26/03/2022
MITUWAR AUREN MATAN HAUSA FILM..
INA MAFITA?
director Nass Kd.
Tabbas babu wata 'ya mace dazataso tayi aure sannan kuma ta fito, saidai su matan da s**a shahara a kowace masana,antar film a duniya zakaga duk motsin da s**ayi duniya ta sani domin kuwa sanin kowane cewar mu 'yan film bamuda sirri ko kadan komai namu a idan duniya yake hakan ne yasa ake sani da zarar auren 'yan film ya mutu.
MEYASA AUREN'YAN FILM KE MUTUWA
yan film mutane ne k**ar kowa amma k**ar na fada basuda sirri dan haka nasu yafi fice k**ar yadda auren kowa ke iya mutuwa haka suma amma idan duniya na kansu shiyasa duniya ke sani da zarar sun fito kuma dayawan mazan suna auren daukakar sune basuba dan haka ba lallai auren ya dade ba dakuma wasu dalilai na kashin kamsu.
INA MAFITA
A iya tinani na rage faruwar hakan ya shafi masana,antar dakuma wajenta misali
Wadan da suke auren su suji tsoran Allah su rinka aurensu dan Allah badan daukaka ko wani abun duniya ba.
Suma matan suji tsoran Allah su rinka hakuri da duk yanayin s**a tsinci kansu gidan aure sannan su k**a sana,a domin ba lallai su sami yadda suke tsammani ba a gidan auren.
Producers da director munada gudunmawa mai karfi na takaita wannan lamarin ta hanyar kin sanya duk wata yar film da tayi aure ta fito duk daukakarta kuwa musammam idan aka gano da laifinta a mutuwar auren.
Hakika mutuwar auren jaruman film kuma su dawo acigaba da damawa dasu yana karya mutuncin masana,antar, kuma hakan na kara ta,azzara lamarin