
11/10/2022

Bn Taheer Zinaria Textile; Mun Ƙara Bunƙasa Sana'armu

"Duniyar sabbin Ɗunkuna na Zamani" shahararren Kamfanin na naku mai Albarka yana mai farin cikin sanar daku cewa mun ƙara bunƙasa Sana'armu, da kun sanmu a iya Ɗinki ne na Kayan Maza da Mata. Da kuma Ready Made woto Kayan da aka riga aka Ɗinka kawai Saya zakayi ka saka.

Ƙarin da aka samu shine yanzu muna Sayar da duk nau'ikan Kayayyaki na Zamani irin su Shadda, Boyel, Kashmir da sauran su. A ɓangaren Kayan Mata kuma akwai Atamfa, Lesis, Material da sauran su. Bai zama dole idan kun Saya sai mun Ɗinka muku ba, kuna iya tafiya dashi.

Muna nan a Adireshin mu Gida mai number 138 opposite 3D Restaurant akan Titin Bauchi Road dake cikin garin Jos, ko kuma ku tuntuɓe mu Kaitsaye Kira ko WhatsApp ta wannan number; 08103706572 Ibrahim Muh'd Tahir Daraktan Kamfanin Bn Taheer Zinaria Textile.

Talata 11/Oct/2022

Hawa 100 Sauka 100; Ko Kunsan Wajennan A Jos?Daga; Ibrahim Muh'd Tahir Jos Hawa 100 Sauka 100 wani tsauni ne dake cikin ...
06/10/2022

Hawa 100 Sauka 100; Ko Kunsan Wajennan A Jos?

Daga; Ibrahim Muh'd Tahir Jos

Hawa 100 Sauka 100 wani tsauni ne dake cikin Meseum dake garin Jos. Shi dai wannan guri masana Tarihi sunce, anan ne Kabilar Jarawa s**a fara zama bayan sun shigo Najeriya a Shekaru masu yawa da s**a gabata. Mai mana bayanin wajen yace da yake su Ƴan Kabilar ta Jarawa sun fi son zama akan tsauni saboda dubarbaru da kuma hikimar yin Yaƙi, da kuma yana yi na gudanar da Al'adun su sun fi jin daɗin yi akan tsauni.

Ya shaida mana cewa anan cikin garin Jos s**a fara zama daga bisani kuma s**a fara rarrabuwa zuwa sassa na Ƙasar Najeriya, Kabila ne na Mutanen da basu san rigima ko abinda yayi k**a da haka. Lallai Jarawa suna da abin birge dangane da yanayin Al'adun su dama yanayin yadda suke gudanar da Rayuwar su cikin lumana ba tareda muzgunawa Al'ummar da suke Rayuwa a cikin su ba, wani ƙarin bayanin ma sai kun shigo Jos kun gane Idon ku.

Wanin ƙarin bayani kuma abin burgewa dangane da wajen, shine idan ka hau kan tsaunin kana iya hango manya gurare da dama na cikin garin Jos. Kai kace duka garin kake hanga ga yanayi mai daɗi gami da nishadi cikin nutsuwa ba tareda fargabar wani mugun abu zai samun ka ba. Yana daga cikin guraren da inkaje su a Jos zaka ƙara yarda da taken da ake yiwa Jos na garin zaman lafiya da kuma yanayi mai daɗi, kuyi ƙokari ku halarci wannan wajen domin tabbatar da hakan.

Alhamis 6/Oct/2022

YANZU-YANZU: Atiku Abubakar Ya Samu Tarbar Miliyoyin Magoya Bayansa A BauchiDaga Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)Ɗa...
05/10/2022

YANZU-YANZU: Atiku Abubakar Ya Samu Tarbar Miliyoyin Magoya Bayansa A Bauchi

Daga Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)

Ɗan takarar shugaban Ƙasa a Inuwar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya isa Jihar Bauchi domin halartar taron Tuntuɓa na Arewa maso Gabas a yau Laraba 5 ga Watan Oktoban 2022.

Babban Labari! Jagoran Ƴan Shi'a Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya amshi baƙuncin Manjo Hamza Almustafa a gidansa dake Abuj...
19/07/2022

Babban Labari!

Jagoran Ƴan Shi'a Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya amshi baƙuncin Manjo Hamza Almustafa a gidansa dake Abuja.

Hotuna;
Talata 19/07/2022

Da Barazanar Fara Tsadar Biredi A Nijeriya!Kamfanonin biredi a Najeriya sun yi barazanar tafiya yajin aiki sak**akon ƙar...
25/06/2022

Da Barazanar Fara Tsadar Biredi A Nijeriya!

Kamfanonin biredi a Najeriya sun yi barazanar tafiya yajin aiki sak**akon ƙarin farashin kayayyakin haɗi.

Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito ƙungiyar 'Association of Master Bakers and Caterer of Nigeria' wadda ta ce farashin fulawa da sikari da sauran kayan haɗi da ake amfani da su wurin yin biredi duk sun yi tashin gwauron zabi.

Ƙungiyar ta kuma ƙalubalancin gwamnatin Najeriya kan zargin nuna halin ko in kula dangane da wannan batu inda ƙungiyar ta yi barazanar tafiya yajin aiki daga ranar 13 ga watan Yulin 2022.

Ko a kwanakin baya dai sai da aka ƙara kuɗin biredi a Najeriya sak**akon ƙarin farashin kayayyaki.

-BBC-Hausa

Putin Ya Zanta Da Shugaban Palasɗinawa! Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya zanta da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas t...
18/04/2022

Putin Ya Zanta Da Shugaban Palasɗinawa!

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya zanta da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ta wayar tarho.

