Gizo Gizo Online

Gizo Gizo Online An samar da shafin nan ne domin ba da sahihan labarai dake faruwa a kasa Nigeria da sauran sassan duniya gami da ilmantarwa fadakarwa da nishadantar wa.

TIRKASHI: Samun Sallar Asuba a cikin Jam'i  ya fi Mauludi sau dubu goma (10,000).Inji Matashin Sha'irin nan na Kano Mala...
06/09/2025

TIRKASHI: Samun Sallar Asuba a cikin Jam'i ya fi Mauludi sau dubu goma (10,000).

Inji Matashin Sha'irin nan na Kano Malam Usman Mai Dubun Isa.

Me za ku ce?

Bazan taba manta ranar 28 June 2017 ba, A ranar ne wannan mugun azzalumin ya kashe mun yaya na abdulaziz har lahira, Yay...
28/08/2025

Bazan taba manta ranar 28 June 2017 ba, A ranar ne wannan mugun azzalumin ya kashe mun yaya na abdulaziz har lahira, Yayana wanda nake binsa. Sun bishi har wurin aikin shi na kanikanci a Unguwar Mu'azu s**a soka mishi makami mai tsini sai da s**a taba zuciyarsa.
kawai saboda suna jin haushin maihaifin mu saboda baya goyon bayan mummunar dabiar su ta sata da kwacen kayan mutane, sun rasa yadda zasuyi da baban mu shine s**a huce haushin su akan yayana 😭😭😭tsakanin mu da wannan azzalumin sai mun hadu a gaban Allah.

Zainab Tahir ✍🏿

Daga Shafin Farfesa Malumfashi Ibrahim Aliyu MohammedMasha Allah!“Hausa da Hausawa a Ƙarni na 21.”Taron RANAR HAUSA TA D...
26/08/2025

Daga Shafin Farfesa Malumfashi Ibrahim Aliyu Mohammed

Masha Allah!

“Hausa da Hausawa a Ƙarni na 21.”

Taron RANAR HAUSA TA DUNIYA da Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe na Jami’ar jihar Kaduna ya shirya ya gudana, ya kuma ƙayatar ƙwarai da gaske!

Godiya ta musamman ga Shugaban Jami’ar Jami’ar jihar Kaduna, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa da Shugaban Sashe, Dakta Samaila Mijinyawa da s**a ƙarfafa wannan taro ya gudana, ya kuma yi armashi fiye da yadda muka yi tunani.

Godiya ga masana daga sassa daban-daban na duniya da s**a karɓa gayyatarmu, s**a baƙunci wannan zaure, k**ar su Dakta Li, Malamin Hausa a jami’ar Nazarin Harsunan Ƙasashen Waje da ke Beijing, ƙasar China da Dakta Umma Aliyu Musa, malamar Hausa daga Jami’ar Hamburg da ke Jamus da kuma Farfesa Ibrahim Hamza, masanin tarihi da rayuwar Hausawan Brazil da ke Jami’ar York, Toronto, Canada da kuma Dakta Muhammad Nabil, malamin Hausa da ke Jami’ar Cairo a ƙasar Masar da Farfesa Ƙassim Bilal daga Jami’ar Sebha a ƙasar Libya da kuma Farfesa Nakamura daga ƙasar Japan.

Haka kuma fitattun masana harshen Hausa da adabi da al’adun Hausawa daga nan cikin Nijeriya sun ba maraɗa kunya, sun shigo zauren, sun baje hajar ilimi a wannan tattaunawa. Akwai Farfesa Salisu Ahmed Yakasai, daga jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato da Farfesa Abdallah Uba Adamu daga jami’ar Bayero Kano.

Haka kuma godiya ga sauran malaman Sashe da s**a samu shiga cikin wannan zaure domin samun damar tattaunawa da kuma ɗimbin masana da malamai da ɗalibai na Hausa da sauran fannonin ilimi daga sassan Nijeriya daban-daban.

Mun gode!

