19/07/2021
Copy From Shariff Tijjani Abul-fathi
TSOKACI AKAN MUQABALAR KANO ; AN KASHE MACIJI- AMMA…….
Na saurari audiyon da aka dauka na Muqabala tun daga farko har qarshe (kuma ina kyautata zaton recording din yafito ne daga wajen Malam Abdul-Jabbar –b***e mabiya s**e ba cikakken najiba ) ;Sannan naji kuma na karanta sharhohi da Juma’a s**a tayi kan wannan Muqabala mai dumbin tarihi. Toh Alhamdulillahi anyi lafiya - kuma an gama lafiya; amma an bar baya da Qura.
Saboda k**ar yadda Malam Abdul-jabbar yayita qorafin cewa ba isashen lokaci ,hakazalika Malaman da yakira da YAN MAJA suma suke qorafin ba’a basu isashen lokaci ba - don zube SHUBUHOHIN a faife attauna sosai ta yadda za’a wareware zare da abawa ga masu sauran shakku.
Sheikh Abubakar Madatai yana daya daga cikin wandanda yayi wannan qorafin acikin hirarsa akan pejin SARKI ZAAKI MKK AMEEN na awa uku –wanda acikin wannan hiran zan dauki wasu niqdodi masu amfani inyi Magana akansu.
An masa tambayoyi k**ar haka-
Alaqar Abdul jabbar da Shi’a da kuma shin awane aji Abdul jabbar yake cikin ilimin Hadisi…?
ZUBA MAS’ALOLIN ABDUL-JABBAR AFAIFE.
Lalle cikin hanyoyin nan uku masu zuwa dole asamu mahangar datasa Malam Abdul-jabbar cikin wannan matsaloli na YAQAR MALAMAN HADISI, QARYATA SAHABBAI da kuma SAKIN HARSHE AJANIBIN ANNABI (SAW).
MAHANGA TA FARKO ITACE TA KAFIRAN DUNIYA:
A da’awar Abdul-Jabbar yana kallon Hadisannan da irin madubin da Maqiya Allah da Manzonsa suke gani. Duk da k**ata yayi ace amatsayinsa na babban Malami mai bincike yasan cewa tun daga farkon bayyanar musulinci wadannan mutanen basu ta6a ganin abu mai kyau acikin musulinci ba. Duk kyan abu idan musulincine ya kawoshi- toh lalle sai sunyi iya qoqarinsu wajen muzantashi. Wannan aikine da SHAIDAN yadora musu, kuma bazasu bari ba har duniya tatashi. Hatta Allah (SWA) yagayawa Annabinsa acikin AL-QURANI Mai girma :
وَلَن تَرْضَىٰ عَنكَ ٱلْيَهُودُ وَلَا ٱلنَّصَـٰرَىٰ حَتَّىٰ تَتَّبِعَ مِلَّتَهُمْ ۗ قُلْ إِنَّ هُدَى ٱللَّهِ هُوَ ٱلْهُدَىٰ ۗ وَلَئِنِ ٱتَّبَعْتَ أَهْوَآءَهُم بَعْدَ ٱلَّذِى جَآءَكَ مِنَ ٱلْعِلْمِ ۙ مَا لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن وَلِىٍّ وَلَا نَصِيرٍ
Babban misali akan haka ,mun taso da wayonmu muna ganin bidiyon SHEIKH AHMAD DEDAT yadda yake muqabala dasu akan Al-qur’ani mai girma da kurakurenda ke cikin littattafansu- amma har zuwa rana mai Kaman ta yau wadannan bayin Allah sunada WEBSITE dinsu wadanda suke iya qoqarinsu naganin sai sun wareware Al-qur-ani mai girma tahanyar aibatashi da nuna akwai kurakure acikinsa (WA- IYAZU BILLAH ) duk da Allah yayi musu tahaddi acikin Al-qur-ani na su kawo kwatankwacinsa amma dadai da Ayah daya sun kasa kawowa :
قُل لَّئِنِ ٱجْتَمَعَتِ ٱلْإِنسُ وَٱلْجِنُّ عَلَىٰٓ أَن يَأْتُوا۟ بِمِثْلِ هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانِ لَا يَأْتُونَ بِمِثْلِهِۦ وَلَوْ كَانَ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ ظَهِيرًا
Saboda haka , da so yake akawo gyara ko difa’I k**ar yadda yayi da’awah ,sannan yana gudun yaran Musulmi su shiga rudani har takaiga yin RIDDAH -sai yayi abunda Malaman Musulinci na INDIA da PAKISTAN s**ayi; shine su dauki kowace tuhuma su warwareta da irin misalai da lafazukan da s**a dace, sannan yayi kira ga iyayen yara musulmi da cewa su dage wajen habbaka ilimin ‘ya’yansu na addini don su zama suna da cikakkiyar amsa ga abokan hamayyarsu sa’ilinda s**a bijiro musu da irin wannan rainin wayon.
