Kidaya

Kidaya Kidaya Is Online Newspaper that features truthful and reliable information in Nigeria and beyond. We

Ɗan Garin Kumo Ya Kafa Tarihi A Jihar Gombe Na Samun Nasara A Fannin IlimiDaga: Muhammad Chigari KumoWani matashi ɗan as...
09/05/2026

Ɗan Garin Kumo Ya Kafa Tarihi A Jihar Gombe Na Samun Nasara A Fannin Ilimi

Daga: Muhammad Chigari Kumo

Wani matashi ɗan asalin garin Kumo da ke ƙaramar hukumar Akko a Jihar Gombe, Muhammad Usman Yahya, ya kafa tarihi a fannin ilimi bayan kammala karatun digiri da na Masta da sakamako na First Class.

Rahotanni sun nuna cewa Muhammad Usman Yahya, wanda ke koyarwa a Gombe State University reshen Dukku, ya samu First Class a Abubakar Tafawa Balewa University (ATBU) da CGPA 4.83, inda ya kasance ɗaya daga cikin ɗaliban da s**a fi ƙwazo a sashensa da kuma a Faculty ɗinsa.

Bayan wannan nasara, ya ci gaba da karatun digirin Masta, inda kuma ya sake samun First Class da CGPA 4.93, abin da ya ƙara tabbatar da kwazonsa, jajircewarsa da kuma himmarsa wajen neman ilimi.

A halin yanzu, yana ci gaba da karatun Digirin Digirgir (PhD) a fannin Estate Management and Valuation, domin zurfafa bincike da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban ilimi da harkar kimanta kadarori.

Da yake bayyana sirrin nasararsa, Muhammad Usman Yahya ya ce jajircewa, haƙuri da mayar da hankali ga buri su ne ginshiƙan da s**a taimaka masa wajen cimma wannan matsayi.

Ya kuma shawarci ɗalibai da matasa da su guji kwatanta kansu da wasu, su dage wajen neman ilimi tare da yin aiki tukuru domin cimma burinsu.

Wannan nasara ta zama abin alfahari ga al’ummar Kumo, Jihar Gombe da ma Najeriya baki ɗaya, tare da nuna cewa ƙwazo da jajircewa na iya kai mutum ga manyan matsayi a rayuwa.

DA DUMI-DUMI: A yau Laraba matasan gidan Professor Isa Ali Pantami da s**a hada mishi fiye da Naira miliyan sittin (N60,...
29/04/2026

DA DUMI-DUMI: A yau Laraba matasan gidan Professor Isa Ali Pantami da s**a hada mishi fiye da Naira miliyan sittin (N60,000,000) kudin siyan form din tsayawa takara sun cika burinsu na siyan form din.

Idan baku manta ba a ranar Jumma'a da ta gabata Matasan da Professor Isa Ali Ibrahim (Pantami), CON, PhD, yayi silar taimakon rayuwarsu da masoyanshi s**a kudiri aniyar saya mishi form din tsayawa takarar Gwamnan jihar Gombe a kokarin matasan na maida halaccin taimakonsu da Professor Isa Ali Pantami yayi a rayuwarsu.

Wannan dalilin yasa matasan s**a kafa kwamitin gaggawa a tsakaninsu ba tare da wani ya saka su ba, inda a cikin kwanaki biyu kacal s**a hada fiye da Naira miliyan sittin (N60,000,000) kudin da ya zarce na iya siyan form din.

Dukkannin mutanen da s**a bada gudummuwarsu babu wanda aka saka ya bayar kowa radin kanshi

Wannan yake kara nunawa duniya cewa Majidadin Daular Usmaniyya ya kafa matasa da ayyukan yi a damar da ya samu.

A yau Laraba wakilan wasu daga cikin matasan s**a je inda ake saida form din, s**a cika burinsu na siyawa Malam Isa Ali Pantami form din kamar yadda s**a kudiri aniya.

2027 Duk Alamu Sun Nuna Professor Isa Ali Pantami Na Kan Gaba a Siyasar GombeA daidai lokacin da siyasar Jihar Gombe ke ...
14/04/2026

2027 Duk Alamu Sun Nuna Professor Isa Ali Pantami Na Kan Gaba a Siyasar Gombe

A daidai lokacin da siyasar Jihar Gombe ke kara daukar zafi gabanin zaben shekarar 2027, alamu da dama na ci gaba da nuna cewa professor Isa Ali Pantami na daga cikin manyan jiga-jigan da suke kan gaba wajen samun tikitin takarar gwamnan jihar, in sha Allah.