Allah ya biya kowa da kowa da mafificin alheri.

Allah ya bar zumunci.

KAN BATUN CANZA SUNA A FACEBOOK An wayi gari da rubuce-rubucen cewa facebook suna rufewa mutane account wai har sai mutu...
24/08/2025

KAN BATUN CANZA SUNA A FACEBOOK

An wayi gari da rubuce-rubucen cewa facebook suna rufewa mutane account wai har sai mutum ya gabatar musu da katin shaida na gwamnatin kasar sa mai dauke da sunan dake kan shafin sa na facebook 😀

Amma sam abin bayyi k**a da hankali ba dalili kuwa shine, ta yaya facebook suke sanin cewa sunan shafin ka bayyi k**a da sunan ka na ainahi ba, ko dai shafukan kowa zasu rufe sannan su bukaci kowa ya gabatar da shaida? Wannan ba abune mai yiwuwa ba, don me yasa facebook zata bukaci sunan mai amfani da ita na ainahi? Shin akwai wata sanarwa ne daga shafin meta dake nuna cewa lallai wannan mataki gaskiya ne? Me yasa facebook zata dauki matakin batare da ta sanar da mabiyan ta ba? Akwai wata sanarwa ne daga gwamnatin kasar ka akan hakan?

GA ABINDA YASA AKE RUFEWA MUTANE ACCOUNT A FACEBOOK

Facebook kaface dake da ka'ida da sharudda daban daban wasu daga cikin su akwai wallafa ababen tashin hankali k**ar hatsari, gobara, jini, gawarwaki, da kalaman ta@ddanci, satar fasaha da dai mak**antansu, aduk lokacin daka saba ƙa'idar facebook zasuyi maka gargadi idan baka kiyaye ka cire ko ka goge ba facebook zasu sanya maka takunkumi ma'ana su rufe maka account sai su buƙaci ka gabatar musu da katin shaida kafin su buɗe ka to anan fa idan ka gabatar da katin daya saɓa da sunan ka to sai kasha baƙar wahala kafin account dinka ya dawo koma ka rasa shi duka.

Saboda haka matukar bazaka karya dokar facebook ba baka da matsala da canza suna kabar sunan ka a yadda yake kai dai kawai ka guji karya dokokin su shine kawai

Jama'a ku daina canza sunayen ku har sai kun samu sanarwa daga facebook, facebook baza ta rufe muku account ba haka kawai su jama'a suke nema basa korar jama'a....

Kun dai san yanayi na neman followers ba sai na gaya muku komai ba

Idriss M Idriss Damaturu Ɗan Jarida .

Ko yan bana bakwai sun san wannan kuwa?
24/08/2025

Ko yan bana bakwai sun san wannan kuwa?

Sharhin Shams Musa Abban Sanam akan malamaiBã ina nufin wa'yanda ke hotunannan ke raba kan al'umma ba, amma su ake kallo...
21/08/2025

Sharhin Shams Musa Abban Sanam akan malamai

Bã ina nufin wa'yanda ke hotunannan ke raba kan al'umma ba, amma su ake kallo idan ana maganar rabuwa.

Idan aka tambayeka tsakanin malamai da yan siyasa suwaye shuwagabannin addini? kowa zaice malamai.

Ma'anarshi! Duk sanda aka samu rabuwar kai a addini laifin malamai ne, domin sune أولي الأمر منكم a Al-Qur'ani, dole su kira 'yan siyasa su zo gabansu

Ku ga yadda Ayãtullahi Khomeini ya juya 'yan siyasar Iran, da Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi a najeriya.

Nã sauka a ra'ayina na cewa 'yan siyasa ke raba malamai, malamai ke raba kai sunã jin dadi k**ar fadin Allah كل حزب بما لديهم فرحون malaman qungiya daya sun zama qungiyoyi da sunan addini saboda duniya.

Ko wannensu yakan debi tawagarsa zuwa wurin yan siyasa ya musu fadanci a biya masa bukatun qungiyarsa.

