Kainuwa Digital TV

Kainuwa Digital TV Kainuwa Digital TV kafar yada labarai ce tare haɗin kan al'umma ta hanyar amfani da muryoyin su.

19/07/2026

Ku Saurari labari mai ban tausayi, 😭😥


Follow Kainuwa Digital TV

AMFANIN YAWAN SALATI GA ANNABI S'A'W ♥️ 281. Yin salati yana sa zuciya ta kasance cikin salama ko da duniya ta rikice.28...
18/07/2026

AMFANIN YAWAN SALATI GA ANNABI S'A'W ♥️

281. Yin salati yana sa zuciya ta kasance cikin salama ko da duniya ta rikice.

282. Mai salati yana samun sauƙin fuskantar jarabawa da hakuri.

283. Salati yana kawar da nauyin bacin rai daga zuciya.

284. Mai salati yana zama abin ƙauna ga bayin Allah.

285. Yin salati yana ƙarfafa zumuncin mutum da iyayensa.

286. Mai salati yana samun albarka a duk abin da ya riƙa.

287. Salati yana sa mutum ya ji daɗin biyayya ga Allah.

288. Mai salati yana samun kariya daga fitinar ƙarshe.

289. Yin salati yana sa zuciya ta zama mai sauƙin karɓar gaskiya.

290. Mai salati yana samun tsarkin rai da zuciya.

291. Salati yana buɗe ƙofofin addu’a ga mai yi.

292. Mai salati yana samun kusanci da Annabi ﷺ a lahira.

293. Yin salati yana sa mutum ya kasance cikin aminci a duniya.

294. Mai salati yana samun natsuwar zuciya mai ɗorewa.

295. Salati yana zama garkuwa daga sharrin shaiɗan.

296. Mai salati yana rayuwa cikin haske da kwanciyar hankali.

297. Yin salati yana ƙara wa mutum ladar ayyuka kaɗan.

298. Mai salati yana samun albarka a numfashinsa.

299. Salati yana zama shaida ga mai yi ranar kiyama.

300. Mai salati yana kasancewa cikin jerin masoyan Annabi ﷺ na gaskiya...


Follow Kainuwa Digital TV

MADINAR MASOYINA ANNABI MUHAMMADU Sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺ Wato a duk lokacin da zuciya ta yi shiru a bakin ƙofar...
18/07/2026

MADINAR MASOYINA ANNABI MUHAMMADU Sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺ

Wato a duk lokacin da zuciya ta yi shiru a bakin ƙofar Madina, addu'a tana fitowa ne daga idanu fiye da yadda take fitowa daga harshe.

Tsayuwa a gaban waɗannan tagogi masu launin zinariya yana sa mutum ya manta da matsayinsa, domin a nan ba buri ne yake magana ba, a’ah tawali'u ne yake magana.

A nan ba kalmomi ne suke gabatar da sallama ba, bugun zuciya ne yake gabatar da ita.

Assalamu Alaika Ya RASULALLAHI ﷺ
Assalamu Alaika Ya HABIB ALLAHI ﷺ

Ya ALLAH! Ka ba mu damar ziyartar wannan ƙofa mai tsarki sau da yawa, mu gabatar da sallama cikin ladabi, kuma Ka ba mu ikon rayuwa cikin sahihiyar ƙaunar Masoyinka Annabi Muhammadu sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺ.


Follow Kainuwa Digital TV

Yha RASULULLAHI Idanuwana suna zubar da hawaye saboda kewar ka Ahmadu Annabi Muhammadu sallallahu alaika Wasallama ♥️ﷺ.Y...
18/07/2026

Yha RASULULLAHI Idanuwana suna zubar da hawaye saboda kewar ka Ahmadu Annabi Muhammadu sallallahu alaika Wasallama ♥️ﷺ.

Yha RASULULLAHI duk abin da ke cikin zuciyata da labarina gaba ɗaya, gare ka nake kai ƙorafina da bayyanawa.

Tsira da amincin ALLAH su tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammadu sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺ.


Follow Kainuwa Digital TV

RAUDHAR MASOYINA ANNABI MUHAMMADU Sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺWannan ba hoto ba ne kawai...Wannan wani yanayi ne na l...
18/07/2026

RAUDHAR MASOYINA ANNABI MUHAMMADU Sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺ

Wannan ba hoto ba ne kawai...
Wannan wani yanayi ne na ladabi, ƙauna da rahama, inda har soyayyahr da wata ƙaramar yarinya take bayyana ƙaunar ta Raudar Manzon ALLAH sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺ.

Duk wanda ya zo wannan ƙofa mai albarka,
yakan manta da damuwar duniya, kuma daga cikin zuciyarsa murya mai taushi kawai tana fitowa tana faɗin...
🌹 اَلسَّلَامُ عَلَيْكَ يَا رَسُولَ اللّٰهِ ﷺ

Ya ALLAH!
Ka azurta mu ma da damar zuwa Raudar Masoyinka Sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺ sau da yawa, ka ba mu cikakken ladabi da ƙaunarsa, kuma a Ranar Alƙiyama Ka azurta mu da cetonsa wato shafa'arsa.

Madina...
Nanne wurin da kowane kallo yake zama ibada,
Ko wace addu'a take zama nutsuwa,
Kuma ko wace zuciya take kiran sa:
"Ya RASULALLAHI Sallallahu Alaika Wasallama ♥️ﷺ."


