
18/06/2025
SALLAR ROKON RUWAN SAMA
An Gudanar Da Sallar Rokon Ruwa a Kaura Namoda Bayan Shafe Kwanaki Da Dama Babu Ruwan Sama, Wanda Har Ta Kai mutane da dama hankulansu ya fara tashi duba da cewar kwanukan damina sun jima da tsayuwa amma har yanzu shiru, yayinda wasu mutanen iraruwansu na cikin ƙwarya domin jiran ruwan shukar.
Liman Malam Badamasu ne ya jagoranci Sallar yayinda Sheikh Malam Muhammad na gangaren Makaranta ya gabatarda Nasihohi masu ratsa zukata akan Muhimman lamura dake kawowa fadawa acikin waɗannan musifu na ɗaukewar ruwan sama da kuma ibada daya kamata a yawaita yinsu adai dai wannan lokaci domin gushewar Wannan farin.
Muhimman mutane da dama sun samu halartar Masallacin dafatan Allah ya bamu ruwan rahama Ameen.
Yahaya Mahi Na-Malam Babba
AMALE Hausa24