Sa6anin wannan duk yunqiri da Malam yake na lalle sai anyiwa wasu daga cikin Hadisan nan gyaran fuska saboda gudun zargin YAHUDU da NASARA aikin banzane ,domin basuda buri illa ace mun bude qofar sauye –sauye cikin manyan littatafan addininmu k**ar yadda muke goranta musu akullum.
MAHANGA TA BIYU ITACE MAHANGA TA SHI’ANCI :
Kamar yadda mukasani MAZHABOBIN MUSLINCI MANYA a Zamanin yanzu sune SHI’A da SUNNAH. Kowanne daga cikin biyun nan bayan AL-Qur-ani mai girma suna da litattafansu da suke komawa don yin hukunci akan abunda yashafi Addinin .
Awajen ‘yan uwanmu ‘yan Shi’a Manyan litattafan Bukhari da Muslim ba sahihaibane- hasalima akwai kurakure da qirqirarrun hadisai acikinsu . Bugu da qari suna Tuhaman IMAMU BAKHARI da NASIBANCI (Qiyayyar Sayyudina ALI) – wanda agaskiyar lamari Malaman Sunnah bazasu taba dagawa Imamuna Bukhari qafaba muddin akwai digo na qiyayyar Sayyiduna Ali (Karramallahu wajahahu) acikin tafiyarsa.
Hanyoyin da suke bi wajen wareware Hadisan dake cikin Bukhari da Muslim sune dogaro da wasu ta’aliqat da wasu malaman hadisi na bangaren Sunnah s**ayiwa Junansu (suna yawan dogara da litattafan Ibnu Hajar da Alqadi Iyad – amma in ka koma wadancan litattafan zaka tarar suna inkarin Hadisanne ba wai suna aibata Imamul Bukhari ba –bugu da qarima wasu Hadisan suna cewa ba Buhari bane yasakasu acikin littatafansa ) –sannan kuma suna amfani da Littafan ALJARHU WATT ADEEL kai tsaye wajen yiwa Hadisan Bukhari da Muslim hukunci.
Wannan al-amarin ba a6oye yakeba- ga duk mai kallo tashoshinsu k**ar ALWILAYAH TV yasan hakan . Bugu da qari akwai litaffi mai suna “ A CRITICAL ASSESSEMENT OF SAHIHI BUKHARI AND SAHIHI MUSLIM BY SAYYID ALI AL-HUSAYNI AL-MILANI – Translated by Dr. Sayyid Abdur Rauf Afzali – akwaishi a online PDF ” bai wuce shafi casa’in ba (90 pages) yanada kyau akarantashi don gane mahangar Shi’a akan littattafan Imamu Bukhari da Muslim da meyasa suke nasabtamasa NASIBANCI .
Shi jifa da NASIBANCI wani yayi ne da akeyin amfani dashi adah, idan ana son adisasar da farin jinin wani Malami awannan zamanin k**ar yadda agefe guda kuma ake jifan wasu da RAFIDANCI (Qiyayyar Sahabbai) –ko kuma abunda yafi tashe ayanzu shine ajefi mutum da Bidi’anci –dukda akwai maqiyan na gaskiya, amma na Imamu Bukhari bincike ya nuna yarfene kawai- don dalilinda aka kawo basuda karfi.
Hakazalika abangaren Sunnah Takardun Shia masu girma k**ar NAH JUL BALAGAH suna da alamomin tambayoyi akanshi.
Kafun in rufe wannan gabar, yanada kyau mu sani cewar ; ba dukkan Malaman Sunnah bane suke yadda da cewar dukkan Hadisan dake cikin Sahihul Bukhari da Muslim ingantatune ba- k**ar Hadisin Iyayen Annabi (SAW) suna wuta (wa – iyazu billah) da sauransu- amma hakan bayasa a aibata masu takardun -sai dai kawai anema musu gafara- (don dan Adam ajizi ne ) kuma anusadda duk mai koyan karatu akansu batare da cin mutunci ,qage ko qazafi ga masu littafi ko sahabbanda akace sun rawaito Hadisan ba.
Saboda haka in ba Shi’a Malamin yakoma ba –bai kyautu ace tsakaninsa da wadannan Malaman na Hadisi akwai irin wadannan zarge-zargen ba .
MAHANGA TA UKU ITACE; MALAM BAI YI KARATUN HADISI AGABAN MALAMAI BA:
Kowane ilimi yanada ahalinsa da kuma MUS’DALAHAT (concepts ) dinsa; muddin ba’a karanceshi daga wajen masanansa ba toh lalle za’a samu fassarar gatari acikin lamarin. Wataqila masu bibiyata daliban makarantar boko ne (don mu akafi dilmiyarwa) ,saboda haka zan bada misali da Kalmar turanci ta “POWER” – awajen dalibin siyasa ko Lauyoyi ma’anarta daban da wajen dalibin Physics ko dalibin lissafi. Saboda haka daga jin yadda malam kewa wasu MUFRADAT (Kalmomi) fassarar son rai kasan bai karanci abun daga wajen masushi ba .