Malamai ke cewa yan siyasa su cire baki a harkar addini domin fagen malamai ne, amma sai kaga malami yã je wurin dan siyasaya ya kai karar malami kuma ya fadi yadda za ayi da malamin kuma ya karbi aikin aiwatar da hukuncin a mimbarinsa.

Dã Allah zai ba yan siyasa ikon su fadiwa al'umma munafinci da malamai ke kai musu kan malamai dã mutuncinsu yã wãtse.

A duk sanda ake tuhuman 'yan siyasa da cewa sunã raba kan musulmai, miyãgun malamai dãdi suke ji domin bazã'a gãne cewa sû ne shaidanun ba.

Wannan rabuwar kai da ake ciki tã fi yiwa shaidanun malamai dadi, domin ta hakane suke iya tãrãwa kansu da iyãlansu duniya.

Malamai sun damalmala hanyar da za'abi a hada kansu da gangan dan sunã jin dadin yadda ake tafiya a rabe duk da su na karyar cewa yã k**ata a hada kai.

Wa'yanda s**ace a hada kai, su s**a rabu bãyan an hadu, yanzu kuma suke cewa a hadu.

Yã k**ata mu dãwo hayyacimmu, da irin wa'yannan malaman su mayar da mu macijin roba suna wasa da mu, gara mu mayar da su muyi wasa da su.

Idan ka gãne zã su barka, zãsu janyo wa'yanda basu san komai ba suyi ta musu karya.

Matsalar rabuwar kai laifin malamaine, kada a yaudareku da cewa 'yan siyasa ne.

Wassalamu Alaikum

Ni yar asalin KABILAR Birom che anan Jos, na fara sha'awar sana'ar film ne tun ina karamaBanyi dogon karatu ba iya Secon...
14/08/2025

Ni yar asalin KABILAR Birom che anan Jos, na fara sha'awar sana'ar film ne tun ina karama

Banyi dogon karatu ba iya Secondry School nayi amma AlhamdulilLah, yanzu kuma na samu karatun zama da mutane.

Nayi aure na samu jarabawa na rabu da mijina wanda daga baya na haɗu da wata Hajara yanzu kwamishina che a jahar Bauchi. Ta kai ni wajen Hayas Film Production daga nan aka Kaini lenzcup daga bisani yayana ya samamun aikin radio duk ban fada a gida ba.

Na shiga film din Hausa na fito a chikin shirin Babban kasa wanda a karin farko keinan dana taɓa ganin Jaruma Daso wanda tsaban kallon ta sai da na buga kaina da murfin windo.

Kalu baken dana samu shine sai da nake Kano na gayawa lalata Chewa gashi inaso nayi film ita kuma taxo ta gaya iyaye na.

Abun da yafi burge Mahaifi na shine yaji anyi hira dani ban boye yare na da inda na fito ba hakan yasa mahaifinsa Yache in ci gaba da film dina Allah ya samun albarka.

Ni ko a fina fina India mutum me mugunta yana burge ni.

Abun da yafi ban wahala a film shine yawan zuwa chanja dressing da ake Chewa ayi Sabida daukar gurare daban daban.

Abun da yafi faranta mun rai shine banda mahaifi banda mahaifiya duk sun rasu, dan haka in naga sao'in sun inna faranta musu sai inji k**ar wa nawa nayi.

Ina son zama k**ar matar wani dan majalisar anan Jos Laylah Ali Othman in zamo me kyautata da temakon mutane.

Shawara ta ga Jarumai yan Film shine Muji tsoron Allah a duk inda muke a duk abun da muke.

Hirar Jaruma Hauwa Musa Adam da BBC Hausa.

Jaruma Rahama Sadau Allah yayi lokaci yayi. Ubangiji ya ba da zaman lafiya a gidan auren ki, ya kuma sanya albarka.Baba ...
09/08/2025

Jaruma Rahama Sadau Allah yayi lokaci yayi. Ubangiji ya ba da zaman lafiya a gidan auren ki, ya kuma sanya albarka.

