17/07/2026
KOTU TA BA DA UMARNIN KWACE JAMI'A, GIDAN REDIYO DA WASU KADARORI 46 DA AKE ALAƘANTA WA TSOHON AGF,
ABUBAKAR MALAMI
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin ƙwace kadarori 48 da ake alaƙanta wa tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN), tare da mayar da su mallakin Gwamnatin Tarayya.
Kotun ta amince da buƙatar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), bayan ta tabbatar da cewa an gabatar da hujjojin da ke nuna cewa kadarorin ana zargin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka, kuma ba a mallake su ta hanyar halastacciyar hanyar samun kuɗi ba.
Daga cikin kadarorin da kotun ta umarci a ƙwace akwai:
• Jami'ar Rayhaan, har da harabar ta ta dindindin da ta wucin gadi.
• Gidan Rediyon Rayhaan.
• Gidan zama na Shugaban Jami'a (Vice Chancellor).
• Otal-otal.
• Gidajen alfarma.
• Gine-ginen kasuwanci.
• Gidajen mai.
• Masana'antu.
• Manyan filayen ƙasa da sauran kadarori da ke Abuja, Kebbi da Kano.
Mai shari'a, Joyce Abdulmalik, ta ce Abubakar Malami, 'yan uwansa da wasu da ake alaƙanta da shi sun kasa gabatar da isassun hujjoji da za su tabbatar da cewa sun mallaki waɗannan kadarori ne ta hanyar halal.
Kotun ta kuma bayyana cewa iƙirarin mallaka kaɗai bai isa ba a irin wannan shari'ar ƙwace kadarori ba tare da samun hukuncin laifi (non-conviction-based forfeiture).