Follow Kainuwa Digital TV

ASSALAMU ALAIKA YHA MASOYINA ANNABI MUHAMMADU Sallallahu Alaika Wasallama ♥️ﷺ Yha RASULULLAHI ka kasance mai daɗin ƙamsh...
17/07/2026

ASSALAMU ALAIKA YHA MASOYINA ANNABI MUHAMMADU Sallallahu Alaika Wasallama ♥️ﷺ

Yha RASULULLAHI ka kasance mai daɗin ƙamshi a rayuwarka da kuma bayan wafatinka, Ya Manzon ALLAH sallallahu alaika Wasallama ♥️ﷺ. Tsira da amincin ALLAH mafi kyau su tabbata a gare ka.

Yha RASULULLAHI Ƙamshinka mai daɗi ya cika sararin duniya, kuma ambatanka mai haske yana sanya idanu su cika da hawaye.

Yha RASULULLAHI Dukkanmu muna kewarka, kuma rabuwarka ta raunata zukatanmu.

Yha RASULULLAHI Yaya tsawon wannan jira yake, kuma yaya daɗin haɗuwa da kai zai kasance..!

Muna kewarka, Ya Manzon ALLAH.
Muna kewar ganinka.
Muna kewar kasancewa tare da kai.
Muna kewar musafaha da kai.
Muna kewar zama tare da kai.
Muna kewar murmushinka.
Muna kewar rungumarka.
Muna kewar sauraron hadisanka.
Sallallahu Wasallama alaika ya Annabi Muhammadu sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺ


Follow Kainuwa Digital TV

FATAN HAƊUWA DA ANNABI MUHAMMADU Sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺYha RASULULLAHI Ina fatan zan haɗu da kai a wurin Al-Hau...
17/07/2026

FATAN HAƊUWA DA ANNABI MUHAMMADU Sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺ

Yha RASULULLAHI Ina fatan zan haɗu da kai a wurin Al-Haud wato (Tafkin Al-Kausara) kana murmushi, kuma in zo in sumbaci hannunka mai albarka da farin haske.

Yha RASULULLAHI Lallai ƙaunarmu da kewarmu gare ka, Ya Manzon ALLAH sallallahu alaika Wasallama ♥️ﷺ, ta daɗe ƙwarai a cikin zuciyar mu.

Tsira da amincin ALLAH mafi kyau mafi daɗi su tabbata a gare ka ya Masoyina Annabi Muhammadu sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺ

Lokacin da kewa take magana...
Idanu suke zubar da hawaye...
Zukata suke ƙuna da ƙauna...
Sai ƙaunar da kewa su fashe daga cikin zuciya,
Hawaye kuma su gangaro,
Saboda ƙauna, kewa da shauƙi ga Masoyi.

Wato Annabi Muhammadu sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺ, wanda tsira da amincin ALLAH mafi kyau su ka tabbata a gare shi.

ALLAH ya ƙara maka daraja uban matsayi sallallahu alaika Wasallama ♥️ﷺ


Follow Kainuwa Digital TV

Wannan Shi ne Wurin da Aka Wanke Raunukan Manzon Allah ﷺ Bayan Yaƙin UhudSha'ibul Jirār (شِعْب الجرار) wani muhimmin wur...
17/07/2026

Wannan Shi ne Wurin da Aka Wanke Raunukan Manzon Allah ﷺ Bayan Yaƙin Uhud

Sha'ibul Jirār (شِعْب الجرار) wani muhimmin wuri ne da ke da alaƙa da Yaƙin Uhud. A nan ne aka ɗebo ruwa daga ramukan da ake kira Mahārīs domin a wanke raunukan Manzon Allah ﷺ bayan ya ji rauni a yaƙin. Lokacin da jininSa bai tsaya ba, Sayyida Fāɗimah (RA) ta ƙona wani ɗan tabarma, ta yi amfani da tokarta wajen danne raunin har jinin ya tsaya da yardar Allah.

Haka kuma, a wannan yanki ne akwai Masallacin Fasḥ, inda Annabi ﷺ ya yi Sallah bayan kammala Yaƙin Uhud. A yau, abin da ya rage daga masallacin wasu duwatsu ne kawai, kuma an fara gina shi a zamanin Umar bn Abdul'aziz (RAH).

Muna addu'an Allah SWT ya sanya albarka a rayuwar mu, ya bamu albarkan IYAYEN mu. Amiin Yaa ALLAH.


Follow Kainuwa Digital TV

ASSALAMU ALAIKA YHA RASULULLAHI Sallallahu Alaika Wasallama ♥️ﷺ Ganinka a wurina ya fi darajar dukkan duniya baki ɗaya. ...
16/07/2026

ASSALAMU ALAIKA YHA RASULULLAHI Sallallahu Alaika Wasallama ♥️ﷺ

Ganinka a wurina ya fi darajar dukkan duniya baki ɗaya. 🌹

Ya Shugabana, Ya Manzon ALLAH, tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare ka. 💚


Follow Kainuwa Digital TV

ALLAH ka ƙaddara mana tsayuwar gaban Annabi Muhammadu sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺMuyi masa sallama mu ce masa ASSALA...
16/07/2026

ALLAH ka ƙaddara mana tsayuwar gaban Annabi Muhammadu sallallahu alaihi Wasallama ♥️ﷺ

Muyi masa sallama mu ce masa ASSALAMU ALAIKA YHA RASULULLAHI

Ajib ya RASULULLAHI 😥😭


Follow Kainuwa Digital TV

Address

Jos
223567

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kainuwa Digital TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share