MYD Media Concept Yelwa

MYD Media Concept Yelwa The fashion of journalism is prior, Starting seens primary school

05/09/2026

The ward of prayer during the ongoing two day medical outrich

05/09/2026

Manya iyayen Katsa!!!

05/09/2026
04/09/2026

I accepted 1 fan badge from Eagle FM 95.5.

I really appreciate, may Almighty Allah shower his blessings for Us.

With Eagle FM 95.5 – I've just made it onto their weekly engagement list by being one of their top engagers!
04/09/2026

With Eagle FM 95.5 – I've just made it onto their weekly engagement list by being one of their top engagers!

GIDAUNIYAR LAMIR TA SHIRYA GAGARUMIN SHIRIN DUBA LAFIYA DA TALLAFAWA MABUKATA A YELWA.‎‎Gidauniyar Lamir ta sanar da gud...
02/09/2026

GIDAUNIYAR LAMIR TA SHIRYA GAGARUMIN SHIRIN DUBA LAFIYA DA TALLAFAWA MABUKATA A YELWA.

‎Gidauniyar Lamir ta sanar da gudanar da wani gagarumin shirin duba lafiya da tallafawa al’umma na tsawon kwanaki biyu, domin taimaka wa mutane masu karamin karfi da wadanda ke cikin mawuyacin hali.

‎Za a gudanar da shirin ne a ranakun 5 da 6 ga Satumbar, 2026, a Lalong Legacy Project, da ke kan titin Garkawa, Yelwa, Ƙaramar Hukumar Shendam ta Jihar Plateau.

‎Shirin dai wani bangare ne na bikin cikar Hon. Lamir Umar Ibrahim shekaru 40, kuma zai kunshi binciken lafiya da ba da magunguna kyauta, da kuma tallafa wa marasa karfi domin inganta rayuwarsu.

‎A yayin shirin, jama’a za su samu damar duba lafiyarsu ba tare da biyan wani kudi ba, yayin da wadanda ke cikin bukata za su samu tallafi da sauran abubuwan da aka tanada domin rage musu radadin matsalolin rayuwa.

‎Gidauniyar Lamir ta bayyana cewa wannan shiri na daga cikin kokarinta na inganta jin dadin al’umma, tallafa wa mabukata da kuma gina kyakkyawar makoma.

‎Ana kuma sa ran shirin zai samu halartar dimbin jama’a daga Yelwa da sauran sassan Ƙaramar Hukumar Shendam, musamman wadanda ake sa ran za su amfana da ayyukan jin kai na gidauniyar.

‎Gidauniyar ta yi kira ga al’ummar Yelwa da kewayenta da su yi amfani da wannan dama, domin amfana da ayyukan kiwon lafiya da tallafin da aka tanada.

‎✍️ DY Musa.

02/09/2026

TSARABAR SAFIYA

Manzon Allah {ﷺ} ya ce: Babu biyayya a cikin saɓon Allah; haƙiƙa, biyayya tana cikin abin da yake na alheri.

[ƘARIN HASKE]
Hadisin yana koyar da cewa ba ya halatta mutum ya yi wa wani biyayya wajen aikata abin da Allah Ya haramta, ko da kuwa mutumin yana da iko ko matsayi.

Amma idan aka umurci mutum da abin da yake na alheri kuma bai saɓa wa Allah ba, to ana umartar shi da yin biyayya.

Misali: Idan shugaba ko wani mutum ya umurce ka da aikata zunubi, To fa ba a bin umarninsa a wannan al'amari. Amma a cikin abubuwan da suke halal da alheri, ana yin biyayya.

Darasi: Biyayya ga halitta tana da iyaka; ba a yin biyayya ga wani wajen saɓawa Allah.

ALLAH YA DATAR DA MU DA FALALARSA.

✍️DY MUSA

Address

Jos

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MYD Media Concept Yelwa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share