Baba kuma Allah ubangiji shima ya ji kansa da rahama. Amin

“YADDA ƳAN SANDA S**A K**A NI, BA TARE DA SANIN CEWAR NINE KWAMISHINAN ƳAN SANDA BA” – MD ABUBAKAR“A lokacin da nake Kwa...
08/08/2025

“YADDA ƳAN SANDA S**A K**A NI, BA TARE DA SANIN CEWAR NINE KWAMISHINAN ƳAN SANDA BA” – MD ABUBAKAR

“A lokacin da nake Kwamishinan Ƴan Sanda a jihar Lagos, bana wasa da aiki — musamman ranar Asabar. Ko da yake ayyuka na suna farawa ne daga karfe 10 na safe, wannan rana na tashi tun 6 na safe don in kai ziyara ba tare da sanarwa ba.

Na hau motata Jeep na nufi ofis, amma sai na yanke shawarar yin ‘yin ziyarar ba-zata’ ga wasu 'yan sanda a kan hanya – domin in ga irin yadda suke gudanar da aikinsu.

A wani shingen bincike “checkpoint” dake t**in Herbert Macaulay, wasu matasan 'yan sanda s**a tsaida ni. Wani karamin dan sanda (constable) ya kalle ni yace:

> "Kai saurayi, ina zaka ne da motar mahaifinka?"

Ya bukaci takardun motar da shaidar lasisin tuƙi. Na ce masa sunana Mohammed. Yace dole sai na nuna ID card. Na ce masa, to ya fara nuna mini nasa. Bai da ID card, don haka sai ya kira sergeant dinsu.

Shi ma sergeant din ya bukaci ID card dina, na ce masa ya nuna mini nasa kafin nawa. Ganin bana jin tsoro ko nuna daraja, sai s**a ce mu tafi ofishin ‘yan sanda na Yaba (Panti) domin “gano ko ni wanene”.

Muna isa station – babu parking sai a wajen DPO. Na ajiye motata a can, constable din ya fusata yace: “Wannan wajen parking din DPO ne fa!” Ko uffan ban ce masa ba.

Bayan mun shiga ciki, sai s**a kaini wurin wani ASP (Assistant Superintendent of Police) wanda ke sanye da gajeren wando 'shorts'!. Yace na shigo, na ki, nace masa ba zai yiwu ya tuhumeni cikin kayan gida ba. Yayi fushi ya jawo ni ciki da ƙarfi – nima ina jan shi. Da ya duba fuskata da kyau sai ya fara zare ido…

A gefe guda, wani tsoho da ke ofishin ya leƙa ofishin DPO don duba hoton shugabannin rundunar Ƴan sanda dake jikin bango. Da ya tabbatar cewa ni ne, sai kawai ya tsallake taga ya gudu!

Sergeant da ya kawo ni ya kasa gane me ke faruwa, har sai da wani Ɗan sanda ya matso kusa da kunnensa, ya ce masa: “Kai, CP ne wannan fa!”

Cikin firgici, ASP ɗin da ke sanye da shorts ma ya bi taga ya gudu!

Bayan haka, Area Commander ya kirani ya tambaya me ya faru. Aka gaya masa cewa an tsare DPO, ASP, da sauran ‘yan sanda da s**a shiga lamarin – suna jiran umarni na.

Abin da ya fi tada min hankali ba wai kamun da s**a yi min ba ne – a’a, amma irin yadda s**a nuna rashin tarbiyya, rashin horo, da rashin kwarewa a aiki

Yaya dan sanda zai tsaya a t**i ba tare da ID ba, yana tsare jama’a? Yaya ASP zai zauna da kaya irin na gida yana sarrafa aiki? Wannan ya kara tabbatar min da cewa shugabanci ba sai ka zauna ofis ba – dole ka fita ka duba, ka gani da idonka, ka tabbatar da gaskiya da adalci a kowanne mataki

