11/09/2026
HAJIYA JAMILA TUKUR BITRUS TA RABA INJIN NIƘA GA MATA A QUA’AN PAN SOUTH
Tsohuwar Kwamishiniyar Al’adu da Yawon Buɗe Ido ta Jihar Plateau, kuma tsohuwar ‘yar takarar Majalisar Dokokin Jihar mai wakiltar Qua’an Pan South, Hajiya Jamila Tukur Bitrus, ta raba injinan niƙa ga wasu mata a yankin, tare da yin alƙawarin ci gaba da tallafa wa ƙarin mata kafin zaɓen shekarar 2027.
An gudanar da wannan shiri ne a jiya, a yayin wani taron Maulidi da Tallafa wa Mata, inda waɗanda s**a amfana s**a bayyana matuƙar godiyarsu ga Hajiya Jamila. Wasu daga cikin matan sun nuna farin ciki sosai har abin ya kai ga zubar da hawaye na murna, tare da bayyana cewa tallafin zai taimaka wajen bunƙasa sana’o’insu da inganta rayuwarsu.
A cikin wata hira da Ra’ayin Kowa TV, Hajiya Jamila ta sake jaddada muhimmancin yin amfani da ƙuri’a yadda ya kamata, inda ta yi kira ga magoya bayanta da su marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang domin wa’adin mulki na biyu, Hon. Joseph Dadin Dashe, wanda aka fi sani da JoeYouth, domin Majalisar Wakilai ta tarayya mai wakiltar Qua’an Pan, Shendam da Mikang, da kuma Hon. Cornelius Doeyok domin kujerar Majalisar Dokokin Jihar mai wakiltar Qua’an Pan South baya.
A ƙarshe, Shugaban jam’iyyar APC na Kurgwi tare da sauran jiga-jigan jam’iyyar da mahalarta taron sun yaba da wannan yunkuri na Hajiya Jamila, tare da ƙarfafa gwiwar mata da su ci gaba da kasancewa masu goyon baya da imani da ‘yan takarar da suke marawa baya domin babban zaɓen shekarar 2027.
Ra'ayin Kowa TV