04/08/2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Aikin Gyaran Titin Mando–Birnin Gwari Kan Naira Biliyan 178.1
Daga Aliyu Samba
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da aikin sake gina Titin Mando zuwa Birnin Gwari mai tsawon kilomita 122.8 a Jihar Kaduna, wanda aka ware wa kuɗaɗen da s**a kai Naira biliyan 178.1. Titin ya tashi daga Mando da ke kusa da Filin Jirgin Sama na Kaduna zuwa iyakar Jihar Neja.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya wakilta wajen ƙaddamar da aikin a ranar Talata, ya ce aikin zai taimaka wajen inganta harkokin sufuri, ƙarfafa tsaro da kuma bunƙasa tattalin arzikin yankin. Ya ce t**in na daga cikin manyan ayyukan raya ƙasa da za su ƙara haɗa yankunan Arewacin Najeriya da Kudu maso Yammacin ƙasar, tare da sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki.
Shugaban ya bayyana cewa aikin na cikin manyan ayyukan hanyoyin tarayya da gwamnatinsa ta amince da su a watan Mayun 2026 domin faɗaɗa ababen more rayuwa a faɗin ƙasar. Ya kuma tuna cewa tun lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2022 ya yi alƙawarin sake gina t**in idan aka zaɓe shi, yana mai cewa fara aikin ya nuna yadda gwamnatinsa ke cika alƙawuran da ta ɗauka ga 'yan Najeriya.
Tinubu ya ce tsawon shekaru da dama Titin Birnin Gwari ya kasance cikin halin lalacewa sakamakon rashin kulawa da gyara yadda ya kamata. Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta ƙuduri aniyar kawo ƙarshen wannan matsala ta hanyar ci gaba da zuba jari a ayyukan hanyoyi, yana mai jaddada cewa matsayin Jihar Kaduna a matsayin ƙofar shiga yankin Arewa ya sa samar da ingantattun hanyoyi ya zama wajibi domin bunƙasa kasuwanci, zirga-zirga da ci gaban yankin.
Da yake jawabi, Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya ce aikin ya nuna ƙudirin gwamnatin Shugaba Tinubu na samar da ababen more rayuwa da za su inganta rayuwar al'umma kai tsaye. Ya ce baya ga ƙarfafa tsaro a hanyar, aikin zai buɗe damar bunƙasa noma a yankin, wanda zai taimaka wajen ƙara samar da abinci da kuma yaƙi da yunwa.
Umahi ya kuma bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta fara aiwatarwa suna ci gaba da haifar da sakamako mai kyau duk da ƙalubalen da gwamnatin ta gada a shekarar 2023. "Ta hanyar aiwatar da wannan aiki, Shugaban Ƙasa na cika alƙawarin da ya ɗauka ga al'umma, kuma hakan zai haifar da gagarumin sauyi a fannin noma a wannan yanki," in ji shi.
Tun da farko, Babban Sakataren Ma'aikatar Ayyuka ta Tarayya, Adeladan Rafiu Olarinre, ya ce aikin wani ɓangare ne na shirin gwamnatin tarayya na zamani da faɗaɗa hanyoyin Najeriya. Ya ce ana sa ran kammala aikin zai rage wahalar zirga-zirga, ya ƙara bunƙasa kasuwanci, tare da haɓaka tattalin arzikin Jihar Kaduna da jihohin da ke maƙwabtaka da ita.