
13/07/2025
“Zamu Fito da Tsare tsare masu kyau da zasu Bunkasa Kasuwar waya ta karamar hukumar Dandume" Inji Hon. Ashiru Umar Gaye
Daya daga cikin fitattun ‘yan takarar shugabancin kungiyar masu sana’ar sayar da waya a karamar hukumar Dandume, wato Dandume Phone and Accessories Sellers Association (DAPAS), Hon. Ashiru Umar Gaye, ya bayyana cewa babban burinsa shi ne inganta kasuwanci, musamman ga matasa da kananan ‘yan kasuwa.
A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Dandume, Hon. Ashiru Umar Gaye ya ce, idan ya samu nasarar lashe zaben shugabancin kungiyar, zai bullo da tsare-tsare na musamman da za su taimaka wajen bunkasa sana’o’in masu ƙaramin karfi, tare da samar musu da damammaki na ci gaba.
Burina shi ne bunƙasa kasuwar waya ta Dandume gaba ɗaya. Zamu fito da shirye-shirye na musamman da za su bai wa matasa da kananan ‘yan kasuwa damar faɗaɗa harkokinsu cikin gaskiya da rikon amana,” inji shi.
Manufofi da Tsare-tsaren Hon. Ashiru Umar Gaye ya bayyana wasu daga cikin muhimman abubuwan da yake da niyyar aiwatarwa idan aka ba shi damar jagorantar DAPAS:
1 Kare martabar kowane mamba na ƙungiya a ko’ina, musamman a cikin jihar Katsina.
2 Ƙarfafa dangantaka mai kyau tsakanin masu sayar da waya da abokan hulɗarsu, domin kasuwanci ya gudana cikin fahimta da jin daɗi.
3 Inganta tsarin warware sabani da rikice-rikice cikin gaskiya da adalci tsakanin abokan kasuwanci.
4 Ƙirƙiro hanyoyin tallafi ga kananan ‘yan kasuwa domin ƙarfafa su su zama masu gaskiya da nagarta a harkokinsu.
5 Inganta hanyoyin samun kudaden shiga na ƙungiya ba tare da takura wa mambobi ba.
Ya ce zai tabbatar da cewa, idan aka ba shi amanar shugabanci, DAPAS za ta zama abar koyi a fannin shugabanci da haɗin kai a fadin jihar.
Idan har aka bani amanar shugabanci, zan tabbatar da cewa wannan ƙungiya ta zama tubalin ci gaba a Dandume da ma jihar Katsina baki ɗaya,” inji Hon. Ashiru Umar.
Tuni dai zaben shugabancin ƙungiyar DAPAS ya ɗauki zafi a Dandume, inda ‘yan takara da dama ke ci gaba da bayyana manufofinsu. Sai dai, Hon. Ashiru Umar Gaye na daga cikin fitattun ‘yan takarar da s**a fi jan hankalin matasa da ‘yan kasuwa, sak**akon tsare-tsaren ci gaba da yake gabatarwa da kuma irin kwarin gwiwar da yake bai wa jama’a.