Masu sharhi da bibiyar siyasa a jihar na ganin cewa kwarewa, gogewa da kuma irin rawar da Pantami ya taka a matakin kasa sun sanya sunansa ya zama daya daga cikin wadanda jama’a ke yawan ambato a duk lokacin da ake maganar makomar shugabancin Jihar Gombe.

A sassa daban-daban na jihar, ana ci gaba da jin kiraye-kiraye daga matasa, masu ruwa da tsaki da sauran al’umma, suna bayyana fatansu na ganin shugabanci mai hangen nesa wanda zai kara inganta cigaban jihar a fannoni da dama.

Ko da yake lokaci bai kai ga bayyana takara a hukumance ba, amma al’ummar Gombe na ci gaba da bibiyar yanayin siyasa, inda da dama ke kallon Professor Isa Ali Pantami a matsayin daya daga cikin manyan zabin da zai iya taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar jihar a 2027.

Rubutawa Muhammad Chigari Kumo

ƘUNGIYAR AREWA MEDIA WRITERS TA BUƘACI GWAMNATIN TARAYYA DA TA GAGGAUTA ƘWACE MAKAMAN ƳAN TA’ADDA DA AKA YI SULHU DA SU…...
31/03/2026

ƘUNGIYAR AREWA MEDIA WRITERS TA BUƘACI GWAMNATIN TARAYYA DA TA GAGGAUTA ƘWACE MAKAMAN ƳAN TA’ADDA DA AKA YI SULHU DA SU

…Ƙungiyar ta ce barin makamai a hannun waɗanda aka yi sulhu da su na ci gaba da jefa al’umma cikin fargaba da rashin tsaro.

Daga Ƙungiyar “Arewa Media Writers”

Ƙungiyar Marubutan Arewa “Arewa Media Writers”, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Comr. Haidar H. Hasheem, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakin kwace makaman ‘yan ta’adda da aka yi sulhu da su, musamman a jihohin Katsina, Zamfara da sauran yankunan Arewacin Najeriya.

Ƙungiyar ta bayyana damuwarta matuƙa kan yadda wasu daga cikin ‘yan bindigar da aka yi sulhu da su ke ci gaba da riƙe makamai, inda ake zarginsu da amfani da su wajen barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.

A cewar ƙungiyar, rahotanni daga wasu yankunan karkara a Jihar Katsina na nuna cewa waɗannan mutane na ci gaba da shiga ƙauyuka, suna tsoratar da jama’a, suna karɓar haraji ba bisa ƙa’ida ba, tare da kwace dabbobi da sauran dukiyoyi daga hannun talakawa.

Ƙungiyar ta ce wannan lamari na nuna cewa sulhun da aka yi bai kai ga cikakken tsaro ba, matuƙar ba a ɗauki matakin kwace makaman da ke hannunsu ba. Ta ƙara da cewa, barin makamai a hannun waɗanda s**a saba aikata laifuka na iya sa su sake komawa aikata ta’addanci a kowane lokaci.

Ƙungiyar Arewa Media Writers ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa wajen tabbatar da cewa duk wanda ya amince da sulhu ya miƙa makamansa gaba ɗaya, tare da sanya ido mai tsauri domin hana sake aikata irin waɗannan laifuka.

A ƙarshe, ƙungiyar ta jaddada cewa wajibi ne a ɗauki matakan da s**a dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da cewa sulhu ya zama hanya ta samar da zaman lafiya mai ɗorewa, ba wata dama da za ta bai wa ‘yan ta’adda ƙarfin ci gaba da cin zarafin jama’a a yankin Arewacin Najeriya ba.

Ƙungiyar ta kuma yi addu’ar Allah Ya kawo ƙarshen waɗannan matsaloli da ake fama da su a yankin Arewa da ƙasa baki ɗaya, tare da roƙon al’umma su ci gaba da saka ƙungiyar cikin addu’o’insu kan ƙoƙarin da take yi na samar da canji da ci gaba mai ɗorewa.

✍️✍️
Comr Muhammad Kwairi Waziri
National Editor 1, Arewa Media Writers

Sama Da Mutum Ɗari Biyu Aka Kashe, An Sace Wasu A Cikin Kwanaki Biyu A Jihohin Zamfara Da KebbiDaga Kungiyar Arewa Media...
23/02/2026

Sama Da Mutum Ɗari Biyu Aka Kashe, An Sace Wasu A Cikin Kwanaki Biyu A Jihohin Zamfara Da Kebbi

Daga Kungiyar Arewa Media Writers

Kungiyar Arewa Media Writers, karkashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Haidar H Hasheem, ta bayyana matukar alhini da fusatarta kan hare-haren kisan gilla da sace jama’a da s**a afku a jihohin Zamfara da Kebbi cikin kwanaki biyun da s**a gabata.

