07/11/2025
An binne wannan saurayin Malam Ali Dogo a shekarar 1935, yau shekaru 90 da kwanciyarsa a Kabari.
An haife shi 1908, ya rasu 1935 yayi shekaru 27 a duniya. Malam Ali Dogo yana kwance a Kabari yana jiran tashin Qiyama, ya shafe shekaru 90 yana kwance yana jira, kuma da sauran tafiya.
Malam kar ka bari rayuwar shekaru 30, 40 ko 50 tasa ka gagara shirya ma kwanciyar shekaru dubu a kasa. Mu shafawa kanmu ruwa, akwai aiki a gaban mu wallahi.
Allah Yajikansa, Allah Yasa mucika da kyau da Imani.