Misali Kalmar “Ha jah” da Mallam yadage akanta tana nufin biyan buqata irin ta tsakanin namuji da mace awannan hadisin , to ba gaskiya bane- don ba Malaminda yabata wannan ma’anar – hasalima awajensa aka farajin irin wannan fassaran . Idanma yanada Salaf ( wato magabaci) toh lalle zaka samu yafito ne daga 6angaren maqiyan litattafan.
Misalin abunda yakeyi yayi daidai da abunda ‘yan uwanmu Salafawa keyiwa litattafan sufaye; ta hanyar yimusu fassarar son zuciya da maida abun alheri ko mai kyau zuwa akasinsa.
Shi karatu daga wajen Ahalin abu yakan tserada mutum daga abubuwa k**ar haka ; gurguwar fahimta ko mumunar fassara –sannan awasu lokuta yasaka kasa tantance littafin gaskiya daga akasinsa .
Misali, Kwannan nake samun labarin wasu mutane da s**a fassara wani Mashahurin littafi na wani babban Mallami aqasarnan zuwa harshen faransaci . Sannan basu tsaya anan ba, sai da s**a qara fasali uku aciki. Duk wannan abubuwanda s**ayi batare da sanin iyalinsa ba (dukda an samu labari yanzu kuma anata qoqarin yadda zaa maganci lamarin, amma ; waya san wane barna s**a sa ,iya mutane nawa s**a siya-a ina da ina yashiga da sauransu) ….Toh wannan ma littafinda bai wuce shekaru sittinba kenan ,balantana Bukhari da ya tsokanewa mutane ido fiye da shekara dubu.
Da irin wannan fassarar da Malam yakeyi ,yatabbata cewa Malam bai cancanta akirashi da dalibin Hadisi ba, b***e yakai matsiyinda zaiyi tsokaci akan ayyukan wadannan bujuman malaman.
AN KASHE MUCIJI AMMA BA’A SARE KANSA BA :
Bayan wannan doguwar shimfida don gane MAHANGA da MADOGARAR Malam Abdul-jabbar ; yanada kyau mufahimci wasu lamura k**ar haka;
I) Yanke hunkuncin dauri ko kissa ga Malam Abdul-jabbar ba ita bace qarshen qadiyar ba, wataqila ta zama sanadiyar bude sabon shafi na rashin fahimta ga makafin mabiya- saboda haka akwai buqatar daukan lokaci ana qara ilimantar da al-umma da warware maganganunsa cikin ilimi don gamsar da bangare na al-ummar dake da sauran tunanin cewar an zaluncishi.
II) Qona dukkan littattafan da Mallam Abdul-jabbar ya rubuta wadanda ke dauke da irin wadannan tunaninnikan ko koyarwarsa - don in ba hakaba tarihi zai maimaita kansa .Saboda duk wanda yakaranta littattafan Sheikhul Islam Ibnu Taimiyah da tarihinsa , yasan cewa fatawowinsa na TAJSIMI da TAKFEER sunyi hanun rigar da koyarwar dukkan manyan Mallaman Mazhabobi hudu na zamaninsa (na Ahlussunnah ) . Amma barin litattafan cikin Al-ummah yana daya daga cikin sababinda ya jefa duniyar musulinci cikin matsananciyar gaba da zubda Jini da ake gani ayau.
III) Daga cikin Salafawa ko Wahabiyawa akwai wadanda suke da irin wannan sakin harshe da rashin Ladabi ga janibin Annabi (SAW ) saboda haka yak**ata ayi irin wannan Majar ayi musu irin wannan titsen sannan ashawarce gomnati ta hukuntasu k**ar yadda akaiwa Malam Abduljabbar –hakazalika ajanibin yan dariqa akwai masu daawar Qaryar Haqiqah suna aikata 6arna da sakin Harshe ga janibin Annabi (SAW) suma yadace ayi musu titse abawa gomnati shawarar yadda zata hukuntasu. In anyi haka za’a zauna lafiya , batare da zagi ko cin mutuncin wanda basuji ba, basu gani ba.
IV) Yanada kyau Daliban ilimi musani bayan karatun boko da mukeyi, yak**ata mukoyi harshen larabci mai zurfi. Don yin hakane kawai zai kubutarda mu daga fadawa cikin fatowowin son zuciya da Malamai masu dadin baki sukeyi awannan zamanin.
Sai sati mai zuwa zanyi posting akan darasukkan rayuwa da na koya daga wannan Muqabalar.
Allah kayi mana arzikin kyakkyawan qarshe don Alfarmar Annabi Sallallahu alaihi wasallam.