Fassara: AB Damare

Wasu sun fassara wannan bayanin na Prof Abdallah Uba a matsayin raddi ga Fatima Hussain (Maryam Labarina) but Ni ba a ma...
05/08/2025

Wasu sun fassara wannan bayanin na Prof Abdallah Uba a matsayin raddi ga Fatima Hussain (Maryam Labarina) but Ni ba a matsayin raddi na kalla ba, idan ma raddi ne, to raddi ne ga Mata masu irin wannan ɗabi'ar, ba Fatima Hussain kaɗai ba. Abinda yasa za'a ga k**ar raddi ne ga Fatima Hussain, saboda a dai dai wannan lokacin shirman da tayi yake trending, wanda na tabbata hakan yasa Professor yai mentioned sunanta, ba dan ta isa ba.

To mu ƙaddarama raddin ne, duk rashin darajan mutum idan yayi magana wanda zai ɓata tarbiyan al'umma, babu laifi dan anyi masa raddi, an ja hankalin al'umma su guje wa karantarwar sa. Yanzu dai ya rage wa Mata, suyi amfani da karantarwar Fatima Hussain ko su watsar, idan sunyi amfani dashi, to duk sak**akon da ya basu kada s**e Maza sun zaluncesu, dan ba Namijin da zai zauna ya zura miki ido kina rashin daraja, ba lallai ba tilas, sai ki koma gidan iyayenki kiyi yadda k**e so.

Da KannyWood za ta burgeni da ta dakatar da Fatima Hussain da sauran yara uku ɗin cen, hakan ya zama izina ga duk Macen da tayi register da masana'antar ta san cewa ba komi za tayi magana akai ba, saboda gudun janyo wa masana'antar zagi.

Inji: Elkhaleel Muhammad

Me za ku ce?

Hoton Tsoffin Gwamnonin Jihar Kano Guda Biyu: Daga Hannun dama marigayi Alhaji Abubakar Rimi, daga Hagu marigayi Sanata ...
31/07/2025

Hoton Tsoffin Gwamnonin Jihar Kano Guda Biyu:

Daga Hannun dama marigayi Alhaji Abubakar Rimi, daga Hagu marigayi Sanata Sabo Bakinzuwo, a liyafar sulhu da aka shirya musu bayan fitowarsu daga kurkuku a shekarar 1985, bayan da gwamnatin Janar Buhari ta daure Sabo Bakinzuwo shekaru 300 a gidan yari, shi kuma Abubakar Rimi Shekaru 180 a gidan yari. Gwamnatin Janar Babbangida ce ta fito da su bayan Juyin mulkin da ta yiwa Gwamnatin Buhari.

Da ga alkalamin Farfesa Malumfashi Ibrahim.Bashin miliyan 10 ga Malaman Jami'o'i!Ya k**ata a gane wani abu game da haka....
31/07/2025

Da ga alkalamin Farfesa Malumfashi Ibrahim.

Bashin miliyan 10 ga Malaman Jami'o'i!

Ya k**ata a gane wani abu game da haka. A cikin tsawon shekara 16 dai ba a ƙara ƙimar albashin malamai ba, saboda haka zuwa yanzu talauci ya samu gida ya zauna a rayuwar yawancin malaman jami'o'i.

A cikin tsawon wannan lokaci, malaman jami'o'i na bin haƙƙoƙi da sun wuce miliyan goma, inda za a biya su, ba ka-ce-na-ce!

Saboda haka abin da ake so a yi shi ne, tun da bashi ya yi wa malaman jami'o'i katutu, haƙƙoƙinsu kuma an danne, an ƙi biya, sai a tura masu bashi da za su biya daga ɗan ɗaunin albashin da bai taka, kara ya karya ba!

Ana yin haka shi ke nan an gama bautar da malaman jami'o'i na har abada! Akwai abin da BAWA kuma zai iya yi daga wannan lokaci?

Sai dai ko jiran mankara!

Address

Gamagira Street
Kaduna South

Telephone

+2349024527474

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gizo Gizo Online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share