04/02/2026
ABINDA YA FARU DAZU A BIRNIN JOS
Dazu da safe wani abu ya faru a cikin birnin Jos inda aka kalli rana a sararin samaniya ta kasu gida uku
Masu ilimin sararin samaniya sun yi bayanin abinda ya haifar da faruwan haka
Sunce wannan abin ba abin damuwa bane, kuma rana ba ta tsage ninki uku ba
Abinda aka gani wani yanayi ne na halitta a sararin samaniya da ake kira "sun dogs" ko ''Parhelia"
Amma me yasa rana ta yi k**a da guda uku?
Ranar gaske ita ce wadda take haske sosai a tsakiya, wadanda suke k**ar karin ranaku a hagu da dama su ne "sun dogs" ko "parhelia", wanda suna faruwa ne idan hasken rana ya ratsa kananan kwayoyin kankara (ice crystals) da ke sama a cikin gajimare
Wadannan kwayoyin kankarar suna aiki k**ar madubai ko ''prism'' wato wani abu mai siffa ta musamman da ke karkatar da haske, suna karkatar da hasken rana su haifar da wuraren haske a matakin rana daya
Me yasa hakan ya faru da safiyar yau a birnin Jos?
Idan gari ya waye wato da safiya rana tana kasa sosai a sararin samaniya, ana samun iska mai sanyi da siraran gajimare, shi ya sa ”sun dogs” s**a fi yawan bayyana da safe ko da yamma
Shin yana da hatsari ko wata alama marar kyau?
-Faruwar wannan ba matsala ba ce
-Ba hari na aljani ko na ruhanai bane
-Ba lalacewar ido ba ne
-Ba bala’in sauyin yanayi ba ne
Wannan Ilimin lissafin kimiyya (physics) ne kawai, yanayin sararin sama suna aikinsu k**ar yadda Allah Madaukakin Sarki ya tsara
Allah Ya sa mu wanye da duniya lafiya