Kungiyar ta ce abin takaici ne yadda rayukan al’ummar Arewa ke ci gaba da salwanta ba tare da daukar tsauraran matakan da s**a dace ba daga hukumomin da abin ya shafa.

A cewar kungiyar, rahotannin da ke fitowa daga jaridar The Cable sun nuna cewa harin ya auku ne a jihar Zamfara a ranar Asabar, inda akalla mutane 50 s**a rasa rayukansu, yayin da sama da mutane 150, ciki har da mata da kananan yara, aka yi garkuwa da su a kauyen Tungan Dutse da ke karamar hukumar Bukkuyum.

Haka zalika, jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an kashe mutane 34 a wasu garuruwa daban-daban na karamar hukumar Arewa a jihar Kebbi.

Kungiyar ta bayyana cewa shiru ko sakaci daga bangaren gwamnati kan irin wannan mummunan lamari tamkar amincewa ne da ci gaba da zubar da jinin bayin Allah. Ta jaddada cewa rayukan al’ummar Arewa suna da daraja kamar na kowanne yanki na kasar nan.

Don haka, Arewa Media Writers ta bukaci gwamnatocin jihohin Kebbi da Zamfara tare da gwamnatin tarayya da su dauki matakan gaggawa, ciki har da:

- Kara yawan jami’an tsaro a yankunan da rashin tsaron ke kara yawaita
- Tallafawa wadanda harin ya rutsa da su
- Bincike mai zurfi kan lamarin
- Daukar mataki kan duk wani jami’i ko mai ruwa da tsaki da aka samu da sakaci ko hannu a matsalar tsaro

Kungiyar ta jaddada cewa ba za ta yi shiru ba har sai an tabbatar da adalci, an kamo masu hannu a wannan ta’asa, tare da daukar matakan da za su kawo karshen wannan bala’i da ke addabar yankin Arewa.

Daga ƙarshe ƙungiyar tayi addu'a kan Allah ya bawa ƙasarmu zaman lafiya musamman yankinmu na Arewacin Najeriya, haka kuma ƙungiyar tayi addu'ar dukkan mai hannu a wannan ta'addancin Allah yayiwa al'umma maganinsa.

✍️ Muhammad Kwairi Waziri, Chief Editer "Arewa Media Writers"

Kamfanin ABBA PANTAMI DATA LTD, suna muku barka da shigowa sabuwar shekara. A yanzu haka Datar 1GB mai kyau da inganci t...
01/01/2026

Kamfanin ABBA PANTAMI DATA LTD, suna muku barka da shigowa sabuwar shekara.

A yanzu haka Datar 1GB mai kyau da inganci ta koma kasa da Naira 500 a cikin Application din ABBA PANTAMI DATA LTD, kowa ya duba Application dinshi domin more garabasa, anyi ragi na musamman a sauran Data na Application din.

DA DUMI-DUMI: Ali Nuhu ya zama Ambasadan kamfanin ABBA PANTAMI DATA LTD, bayan kulla yarjejeniyar Naira miliyan 30 na ts...
25/12/2025

DA DUMI-DUMI: Ali Nuhu ya zama Ambasadan kamfanin ABBA PANTAMI DATA LTD, bayan kulla yarjejeniyar Naira miliyan 30 na tsawon shekara guda

ABBA PANTAMI DATA LTD ya sake rage muku farashin Data zuwa Naira 500 akan kowane 1GB, ku hanzarta ku sauke Application din, domin ku more garabasa.

Duk wanda ya sayi Data mai 30DAYS a Application din ABBA PANTAMI DATA LTD to sai tayi kwanaki 30 sannan za tayi Expired. Akwai bambanci tsakanin Expired da kuma karewa.

Matukar kuna amfani da Application din ABBA PANTAMI DATA LTD da zaran ka hadu da matsalar network ko makalewar kudi kana yiwa customer care dinsu magana anan take zasu gyara maka.

Idan baka taba amfani da Application din ba ka gwada, idan ka dade baka yi amfani dashi ba ka sake gwadawa a yanzu domin tabbatar da ingancin shi.