Shugabannin sun tattauna batutuwa da s**a shafi matsugunin Yahudawa da ke ƙara rurua rikici a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da kuma gabashin Kudus.

Sun bayyana fatan wannan ba zai kai ga fito na fito ba tsakanin Falasdinawa da Isra’ila ba. Sun jaddada buƙatar sake farfaɗo da hawa teburin sulhu tsakanin Falasdinawa da Isra’ila.

Shugaban sun tattauna yadda za su inganta hulɗar kasuwanci da tattalin arziki. Sannan Putin ya taya Mahmoud Abbas da Falasdinawa murnar azumin watan Ramadan.

Me yayi zafi haka: An mika bakin bakarabe ga hannun "Yan sandan jahar NasarawaAn Miƙa Baƙin Balarabe Hannun Ƴan Sandan J...
18/04/2022

Me yayi zafi haka: An mika bakin bakarabe ga hannun "Yan sandan jahar Nasarawa

An Miƙa Baƙin Balarabe Hannun Ƴan Sandan Jihar Nasarawa Saboda Ya Ki Miƙa Raƙumin Da Ya Ba Shugaban Jami'yyar APC Na Kasa Kyauta.

Akasin labari mai daɗi da jama'a suke dakon ji, ta sauya zane a halin yanzu dai an damka Bakin Balarabe hannun Jami'an Ƴansanda a jihar Nasarawa.

Idan dai ba'a manta ba Bakin Balarabe ya damka Raƙumin shi ga Sabon Shugaban Jam'iyya APC Abdullahi Adamu da niyyar tayashi murna, sai dai maimakon samun tukuici mai gwaɓi Bakin Balarabe ya samu tukuicin Naira Dubu Ɗari ne kaɗai, lamarin da baiyima Bakin Balarabe daɗi.

Wannan lamarin dai yasa ya sauya tunanin shi tare da cewa ya fasa bada wannan Raƙumin nashi ga Shugaban Jam'iyyar tasu.

Bakin Balarabe dai yayi tattaki ne da Raƙumin shi tun daga Katsina har zuwa Abuja wajen babban taron Jam'iyya domin Karrama ita Jam'iyyar tashi ta APC yayin convention.

Da muke zantawa dashi yace kuɗin da aka bashi ko kuɗin abincin Raƙumin basu kaiba b***e kuma kuɗin Raƙumin kanshi da sauran Dawainiyar da yayi tun daga Katsina har zuwa Abuja kafin kuma daga nan ya yanki hanya zuwa Nasarawa.

Ibrahim yace Shugaban Jam'iyyar ya bashi Dubu Ɗari da Umarnin cewa a ɗauki Raƙumin akai shi Gidan Gona yayin da shi kuma ya k**a hanyar zuwa Abuja, sai dai Ibrahim yace hakan bata saɓuba dan haka yayi Yunƙurin tafiya da Raƙumin shi yayinda su kuma yaran Shugaban Jam'iyyar s**a lallai hakan kuma ba zata yiyu ba.

Ya zuwa yanzu dai Lambar wayar Bakin Balarabe idan an kira tana ta kaɗawa amma ba'a ɗauka 08141918731.

Muna mashi fatan samun mahita akan wannan Lamarin Amin.

MAJIYA- Blueink News Hausa

18/04/2022
Mu Tattauna Tareda; Ibrahim Muh'd TahirYadda ake shan wahala wajen sayan man fetur a wasu jihohin ƙasar nan.Taya kuke ga...
08/03/2022

Mu Tattauna Tareda; Ibrahim Muh'd Tahir

Yadda ake shan wahala wajen sayan man fetur a wasu jihohin ƙasar nan.

Taya kuke ganin za'a shawo kan wannan matsalar?

Ku bayyana mana ra'ayoyin ku a kasan wannan rubutun!

Gwamnatin Legas na bincike kan waɗanda s**a raba man fetur a wurin bikiDaga; Rahoton BBC HausaGwamnatin Jihar Legas da k...
05/03/2022

Gwamnatin Legas na bincike kan waɗanda s**a raba man fetur a wurin biki

Daga; Rahoton BBC Hausa

Gwamnatin Jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta ce tana bincike kan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta inda wasu ke raba man fetur a cikin jarakuna a matsayin kyautar halartar biki.

Kwamashinan Yaɗa Labarai na Legas, Gbenga Omotoso, ya ce "shakka babu wannan lamarin abin haɗari ne kuma zai iya jawo rasa rayuka da dukiyoyi".

A 'yan awannin da s**a gabata ne bidiyon ya ɓulla, inda aka ga jarakunan fetur masu lita 10 a jere da za a raba wa mahalarta bikin. Daily Trust ta ce Chidinma Pearl Ogbulu ce ta shirya taron don murnar naɗa ta a matsayin Erelu Okin.

Yanzu haka 'yan Najeriya na fama da ƙarancin man fetur, inda suke shafe awanni masu yawa a kan dogayen layuka.

KO KAN MABIYA DARIKAR TIJJANIYYA YA RABU NE?Hoto na farko Mauludin Shaikh Ibrahim Inyas ne a Kano Karkashin jagorancin S...
04/03/2022

KO KAN MABIYA DARIKAR TIJJANIYYA YA RABU NE?

Hoto na farko Mauludin Shaikh Ibrahim Inyas ne a Kano Karkashin jagorancin Shaikh Dahiru Bauchi

Sai kuma hoto na kasa, shi ma taron Mauludin Shaikh Ibrahim Inyas ne da ake gudanarwa a jihar Zamfara karkashin jagorancin Sarki Sanusi II.

Address

Angwan Rimi
Jos

Telephone

+2348103706572

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zinariya Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zinariya Hausa News:

Share