05/08/2022
Taron Tunawa Da Shahadar Abdullahir Radi Dan Imam Hussain (A.S) Da Yayi Shahada A Hannun Mahaifinsa A Filin Karbala………
Daga: Salisu Jibril Khidir
A yau Juma’a 7 ga Watan Al-Muharram, 1444 Dai-dai da 5 ga Ogustan, 2022 ‘Yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) na Zariya. s**a shiga Rana ta Bakwai a jerin Kwanukan Zaman Makokin Ashura, Rana wacce tayi dai-dai da Ranar da Imam Hussain yayi sadaukarwa da Jinin Jaririnsa, sadaukarwa mai girma ga Ubangijinsa na Jinin Dansa Abdullahir Radi, wanda yayi Shahada a Hannun Mahaifinsa Imam Hussain (A.S) a filin Karbala.
Taro ne da ake shiryawa a duk shekara. Domin tunawa da irin sadaukarwar da Imam Hussain yayi na Jinin Dansa Abdullahir Radi a filin Karbala, Hadi da wahalar da Iyalan gidan Manzon Allah S.A.WW s**a fuskanta a filin Karbala na ‘Kishin Ruwa hadi da Dauri da sarka daga Sojojin Yazidu Dan Mu’awuya, a bisa Umurninsa. suna tafe ana Duka da Bulala. A irin wannan Azabtarwar Ne Imam Hussain (A.S) ya Bukaci Sojojin Yazidu Dan Mu’awuya da su baiwa Jaririnsa mai dauke da matsanancin kishin Ruwa ya sha, amma s**a hana. Inda daga Karshe Shugaban Rundunar Sojin Mu’awuya yayi Umarni ga wani fasuki mai Suna “Harmala” ya harbeshi da kibiya, a dai-dai saitin Makogoronsa. Ya koma izuwa ga Mahaliccinsa.
Abisa haka ne ‘yan uwan na Zariya. S**a shirya taron tunawa da Shahadar Abdullahir Radi Dan Imam Hussain wanda yayi Shahada a filin Karbala, Inda Taron Ya sami Halartar ‘Yan’uwa Mata tare da Jariransu da dama daga Birni da Karkaran na Zariya.
Shakh Abdulhamid Bello ne ya Jagoranci zaman inda ya gabatar da Jawabinsa Takaitacce, ya kumayi kira ga Iyaye akan suyi koyi da irin Sadaukarwar da Aba Abdullah Imam Hussain (A.S) yayi na Sadaukarda Dansa, da shi Kansa, Ya zama idan bukatar hakan ta taso bama ‘Yayan ka ba Har Kanka, ka Sadaukar domin tabbatar da Addinin Allah Ta’alah, kasance Mai sallamawa mawa ga Ubangijinka akan komai ka mallaka, yaza ashirye kake.
akarshe Shaikh Abdulhamid Bello ya gabatar da Addu'a.