Kuyi Download din Application din ABBA PANTAMI DATA ta wannan link din a PlayStore da kuma AppStore

👇👇
Ga link din PlayStore
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.com.abbapantamidata.app

Ga link din AppStore
https://apps.apple.com/us/app/abba-pantami-data-ltd/id6744061271

Mai bukatan karin bayani, ya tuntubi daya daga cikin customer care ta WhatsApp;
09138275183
08126081967
07046868000
07061347599

TIRKASHI: Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bayar da Naira biliyan 2.5 ga kasar Najeriya domin su gina filin kwallo...
26/10/2025

TIRKASHI: Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bayar da Naira biliyan 2.5 ga kasar Najeriya domin su gina filin kwallon kafa a jihar Kebbi da Delta.

Itama Kenya an bata irin wannan kudin domin ta gina.

Ga dai na Najeriya da aka gina a Kebbi an kashe mishi biliyan 1.2😅😂
Ga kuma na Kenya.

Dr. Bashir Abdullahi Gaddafi Ya Halarci Zaman Da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar a AbujaDaya daga cikin m...
21/10/2025

Dr. Bashir Abdullahi Gaddafi Ya Halarci Zaman Da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar a Abuja

Daya daga cikin manyan ‘ya’yan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Gombe, Hon. Dr. Bashir Abdullahi Gaddafi, ya kasance cikin tawagar shugabannin jam’iyyar da s**a ziyarci tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma jagoran kwatowa talakawa ‘yancinsu, Alhaji Atiku Abubakar, a babban birnin tarayya Abuja, a daren Litinin.

Ziyarar ta kasance wani ɓangare na ci gaba da tattaunawa tsakanin shugabannin jam’iyyu da fitattun ‘yan siyasa domin ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin ‘yan Najeriya, tare da neman hanyoyin da za su inganta rayuwar talakawa da haɓaka dimokuraɗiyya a ƙasar nan.

A cewar Dr. Gaddafi, wannan zama na da muhimmanci wajen ƙarfafa haɗin kai da samar da cigaba a yankin Arewa, musamman a Jihar Gombe da Karamar Hukumar Akko.

Ubangiji Allah Ya sanya wannan zama ya amfanar da al’ummar Najeriya, Jihar Gombe, da Karamar Hukumar Akko gaba ɗaya,” in ji Dr. Bashir Abdullahi Gaddafi yayin da yake ganawa da manema labarai bayan zaman.

Dr. Gaddafi ya kara da cewa lokaci ya yi da ‘yan siyasa za su mayar da hankali wajen warware matsalolin tattalin arziki, ilimi da zaman lafiya domin dorewar ƙasa.

Wannan ziyara ta Dr. Gaddafi ta ƙara nuna yadda matasa masu kishin ƙasa ke shiga harkokin siyasa cikin natsuwa da hangen nesa, tare da neman hanyoyin haɗin kai domin ci gaban al’umma.

Fatan Nasara Baba Atiku
Tare da Dr. Bashir Gaddafi Kumo. ✅🇳🇬

Hon. Dr. Bashir Abdullahi Gaddafi Ya Gana da Kungiyoyi a Garin KumoJagoran kawo canji a siyasar Karamar Hukumar Akko, Ho...
17/10/2025

Hon. Dr. Bashir Abdullahi Gaddafi Ya Gana da Kungiyoyi a Garin Kumo

Jagoran kawo canji a siyasar Karamar Hukumar Akko, Hon. Dr. Bashir Abdullahi Gaddafi, ya gudanar da ganawa da wasu kungiyoyi masu muhimmanci a garin Kumo, domin tattauna hanyoyin da za su inganta hadin kai da cigaban al’umma.

Kungiyoyin da s**a halarci taron sun haɗa da wakilan ƙungiyar makanikai, Northern Youth Solidarity Movement, Matasan Anguwan Makera Tambe, da kuma Akko Great Ambassadors Youth Forum.

A yayin tattaunawar, Dr. Gaddafi ya bayyana cewa tafiyar da suke yi tafiyar kowa da kowa ce, wacce nufinta shi ne samar da sauyi mai ma’ana da kuma tabbatar da cigaba ga jama’ar Akko.

Ya kara da cewa, da yardar Allah, zamu kai inda muka dosa, yana mai tabbatar da cewa wannan tafiyar za ta bai wa talakawa damar amfana da romon dimokaradiyya.

A ƙarshe, mahalarta taron sun yi addu’ar samun nasara ga tafiyar siyasar Dr. Gaddafi domin dorewar cigaba da zaman lafiya a Akko.

Address

Kaduna Zaria Round
Kaduna South
2580111

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kidaya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share